Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • An Bawa Fasto Yohanna Buru Sarautar “Jagoran Zaman Lafiyar Arewacin Najeriya” Afrika
  • Inuwa Yahaya Ya Yi Alkawarin Barin Gombe Ba Tare Da Bashin Fansho Ba Afrika
  • NBA Gombe Ta Nemi IGP Ya Binciki Zargin Karɓar Kuɗi A FCID Annex Gombe Afrika
  • Ɗalibai 670 Sun Amfana Da Tallafin Jakakkuna Da Littattafai Daga Hukumar NEDC A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Gombe Ta Ƙarfafa Matakan Kare Dabbobi Daga Cututtuka Afrika

Gombe: An Kama Mutane Biyu Kan Zargin Kashe Matar Dan Sanda
Published: September 27, 2026 at 4:08 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rundunar ’Yan Sandan jihar Gombe ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a cikin wani hari da ya yi sanadin mutuwar matar wani jami’in ’yan sanda a unguwar Wuro Shie da ke cikin birnin Gombe.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:35 na asubahin ranar Asabar, 26 ga Satumba, 2026, lokacin da wasu mutane da har yanzu ba a tantance adadinsu ba, dauke da adduna da makamantansu, suka kutsa cikin gidan Inspector Salisu Waziri, wanda ke aiki da rundunar Safer Highway Patrol.

A cewar ’yan sanda, maharan sun yi yunkurin kwace wayar salula daga hannun matar jami’in, Mrs. Aishatu Salisu.

Rahoton ya ce matar ta yi ƙara domin neman agaji, lamarin da ya sa ɗaya daga cikin maharan ya kai mata hari tare da caka mata adda, kafin su tsere daga wurin.

An ce maharan sun bar wayar salular matar a wurin bayan sun tsere.

Bayan samun rahoton, jami’an rundunar sintiri na sashen ’yan sanda na Pantami sun gaggauta isa wurin da lamarin ya faru, inda suka garzaya da matar zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe domin ba ta agajin gaggawa. Sai dai, likitoci sun tabbatar da cewa ta rasu.

Bayan faruwar lamarin, Rundunar ’Yan Sandan Gombe ta fara gudanar da bincike tare da ƙara kaimi wajen gano mutanen da ake zargi da hannu a harin.

A sakamakon binciken, jami’an ’yan sanda sun kama mutane biyu da ake zargi da hannu a lamarin.

Waɗanda aka kama sun hada da Muhammad Bashir Sale, wanda aka fi sani da “Full”, mai shekaru 20, da Musa Sale Ahmad, wanda aka fi sani da “Abba”, mai shekaru 18.

Rundunar ta ce dukkan mutanen biyu mazauna unguwar Wuro Shie ne a Gombe.

A yayin binciken farko, ’yan sanda sun ce waɗanda ake zargin sun amsa cewa suna da hannu a cikin laifin.

Haka kuma, rundunar ta ce an kwato wata wuka mai kaifi wadda aka ajiye a matsayin shaida domin taimakawa wajen gudanar da binciken.

A halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin a Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar Gombe, wato State CID.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike cikin sirri domin tabbatar da cewa duk wanda aka samu da hannu a laifin ya fuskanci hukuncin da ya dace.

Rundunar ta kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa za ta ci gaba da daukar matakan kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da ƙara ƙaimi wajen yaki da miyagun laifuka a fadin jihar.

Ta bukaci jama’a da su kasance masu taka-tsantsan tare da gaggauta sanar da jami’an tsaro duk wani mutum, motsi ko wani abu da suka ga yana da nasaba da laifi.

Rundunar ta ce za ta sanar da jama’a duk wani sabon ci gaba da aka samu dangane da binciken.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Pantami, Mailantarki Da Garry Za Su Fafata A Sabon Zaɓen Fidda Gwani Na PDP A Gombe
Next Post: Rikicin Sarautar Akwa: Ƙungiyoyi Biyu Sunyi Arangama A Douala

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaba Tinubu Ya Tafi Kasar Faransa Afrika
Sarkin Gombe Ya Yabi Nasarorin Inuwa Yahaya A Fannonin Tsaro Da Raya Kasa Afrika
Sojin Saman Najeriya Sun Lalata Sansanonin ‘Yan Ta’adda Afrika
Harin Ukraine Yayi Mummunan Barna A Rasha Afrika
Shugaba Tinubu Zai Shafe Makonni Uku A Hutun Shekara-Shekara Afrika
Addini Ko Kabilanci Basu Da Gurbi Cikin Ta’addanci Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • An Bawa Fasto Yohanna Buru Sarautar “Jagoran Zaman Lafiyar Arewacin Najeriya”
  • INEC TA Fitar Da Jerin ’Yan Takarar Gwamnan Gombe, Ba A Ga Sunan Sheikh Pantami Ba
  • Inuwa Yahaya Ya Yi Alkawarin Barin Gombe Ba Tare Da Bashin Fansho Ba
  • NBA Gombe Ta Nemi IGP Ya Binciki Zargin Karɓar Kuɗi A FCID Annex Gombe
  • Ɗalibai 670 Sun Amfana Da Tallafin Jakakkuna Da Littattafai Daga Hukumar NEDC A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnan Gombe Ya Taya Sarkin Musulmi Murnar Cika Shekaru 70, Ya Yi Masa Addu’ar Ƙarin Lafiya Da Tsawon Rai Afrika
  • Sanyin Hunturu Yayi Ajalin ‘Yan Cirani A Morocco Afrika
  • Manya-Manyan Wasannin Wannan Makon Wasanni
  • Jirgin Sojojin Ruwa Yayi Gobara A Cross River Najeriya
  • Tinubu Ya Maye Gurbin Badaru Da Tsohon Soja Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Arsenal Ta Fara Kare Kambun Gasar Premier League Da Ci 3-0 A Kan Coventry City Wasanni
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.