Hukumomin gwamnati, masana kimiyya, ƙungiyoyin farar hula da masu ruwa da tsaki kan harkokin ci gaba a jihar Kaduna, sun yi kira ga ’yan kasuwa da ƙananan da matsakaitan masana’antu, SMEs, da su mayar da matsalolin sauyin yanayi, sarrafa shara da sauran ƙalubalen muhalli zuwa damammaki na kirkire-kirkire, samar da ayyukan yi da bunkasar tattalin arziki.
Masu ruwa da tsakin sun yi wannan kiran ne a yayin taron Kaduna Monthly Climate Hangout na watan Satumba, wanda Sakatariyar ITIEC ta shirya tare da haɗin gwiwar Desk na Climate Change and Environment na Interfaith Mediation Centre, IMC, Kaduna, da African Climate Reporters, ACR.
An gudanar da taron na yini guda mai taken “Ƙarfafa ’Yan Kasuwa da SMEs ta hanyar Noma Mai Jure Sauyin Yanayi, Kirkire-kirkiren Kore, Ciniki Mai Dorewa da Bunkasar Tattalin Arziki.”
Taron ya samu halartar jami’an gwamnati, manoma, ’yan kasuwa, masana kimiyya, ƙwararrun muhalli da sauran masu ruwa da tsaki.
Da yake jawabi a wajen taron, Manajan Hukumar Bunƙasa Ƙananan da Matsakaitan Kamfanoni ta Najeriya, SMEDAN, na jihar Kaduna, Malam Badamasi Yau Barau, ya ce sauyin yanayi ya riga ya fara shafar manoma, masu sarrafa amfanin gona da ’yan kasuwa, sakamakon sauyin ruwan sama, ambaliyar ruwa da kuma ƙarin zafin yanayi.
Barau ya ce ’yan kasuwa da ƙananan masana’antu bai kamata su ɗauki sauyin yanayi a matsayin matsalar gwamnati ko masana kimiyya kawai ba, yana mai cewa ana buƙatar kirkire-kirkire da zuba jari daga ɓangaren masu zaman kansu.
Ya ce noma mai jure sauyin yanayi ya wuce amfani da sabbin fasahohi kawai, domin ya haɗa da nemo hanyoyin da za su taimaka wajen ƙara samar da abinci tare da rage yawan albarkatun da ake amfani da su da kuma daidaita noma da sauyin yanayin.
A cewarsa, akwai damammaki a fannin ban ruwa mai amfani da hasken rana, inganta adana amfanin gona, rage asarar amfanin gona bayan girbi, ayyukan noma masu jure sauyin yanayi, da kuma mayar da sharar amfanin gona zuwa abincin dabbobi da takin zamani.
Manajan SMEDAN ya ƙarfafa gwiwar matasa da mata da su shiga sabbin harkokin kasuwanci masu alaƙa da muhalli, ciki har da sake sarrafa shara, sarrafa sharar gida, makamashi mai sabuntawa, marufi masu kare muhalli da noma mai jure sauyin yanayi.
Ya shawarci ’yan kasuwa da kada su jira komai ya zama cikakke kafin su fara, yana mai cewa su duba matsalolin da ke kewaye da su sannan su nemo hanyoyin kasuwanci da za su magance su.
Ya kuma bukaci ’yan kasuwa su ƙara samun sabbin ƙwarewa, su riƙa adana bayanan kasuwancinsu yadda ya kamata, su rungumi fasaha, su rage ɓarnar albarkatu tare da kafa haɗin gwiwa.
Ya ce horo kaɗai bai isa ba, sai an samu damar samun jari, kasuwanni, fasaha, rajistar kasuwanci da jagoranci daga ƙwararru.
Shi ma Kodinetan Hukumar Kula da Ka’idojin Muhalli ta Najeriya, NESREA, na jihar Kaduna, Emmanuel Dangari, ya ce ya kamata a haɗa kare muhalli da bunƙasar tattalin arziki.
Dangari ya ce ɓangaren noma na Najeriya na da babbar damar taimakawa wajen sauya tsarin tattalin arziki daga tsarin amfani da albarkatu sannan a zubar da su, zuwa tsarin circular economy, inda ake mayar da sharar gida zuwa abubuwan da za su sake amfani.
Ya ce ragowar amfanin gona, kashin dabbobi da sharar masana’antun sarrafa abinci za a iya mayar da su takin zamani, iskar gas ta biogas da takin gargajiya, wanda zai samar da ƙarin hanyoyin samun kuɗi ga manoma da ’yan kasuwa.
Ya kuma nuna damuwa kan ƙara yawan robobin da ake amfani da su a harkar noma, ciki har da kayan ban ruwa da buhunan takin zamani, yana mai gargadin cewa zubar da su ba bisa ƙa’ida ba na taimakawa wajen haifar da ambaliya da gurɓatar muhalli.
Dangari ya ƙarfafa gwiwar ƙananan masana’antu da ’yan kasuwa da su shiga harkokin tattara shara, sake sarrafa ta, samar da marufi masu ɗorewa, samar da biogas, ingantaccen ban ruwa da kuma amfani da manhajojin zamani wajen haɗa masu samar da shara da masu sake sarrafa ta.
Ya kuma bukaci masu samar da kayayyaki su ɗauki alhakin sharar marufin kayayyakin da suke samarwa ta hanyar tsarin Extended Producer Responsibility, yana mai cewa bin ƙa’idojin kare muhalli ya kamata ya kasance wani ɓangare na tsarin kasuwanci tun daga farko.
A nasa ɓangaren, Co-Executive Director na Interfaith Mediation Centre, IMC, Kaduna, Mista Samson Auta, ya yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati, ƙungiyoyin farar hula, ’yan kasuwa, manoma, masana kimiyya da al’umma wajen magance matsalolin muhalli.
Auta ya ce kare muhalli bai kamata a bar shi a hannun hukumomin gwamnati kaɗai ba, yana mai cewa haɗin gwiwar kowa ya zama dole wajen magance sauyin yanayi, gurɓatar muhalli, sare itatuwa da sauran matsalolin lalata muhalli.
Ya ce ya zama wajibi ƙungiyoyi da daidaikun mutane su haɗa kai wajen kare muhalli, domin illolin lalacewar muhalli na shafar al’umma ba tare da la’akari da matsayinsu na zamantakewa, addini ko tattalin arziki ba.
Auta ya kuma jaddada muhimmancin wayar da kan jama’a tare da ƙarfafa gwiwar al’umma da su mallaki shirye-shiryen kare muhalli.
Shi ma Shugaban Sashen Masu Rahoto Kan Kimiyya da Muhalli na African Climate Reporters, Comrade Ibrahima Yakubu, ya ce an shirya taron Kaduna Monthly Climate Hangout ne domin haɗa masu ruwa da tsaki a harkokin tattalin arziki da noma da masana kimiyya da ƙwararrun sarrafa shara, domin samar da hanyoyin magance sauyin yanayi da lalacewar muhalli.
Yakubu ya ce ’yan kasuwa, manoma masu kasuwanci, SMEs da ’yan kasuwa suna buƙatar ƙarin wayar da kai kan yadda sauyin yanayi da lalacewar muhalli ke shafar fannoni daban-daban na tattalin arziki.
Ya bayyana cewa a cikin shekaru biyar da suka gabata, Kaduna Monthly Climate Hangout ya samar da wani dandali da masana kimiyya, masana ƙasa, ’yan jaridar muhalli, ƙungiyoyin farar hula, kungiyoyi masu zaman kansu, masu kare muhalli da wakilan gwamnati ke musayar ilimi da tattauna hanyoyin kare muhalli.
A cewarsa, taron yana kuma samar da dama ga masana kimiyya da ’yan jarida wajen ƙarfafa haɗin gwiwa da inganta samun sahihin bayani kan sauyin yanayi, noma, sarrafa shara da kare muhalli.
Masu ruwa da tsakin sun amince cewa gina tattalin arzikin da zai iya jure sauyin yanayi na buƙatar ƙarin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati, ’yan kasuwa, manoma, cibiyoyin kuɗi, abokan hulɗar ci gaba da masu amfani da kayayyaki.
Sun jaddada cewa bai kamata a riƙa kallon noma, sarrafa amfanin gona da sarrafa shara a matsayin fannoni daban-daban ba, domin suna da alaƙa da juna kuma za su iya taimakawa wajen samar da ayyukan yi, rage gurɓatar muhalli da inganta rayuwar al’umma.
Dangari ya ƙarfafa gwiwar ’yan kasuwa da su kalli ƙalubalen muhalli a matsayin damammaki na kirkire-kirkire, yana mai cewa ya kamata a sauya tunani daga shara zuwa albarkatu, daga gurɓata muhalli zuwa rigakafin gurɓacewa, da kuma daga ƙalubalen muhalli zuwa damammakin kasuwanci.


