Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Netanyahu Ya Umarci Rundunar Sojoji Takara Fadada Ayyukanta A Lebanon
Published: March 30, 2026 at 9:20 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana a ranar Lahadi cewar, ya umarci rundunar sojoji da ta ƙara faɗaɗa ayyukanta a kudancin Lebanon, yana mai danganta hakan da ci gaba da harba rokokin da ƙungiyar Hezbollah ke yi.

Isra’ila ta ce a makon da ya gabata tana ƙara faɗaɗa wani “yakin kariya” har zuwa kogin Litani. Sai dai ba a bayyana kai tsaye ko Netanyahu na nufin wannan yanki ba ne ko kuma a yankin da suka ƙwace yanzu.

Netanyahu ya ce a cikin wani bidiyo da ya fitar daga hedikwatar rundunar arewacin Isra’ila cewa: “Na bayar da umarni a ƙara faɗaɗa yankin tsaro da ake da shi domin a ƙarshe a kawar da barazanar kutse, tare da tura hare-haren makaman roka masu lalata tankuna daga kan iyakokinmu.”

Ofishinsa ya ƙi bayar da ƙarin bayani, sannan har yanzu ba a tattauna wannan batu a majalisar tsaron ƙasar ba.

A makon da ya gabata, Ministan Tsaro Israel Katz ya ce sojojin Isra’ila za su “ci gaba da riƙe sauran gadoji da yankin tsaro har zuwa kogin Litani,” wanda ke haɗuwa da Tekun Bahar Rum kusan kilomita 30 arewa da iyakar Isra’ila.

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Jami’ar ABU Zaria Ta Karbi Kudade Naira Bilyan 1.3 Daga Shirin Nelfund
Next Post: Pakistan Zata Karbi Tattaunawar Rikicin Gabas Ta Tsakiya

Karin Labarai Masu Alaka

Isra’ila Zata Rusa Gidajen Da Suke Iyakarta Da Lebanon Labarai
Najeriya Da Maroko Sun Kulla Yarjejeniya Afrika
Gwamnatin Najeriya Ta Jadda Da Aniyar Rage Radadin Talauci Afrika
Shugaban Lebanon Ya Nemi Gudanar Da Shawarwari Kai Tsaye Afrika
Limamin Da Ya Ceci Kiristoci Lokacin Rikicin Addini A Jihar Filato Ya Rasu Labarai
Afirka Ta Kudu Ta Kubutar Da ‘Yan Kasar Da Suke Taya Sojojin Rasha Yaki Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gobara Ta Lalata Babban Zauren Majami’ar ECWA Gospel A Gombe Afrika
  • Dalibai Sun Koma Makarantu A Wasu Jihohin Najeriya Najeriya
  • CAF Ta Hukunta Samuel Eto’o AFCON 2025 Labarai
  • NSCIA Ta Gargadi Gwamnati Kan Zargin Tauye Haƙƙin Musulmi Afrika
  • Darajar Kudin Afirka Ta Kudu Ya Tashi Afrika
  • Gwamna Inuwa Yahaya Ya Bukaci Al’ummar Gombe Su Haɗa Kai Wajen Yaƙi Da Ta’addanci Afrika
  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai Wasanni
  • Shugaba Tinubu Ya Kara Aika Sunayen Jakadu Ga Majalisa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.