Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

‘Yan Ta’adda Sun Kashe ‘Yan Sanda A Jihar Katsina
Published: January 28, 2026 at 7:48 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

‘Yan sanda 3 sun rasa rayukan su, yayin da wasu 2 suka jikkata lokacin da ‘yan ta’adda dauke da makamai suka kai hari kan ‘yan sanda masu sintiri a jihar Katsinan Najeriya ranar Talata, a cewar ‘yan sanda ranar laraba.

Wannan na daga cikin karuwar hare-hare da ‘yan ta’adda ke kaiwa, da ya hada da garkuwa da mutane da ‘yan bindiga ke yi idan sun far wa makarantun da wuraren ibada, a arewa maso yammacin kasar.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Katsina, Abubakar Sadiq Aliyu ya ce an far ma ‘yan sandan ne a wajen hanyar Guga da Bakori lokacin da suke sintiri. Ya ce ‘yan sandan sun nuna jarumta sosai wajen mai da wuta, inda suka fattattaki ‘yan ta’addan, amma sun rasa jami’ai uku a musayar wuta. ‘Yan sanda biyu da suka samu raunuka na karbar magani a wani asibiti da ke kusa da inda abun ya faru.

A wani labarin kuma, a dai Najeria, a yau ‘yan sanda a jihar Lagos sun harbawa masu zanga-zanga kan rushe sansanin gidajen talakawa dake gab da teku da gwamnatin jihar ta yi tear gas, inda daya daga cikin masu zanga-zangar ya samu rauni. Rushe gine-ginen ya jawo da dubbannan mutane rasa matsugunin su.

Jami’ai a jihar Lagos, tare da taimakon ‘yan sanda da mashunan tonon kasa, sun fara rushe gidajen talakawa a unguwar Makoko, inda suka ce mazauna wurin sun gina gidajen nasu ne ba bisa ka’ida ba, wadanda yawanci gidajen katako ne aka gina su a saman ruwa, kusa da injunan lantarki masu hatsari.

Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Kotu A Kasar Uganda Ta Bada Belin ‘Yar Gwagwarmaya
Next Post: Maganganun Jami’an Shige Da Fice Dana Shugaban Kasa Trump Suna Cin Karo Da Juna

Karin Labarai Masu Alaka

Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya Ta Ƙaddamar Muhimman Ayyuka A Jihar Jigawa Afrika
Akwai Yiwuwar Iran Da Amurka Su Cimma Matsayar Dakatar Da Shirin Nukiliya Amurka
Hare Hare A Kasar Congo Ya Jikkata Mutane Da Dama Afrika
NLC Ta Yabawa Gwamnan Gombe Inuwa Yahaya Najeriya
Jami’an Tsaro Suna Farautar Wasu ‘Yan Ta’adda A Najeriya Afrika
Shugaba Tinubu Ya Umarci Janye ‘Yan Sanda Masu Gadin Ministoci Tsaro

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Lewandowski: Zan Kokarta Zura Kwallo Ta 90 Don Kafa Tarihi A Poland Wasanni
  • Karo Na Biyu Cikin Kwanaki 29 An Samu Gobara A Kasuwar Katako Labarai
  • An Kaddamar Da Rijistar Zamani Ta Zamowa Mamba A Jam’iyar APC Siyasa
  • Farashin Mai Ya Doshi Dala 100 Kowacce Ganga Afrika
  • Anyi Sallar Rokon Ruwa A Saudiya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Harkar Zirga Zirgar Jiragen Sama Ya Bunkasa A Kenya Afrika
  • Amurka Na Zargi Kasar Rwanda Da Kokarin Saba Yarjejeniyar Zaman Lafiya Amurka
  • Shugaba Tinubu Ya Umarci Janye ‘Yan Sanda Masu Gadin Ministoci Tsaro
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.