Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Aminu Tambuwal Ya Fice Daga PDP Ya Koma ADC
Published: March 12, 2026 at 7:15 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Sanata Aminu Waziri Tambuwal, tsohon Gwamnan jihar Sokoto kuma Sanata mai wakiltar Mazabar Sokoto ta Kudu, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tare da komawa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).

A cikin wata wasika mai kwanan wata 11 ga Maris, 2026 wadda ya aikewa da shugaban jam’iyyar PDP na gundumarsa ta Tambuwal/Shinfiri da ke Karamar Hukumar Tambuwal a jihar Sokoto, Sanata Tambuwal ya bayyana cewa ya ajiye zama dan jam’iyyar PDP nan take.

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai a Najeriyan ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne bayan zurfin tunani da kuma tuntuba mai fadi da abokan siyasa da magoya bayansa.

A cewarsa, rikice-rikicen cikin gida, sabanin ra’ayi tsakanin shugabannin jam’iyyar da kuma rarrabuwar kawuna da ke ci gaba da addabar PDP sun sa ya zama da wahala a gare shi ya ci gaba da kasancewa a cikinta.

Ya kara da cewa wadannan matsaloli sun raunana hadin kai da kuma alkiblar da jam’iyyar ta tsaya a kai a baya.

Sanata Tambuwal ya kuma nuna godiyarsa ga jam’iyyar PDP bisa damar da ta ba shi ya yi wa kasa hidima a mukamai daban-daban, ciki har da Kakakin Majalisar Wakilai da kuma Gwamnan jihar Sokoto na wa’adi biyu.

Bayan sanar da ficewarsa daga PDP, Sanata Tambuwal ya tabbatar da cewa ya shiga jam’iyyar ADC tare da wasu daga cikin abokan siyasa da magoya bayansa.

Ya bayyana cewa matakin ya samo asali ne daga yakinin da yake da shi na cewa Najeriya na bukatar wata dandalin siyasa mai karfi da za ta ginu kan gaskiya, rikon amana, hada kai da kuma cikakken kudurin bunkasa kasa.

Sanatan ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da yi wa Najeriya hidima tare da kare muradun dimokuradiyya, adalci da hadin kan kasa.

Afrika, Labarai, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Kasar Gabon Ta Nemi Tallafin Asusun Bada Lamuni Na IMF
Next Post: Nan Gaba Kadan Kwallon Badminton Zata Samu Karbuwa Kamar Kwallon Kafa A Duniya

Karin Labarai Masu Alaka

Jami’an Tsaron Pakistan Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Labarai
Gobara Ta Tashi A Hukumar FIRS Dake Abuja Najeriya
Dottin Shara Ya Damu Jama’ar Havana Kasar Cuba Labarai
Guinea Bissau Ta Tsaida Gwaje-Gwajen Allurar Rigakafin Shawara A Kasar Labarai
‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika
Kotu A Birnin Tarayya Abuja Ta Bada Belin Tsohon Minista Abubakar Malami Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Netanyahu Ya Umarci Rundunar Sojoji Takara Fadada Ayyukanta A Lebanon Afrika
  • Gasar Cin Kofin Nahiyar Afrika A Wannan Makon Wasanni
  • Gwamnatin Kano Ta Samar Da Wasu Dabarun Inganta Tsaro Tsaro
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran Amurka
  • Wasan Hamayya (Istanbul Derby) Fenerbahçe Da Galatasaray 1-1 Labarai
  • Sakataren Gwamnatin Amurka Ya Bayyana Bawa Kungiyoyin Agaji Damar Kai Taimako Sudan Amurka
  • Iran Ta Kama Wasu ‘Yan Leken Asiri Afrika
  • Kungiyar Kwadago Ta Shirya Zanga-Zanga A Najeriya Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.