Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

A Hudubar Kirsimeti Paparoma Leo Ya Jajantawa Al’ummar Falatsinu A Yankin Zirin Gaza
Published: December 25, 2025 at 8:19 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

A hudubar Kirsimetinsa ta farko a yau alhamis, Paparoma Leo, ya nuna jimamin hali da al’ummar Falatsinu suke ciki a yankin zirin Gaza, yana mai furta cewa ta yaya mai hankali zai kalli Falasdinawan dake zaune cikin tanti, inda suka yi makonni suna fama da ruwan sama da iska da kuma sanyin hunturu.

Paparoma Leo, wanda shine ba Amurke na farko da aka taba zaba Paparoma a watan Mayu, wanda kuma wannan shine kirsimetinsa na farko a kan wannan mukami, bai saba fitowa yana magana kan batutuwan siyasa a hudubarsa ba.

Sabon Paparoman ya sha yin maganganu a kan halin da Falasfinawa suke ciki a Gaza, inda a watan da ya shige ya fadawa ’yan jarida cewa hanya daya tak ta kawo karshen takun sakar da aka jima ana yi a tsakanin Isra’ila da Falasdinawa ita ce ta kafa kasar Falasdinu.

Haka kuma Paparoma Leo ya nuna jimamin halin da ‘yan gudun hijira suke ciki a nahiyar Amurka, Paparoman wanda can baya ya sha sukar shugaba Donald Trump na Amurka game da matakan da yake dauka a kan ‘yan gudun hijira, bai ambaci sunan shugaban a hudubar tasa ta yau ba.

Amma a hudubar da yayi ta jajiberin kirsimeti a ranar laraba, Paparoman ya ce kin taimakawa talakawa ko baki, tamkar kin bin umurnin Allah ne.

Amurka

Post navigation

Previous Post: Harin Bom Din Maiduguri Ya Kashe Mutane Biyar Ya Raunata Fiye Da Talatin
Next Post: Jirgin Sama Mai Saukar Ungulu Ya Kashe Mutane Biyar A Tanzaniya

Karin Labarai Masu Alaka

Iran Zata Kai Hari Tashar Makamashin Ruwa A Gulf Afrika
Shugaba Donald Trump Yabada Umarnin Hana Jiragen Dakon Mai Shiga Venezuela Amurka
Amurka Ta Kai ‘Yan Cirani Kamaru Afrika
Amurka Tafara Mayar Da ‘Yan Afghanistan Da Suka Makale A Qatar Amurka
Shugaba Trump Yayi Barazanar Tura Sojoji Ga Masu Zanga Zanga Amurka
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Ta Saka Takunkumi Visa Ga Wasu ‘Yan Rwanda Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Somaliya: Ba Za Mu Dauki Wulakancin Donald Trump Ba! Sauran Duniya
  • Bincike Yanuna Kasashen Afirka Suna Cikin Mafiya Cin Bashi A Duniya Afrika
  • An Sako Dan Siyasar Kasar Venezuela Daga Gidan Yari Labarai
  • Dakaru Sun Hallaka ’Yan Ta’adda Masu Yawa – DHQ Afrika
  • Hukumar Hasashen Kasuwanci Na Zargin Saida Bayanan Sirri Amurka
  • An Kashe Mutane 7 A Unguwar Dorayi Dake Kano Najeriya
  • Sarkin Gombe Ya Ziyarci Gwamna Inuwa Yahaya Afrika
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Alhamis 11.20.2025 Rediyo
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.