Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata Afrika
  • NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa Afrika
  • Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno Amurka
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe Afrika
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya Afrika

An Damke Wani Likita Da Ke Taimakawa ‘Yan-Ta’adda
Published: December 5, 2025 at 1:36 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: December 5, 2025

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kama wani likita da ake zargi da jigilar kayan magani daga Jihar Sokoto zuwa wasu kungiyoyin masu garkuwa da mutane da ke aiki a sassan jihar Kwara.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin Facebook na gidan Gwamnatin Jihar Kwara a ranar Juma’a.

Rahotanni sun ce an kama likitan ne a Jebba, cikin Karamar Hukumar Moro, bayan samun bayanan sirri da suka hada shi da wata hanyar kai magunguna ga kungiyoyin ‘yan bindigar.

An ce kama ire iren sa, yana daya daga cikin matakan da ake dauka domin dakile hanyoyin da ke tallafa wa miyagun kungiyoyi a yankin.

Majiyoyin tsaro sun ce ‘yan bindigar sun kara yawan neman kulawar likita, musamman wajen magance raunukan harbin bindiga da suke samu yayin artabu da jami’an tsaro.

Wannan karuwar bukatar magunguna ta jawo hankalin hukumomin tsaro da ke sa ido kan zirga-zirgar haramtattun kayayyaki.

Wani jami’in tsaro ya yi gargadin cewa cibiyoyin lafiya da ke kusa da dazuka na iya fuskantar karin barazana, domin miyagun mutane na iya kai farmaki don neman kulawar gaggawa.

Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Rivers: ‘Yan Majalisa 16 Sun Canza Sheka Zuwa APC
Next Post: Ƙungiyoyin Premier 17 Za Su Rasa ‘Yan Wasa 40 saboda Gasar AFCON 2025,

Karin Labarai Masu Alaka

Majalisar Dokokin Filato Ta Kare Kudirin Alawus Ga Tsofaffin ‘Yan Majalisa Afrika
Shugaba Tinubu Ya Bukaci Samar Da Zaman Lafiya A Filato Afrika
Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
Majalisar Dottawa Ta Kafa Komitin Dokar Zabe Najeriya
Jiragen Ruwa Suna Biyayya Ga Dokar Hana Ketare Ruwa Amurka
‘Yan Tawayen Houthi Sunkai Hari Isra’ila Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata
  • NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa
  • Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Trump Ya Hana Kaiwa Cuba Man Fetur Daga Venezuela Amurka
  • Wani Alkali A Amurka Ya Kalubalanci Gwamnatin Kasar Afrika
  • Domin Karfafa Tsaro Babban Hafsan Sojin Najeriya Ya Ziyarci Jos Afrika
  • Iran Ta Bukaci Duniya Ta Shirya Domin Fuskantar Tsadan Mai Amurka
  • Amurka Zata Bada Gudumawar Kudi Dala Bilyan 10 Ga Ayyukan Kwamitin Wanzar Da Zaman Lafiyan Amurka
  • Uefa Ta Zabi Artan, Ya Jagoranci Wasan Cin Kofin Uefa Super Cup Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • An Gargadi Kasar Canada Game Da Tura Sojoji Lebanon Afrika
  • Sojin Najeriya Da ‘Yan Ta’adda Sunyi Taho Mugama Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.