Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Najib Razak Zai Kara Shekaru 15 A Gidan Yari Saboda Cin Zarafin Kujerar Mulki
Published: December 27, 2025 at 5:57 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

An yankewa tsohon fira ministan Malaysia, Najib Razak karin shekaru 15 a gidan yari ranar Jumu’a, kuma an ci shi tarar dala miliyan dubu biyu da dari takwas saboda cin zarafin kujerar mulki da batar da wasu kudin haramun, a shari’a mafi girma na miliyoyin daloli daga asusun raya kasa na IMDB, kuma ana ganin hukuncin zai yi tasiri sosai a tsarin siyasar kasar.

Masu bincike na Amurka da Malaysia sun ce an sace zunzurutun kudi akalla dala miliyan dubu 4 da dari biyar daga wannan asusun da cikakken sunansa shine “One Malaysia Development Berhad” wanda Najib ya taimaka wajen kafawa a 2009, a watanni 9 na wa’adinsa na farko kan karagar mulkin kasar dake kudu maso gabashin Asiya.

Fiye da dala miliyan dubu daya na wadannan kudade sun sulale zuwa cikin asusun ajiyar bankin Najib mai shekaru 72 da haihuwa.

An fara saka shi a kurkuku a shekarar 2022 a wata shari’ar da ta shafi wannan asusu, inda tun da yake ikirarin an dora masa laifi ne, a badakalar kudin mafi girma a kasar.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Shugaban Ukraine Ya Tattauna Da Trump Akan Zaman Lafiya
Next Post: CAF Ta Ci Tarar Ƙasar Masar Dala 5,000 AFCON 2025

Karin Labarai Masu Alaka

Jami’an Tsaron Pakistan Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Labarai
ADC Ta Kaucewa INEC Ta Gudanar Da Babban Taro Labarai
Mamakon Ruwan Sama Da Iska Ya Hallaka Mutane Uku A Jihar Yobe Labarai
An Sako Dan Siyasar Kasar Venezuela Daga Gidan Yari Labarai
Wata Biyu Najeriya Bata Bada Lasisin Shigo Da Mai Daga Ketare Ba Labarai
Kamfanin NNPC Yana Tattaunawa Da Wani Kamfanin Kasar China Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Hukumar Tsaron Teku A Libya Tafara Janye Jirgi Mai Dauke Da Iskar Gas Labarai
  • An Kama Maharan Bom Din Maiduguri Tsaro
  • Za’a Ninka Shekarun Zama A Gidan Kurkuku Ga Masu Auren Jinsi A Senegal Afrika
  • Kasar China Ta Kaddamar Da Rawar Daji A Yankin Taiwan Labarai
  • Shugaba Tinubu Ya Kara Aika Sunayen Jakadu Ga Majalisa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugaban Trump: Washington Zatayi Cinikayya Da Indiya Amurka
  • Matasa Sun Sayawa Ferfesa Pantami Fom Din Takarar Gwamnan Gombe Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Horar Da Matasa Sama 7,000 A Matsayin Masu Tsaron Daji Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.