Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Gwamnatin Najeriya Ta Jadda Da Aniyar Rage Radadin Talauci
Published: April 27, 2026 at 10:48 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyarta na yaƙi da talauci tare da samar da hanyoyin inganta rayuwar ’yan ƙasa, musamman ma mazauna karkara waɗanda ayyukan ci gaba ba su cika isa gare su ba.

Babban Manajan Shirin GEEP 3.0 na “FarmerMoni” karkashin tsarin ‘Renewed Hope’, Hamza Ibrahim-Baba, shi ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin taron wayar da kan kafofin yaɗa labarai na shiyyar Arewa maso Yamma da aka gudanar a birnin Kano.

Ibrahim-Baba ya bayyana cewa wannan shiri na RH-GEEP 3.0, wanda ya shafi manoman rani da na damina, wani ɓangare ne na manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na farfaɗo da tattalin arziƙin ƙananan sana’o’i a faɗin ƙasar nan.

Ya ce: “An tsara GEEP 3.0 ne domin ya isa zuwa ga al’ummar da aka bari a baya, da kuma inganta tattalin arziƙi tun daga tushe. Burinmu shi ne mu tallafa wa ’yan Nijeriya da ke can ƙasan matattarar tattalin arziƙi, mu inganta rayuwarsu, kuma mu samar musu da damar samun kudin shiga mai dorewa.”

A nata jawabin, Darakta Janar ta Hukumar Kare Muradin Jama’a ta Jihar Kano, Fatima Abubakar-Abdullahi, ta bayyana cewa shirin ya sa gaba ne wajen tallafa wa rukunin mutanen da suka fi rauni, musamman manoma da ƙananan ’yan kasuwa na karkara.

Ta ƙara da cewa shirin zai samar da damar samun rance ba tare da ruwa ba, tare da bayar da horon gina ƙwarewa ga masu cin gajiyar shirin.

Haka zalika, ta jaddada mahimmancin wayar da kai, inda ta nuna cewa da yawa daga cikin waɗanda suka cancanci shirin ba su riga sun fahimci hanyoyin da za su bi domin cin gajiyar sa ba.

“Irin wannan wayar da kan na da mahimmanci matuƙa. Idan mutane suka fahimci yadda shirin yake tafiya, shiga cikinsa zai ƙaru, sannan tasirinsa zai kasance mai ma’ana ga rayuwarsu,” in ji ta.

Afrika, Labarai, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Kungiyoyin Fararen Hula A Gombe Sun Bukaci A Bawa Mata Jagoranci
Next Post: Majalisa Ta Tabbatar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan Kano

Karin Labarai Masu Alaka

Kimanin Mutane 200 Ne Suka A Mutu A Wani Harin Jirgin Yakin Sojin Najeriya Afrika
Yeriman Ingila Ya Gana Da Yeriman Saudiya Mai Jiran Gado Amurka
Sama Da Zawiyya 100 Ne Suka Samu Tallafin Kayan Abinci Daga Al’mustapha Haji Sufi Labarai
Gwamnatin Najeriya Tace Ta Farmaki Mayakan ISIS A Jihar Sokoto Labarai
Shahararren Dan Dambe Anthony Joshua Yayi Hatsarin Mota A Jihar Ogun Labarai
‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane A Wajen Hakar Ma’adanai Dake Jihar Filato Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gobara Ta Tashi A Hukumar FIRS Dake Abuja Najeriya
  • Wani Jirgin Kasa Yayi Hatsari A Kudancin Spain Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Dakaru Sun Hallaka ’Yan Ta’adda Masu Yawa – DHQ Afrika
  • NAHCON Ta Fara Shirye-shiryen Dawowar Alhazai Afrika
  • Nuhu Ribadu Ya Mika Yara 130 Da Aka Kubutar Ga Gwamna Bago Tsaro
  • Mawakiyar Amurka Cardi B. Ta Cashe A Saudi Araibiya Nishadi
  • Gwamnatin Jihar Yobe: Ana Cin Zarafin Fursunoni A Gidan Gyaran Halin Potiskum Tsaro
  • Rashin Hanya da Asibiti Ya Jawo Asarar Rayuka A Jihar Gombe – Sarkin Gargajiya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.