Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • An Bawa Fasto Yohanna Buru Sarautar “Jagoran Zaman Lafiyar Arewacin Najeriya” Afrika
  • Inuwa Yahaya Ya Yi Alkawarin Barin Gombe Ba Tare Da Bashin Fansho Ba Afrika
  • NBA Gombe Ta Nemi IGP Ya Binciki Zargin Karɓar Kuɗi A FCID Annex Gombe Afrika
  • Ɗalibai 670 Sun Amfana Da Tallafin Jakakkuna Da Littattafai Daga Hukumar NEDC A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Gombe Ta Ƙarfafa Matakan Kare Dabbobi Daga Cututtuka Afrika

’Yan Sandan Bauchi Sun Kama Mutane Biyu Kan Zargin Kashe Jariri
Published: September 25, 2026 at 2:26 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rundunar ’Yan Sandan jihar Bauchi ta tabbatar da kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a wasu munanan laifuka guda biyu da suka faru a ƙananan hukumomin Katagum da Itas/Gadau.

A cewar sanarwar da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar SP Nafiu Habib, ya fitar a ranar 25 ga Satumba, 2026, lamarin farko ya faru a yankin Zirami da ke Azare.

Rundunar ta ce a ranar 24 ga Satumba, wata mata mai shekaru 20 ta kai jaririyarta mai wata huɗu, Fatimah Muhammad, zuwa Ofishin ’Yan Sandan Azare bayan ta same ta ba ta numfashi.

Matar ta bayyana cewa ta bar jaririyar tana barci a gida yayin da ta je gidan maƙwabcinta domin gyaran gashi. Bayan ta dawo, ta ce ta tarar da mijinta, Muhammad Garba Ladan mai shekaru 27, yana fitowa daga ɗakin.

Rundunar ta ce matar ta kuma yi zargin cewa mijin nata ya taɓa ƙoƙarin cutar da jaririyar a baya.

Bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda sun garzaya da jaririyar zuwa Babban Asibitin Azare, inda likita ya tabbatar da rasuwarta sakamakon shaƙewa, kamar yadda sanarwar rundunar ta bayyana.

AN KAMA WANDA AKE ZARGIN, KUMA ANA CI GABA DA GUDANAR DA BINCIKE.

An Kama Wani Kan Zargin Kashe Mace Bisa Zargin Maƙarƙashiyar Boka

A wani lamari makamancin haka, rundunar ta ce ta kama wani matashi mai shekaru 25, Haruna Amadu, bisa zargin shiga gidan wata mata mai shekaru 60, Hafsatu Ya’u, a ƙauyen Wasari da ke Gadau District.

Rundunar ta ce wanda ake zargin ya kai wa matar hari bayan ya zarge ta da hannu wajen rashin lafiyar wata mata mai suna Maryam Amadu, wadda ke fama da rashin lafiya.

An garzaya da Hafsatu zuwa Babban Asibitin Azare domin samun kulawar gaggawa, amma likita ya tabbatar da rasuwarta.

Rundunar ta tabbatar da kama wanda ake zargin, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Rundunar ’Yan Sandan jihar Bauchi ta ce za a tura duka shari’o’in zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jiha (SCID) da ke Bauchi domin gudanar da cikakken bincike.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yi Allah-wadai da ɗaukar doka a hannu, kisan da ake dangantawa da zargin maƙarƙashiyar bokanci, da kuma cin zarafin mata da yara.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu, tare da kai rahotannin laifuka ga hukumomin tsaro domin ɗaukar matakin da ya dace.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Sauyin Yanayi: Masana A Kaduna Sunyi Kira Ga Yan Kasuwa Su Mayar Da Shara Zuwa Kudi
Next Post: Pantami, Mailantarki Da Garry Za Su Fafata A Sabon Zaɓen Fidda Gwani Na PDP A Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

Jagoran Kwankwasiya A Najeriya Ya Koma Jam’iyar ADC Labarai
Aliko Dangote: Faruk Ahmed Ya Ci Amanar ‘Yan Najeriya! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Kwamitin Malamai Don Binciken Rikicin Addini Afrika
Burkina Faso Ta Sako Jami’an Rundunar Sojin Saman Najeriya 11 Da Aka Tsare Tsaro
Dan Majalisar Wakilai Yaya Bauchi Tongo Ya Rasu A Abuja Bayan Doguwar Jinya Afrika
JEI Da Abokan Hulɗar Sun Gudanar Da Aikin Shuka Itatuwa Domin Bikin Ranar Muhalli Ta Duniya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

https://www.youtube.com/watch?v=sainfSmn-EQ

Sabbin Labarai

  • An Bawa Fasto Yohanna Buru Sarautar “Jagoran Zaman Lafiyar Arewacin Najeriya”
  • INEC TA Fitar Da Jerin ’Yan Takarar Gwamnan Gombe, Ba A Ga Sunan Sheikh Pantami Ba
  • Inuwa Yahaya Ya Yi Alkawarin Barin Gombe Ba Tare Da Bashin Fansho Ba
  • NBA Gombe Ta Nemi IGP Ya Binciki Zargin Karɓar Kuɗi A FCID Annex Gombe
  • Ɗalibai 670 Sun Amfana Da Tallafin Jakakkuna Da Littattafai Daga Hukumar NEDC A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Iran Ta Kama Wani Jirgin Ruwa Shake Da Mai Labarai
  • Gwamnatin Najeriya Da Haɗin Guiwar Gwamnatin Jihar Zamfara Suna Shirin Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Jihar Rumbun Hotuna
  • Hukumar Hakar Ma’adanai A Kasar Zambiya Ta Dakatar Da Ayyukanta Kimiya
  • ‘Yan Uwan Wadanda Aka Kashe Sunkai Kara Kotu Amurka
  • Amurka Tafara Yiwa Kasar Iraq Barazana Amurka
  • Harin Isra’ila A Gaza Da Jirgi Maras Matuki Ya Kashe Mutane Afrika
  • Arsenal Ta Doke Manchester City 3-0, Ta Ɗauki Kofin Community Shield Wasanni
  • Bayan Shafe Shekaru Hudu A Mulki Sarkin Hausawan Ibadan Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.