Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata Afrika
  • NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa Afrika
  • Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno Amurka
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe Afrika
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya Afrika

Isra’ila Ta Kashe Babban Jami’in Tsaron Iran Ali Larjani
Published: March 18, 2026 at 8:06 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ranar talata, Isra’ila ta bada sanarwar ta kashe babban jami’in tsaro a Iran, jami’in Farisa mafi-girma da ta auna hari akansa tun fara bayanin ranar farko na fara yakin, a yayinda wani jami’in kasar yake cewa, sabon shugaban addinin kasar ya ki amincewa da tayin sassauta rikicin, da wata kasa mai shiga tsakani ta gabatar mata.

Nan take dai Iran bata ce komi ba kan sanarwar da Isra’ila ta bayar cewa ta kashe Ali Larijani, wanda ake kallo a zaman mai fada aji kuma na hanun daman marigayi tsohon shugaban addinin kasar, da magajinsa kuma dansa Mojtaba.

A wata alamar ci gaba da bijirewar da Iran take yi, bayan fiye da mako biyu ana gwabza yaki, wani babban jami’in kasar, wanda ya bukaci a sakaye sunansa, yace Mojtaba Khameni yayi watsi da wani daftari da aka gabatarwa ma’aikatar harkokin wajen kasar na bukatar, “ a sassauta rikicin, ko a tsagaita wuta tsakaninta da Amurka,” Inji jami’in.

Jami’in yace sabon shugaban addinin kasar yayi zaman farko na shawarwari game da harkokin wajen kasar, sai dai bai fayyace ko sabon shugaban wanda zuwa yanzu ba’a ganshi ba tunda aka nada shi, ya halarci zaman shawarwarin na farko da kansa, kodai ya halarci taron ne daga nesa tare da amfani da hanyoyin sadarwa na zamani.

Afrika, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Trump Yace Kawayen Amurka A Kungiyar NATO Basa Goyon Bayan Su
Next Post: Na Yi Murabus Ne Don Amurka Ta Keta Haddin Iraniyawa

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Kasar Guinea Ta Soke Wasu Jam’iyyun Siyasa Afrika
Wani Harin ‘Yan Bindiga Ya Kashe Mutane 35 A Jihar Borno Labarai
Kasar Togo Ta Kori Paul Henri Damiba Zuwa Kasar Sa Ta Haihuwa Afrika
Kasar China Ta Sauka Daga Ragamar Bada Bashi Labarai
An Sace Masu Ibada A Wata Majami’ar Ecwa A Jihar Kogi Tsaro
Ingila, Hauhawar Farashi Yayi ƙasa Sosai Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata
  • NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa
  • Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • FIFA Na Shirin Fadada Babban Na’urar VAR A Gasar Cin Kofin Duniya 2026. Wasanni
  • Ma’aikatan Tattara Kudin Haraji Sunyi Rikici Da Masu Babura A Bauchi Najeriya
  • Bisa Alamu Hadinkan Kasashen Yankin Sahel Zai Haifar Da Nagarta Afrika
  • Shugabannin Kiristoci Sun Halarci Filin Idi A Kaduna Domin Nuna Haɗin Kai Afrika
  • Kasar Faransa Ta Karyata Cire Afirka Ta Kudu Daga G7 Afrika
  • Gwamnatin Jihar Yobe: Ana Cin Zarafin Fursunoni A Gidan Gyaran Halin Potiskum Tsaro
  • Kasar Colombia Tare Da Amurka Zasu Fitar Da Man Venezuela Labarai
  • Zamfara: Sai Mun Hada Kai Don Kawo Karshen Ta’addanci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.