Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

Amurka Tasakawa Sojin Rwanda Takunkumi
Published: March 3, 2026 at 12:32 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ranar Litinin, Amurka ta azawa rudunar sojin Rwanda takunkumi da wasu manyan hafsoshin kasar dangane da irin rawar da suke takawa a yaki da ake yi a gabashin jamhuriyar Demokuradiyyar kwango, kuma ta bukaci su janye daga yankin mai albarkatun ma’adinai ba tare da bata wani lokaci ba.

Rwanda dai ta jima tana musanta zargi daga kwango da MDD da manyan kasashen yammacin duniya suke yi mata cewa ita take daurewa Kungiyar ‘yan tawayen M23 gindi, wacce a bara tayi kukan kura a gabashin jamhuriyar kwangon, inda yanzu take rike da kasa fiye da a ko wani lokaci da ake wannan rikici.

Ma’aikatar kudi ta Amurka ta fada ranar Litinin cewa babu yadda za’a yi ‘yan tawayen M23 su sami nasarar kama kasa mai yawa haka ba tare da taimakon Rwanda ba. A nata bangaren ma’aikatar harkokin wajen Amurka tace, saboda goyon bayan da Rwanda take baiwa ‘yan tawayen M23 sun aikata mummunar barna da keta ‘yancin Bil’adama.

A cikin wata sanarwa da ta aikewa kamfanin dillancin labarai na Reuters, gwamnatin Rwandan tace takunkumin bashi da adalci domin ya auna bangare daya ne a yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla, kuma hakan “bai bayyana hakikanin gaskiyar abunda yake kasa ba, kuma ya dagula ainihin rikici da ake yi a yankin.

Afrika, Amurka, Labarai, Tsaro

Post navigation

Previous Post: China Ta Yi Kira Da Kasashen Gabas Ta Tsakiya Su Hada Kai
Next Post: Kasar Faransa Zata Bunkasa Nukiliyarta

Karin Labarai Masu Alaka

Masana Lafiya – Preeclampsia Cuta Ce Mai Hadari Amma Ana Iya Magance Ta Afrika
Shugaban Hukumar Kwallon Kafa Ta Senegal Yaki Amincewa Da Hukuncin CFA Afrika
Kasuwannin Hannayen Jari Suna Fuskantar Durkushewa Sakamakon Matsin Lambar Shugaba Trump Amurka
Kasar China Ta Daina Bada Bashi Da Dalar Amurka Sai Da Kudin Kasar Yuan Labarai
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Gombe Ya Ziyarci Pindiga Labarai
Amurkawa Suna Turuwa Zuwa Kasar Faransa Duk Da Rashin Jituwa A Tsakanin Kasashen Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kotun Kasar Rasha Ta Daure Dan Kasar Belarus Shekarar 22 A Kurkuku Labarai
  • An Yankewa Prime Ministan Kasar Tunisiya Hukuncin Shekaru 24 A Gidan Yari Afrika
  • Tinubu Ya Jaddada Buƙatar Kare Rayukan ‘Yan Afirka A Taron ECOWAS Afrika
  • Najeriya Ta Bawa Dan Takarar Guinea-Bissau Mafaka Afrika
  • Shugabannin Kasashen Sahel Sunyi Taro a Mali Afrika
  • Rasha Takai Mummunan Hari Birnin Kyiv Afrika
  • Wani Bincike Ya Nuna Cewar Da Wuya Iran Ta Bude Mashigin Hormuz Afrika
  • Rundunar Hadinkan Saudiya Tayi Ikirarin Mayar Da Martani Ga ‘Yan Aware Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.