Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Kungiyar HPV A Jihar Gombe Ta Jagoranci Yaki Da Karuwar Cutar Daji
Published: April 5, 2026 at 10:15 AM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: April 6, 2026

Kungiyar HPV ta jihar Gombe ta shirya wani gangamin wayar da kan al’umma, inda ta hada ‘yan jarida, ma’aikatan lafiya, masana ilimi, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki domin tunkarar barazanar karuwar cutar daji a jihar.

Da yake jawabi a wajen taron, Farfesa Muhammad Manga ya bukaci mahalarta su kirkiro dabaru masu amfani domin hana yaduwar cutar daji, musamman cutar sankarar mahaifa, da kuma yadda za a magance sauran nau’o’in cutar a cikin al’umma.

Ya bayyana cewa an hada bangarori daban-daban cikin shirin ne da gangan, musamman mambobin Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya, domin inganta tattaunawa da gano hanyoyin magance matsalolin cutar daji.

Farfesa Manga ya yaba wa mahalarta taron bisa jajircewarsu, yana mai jaddada cewa ana iya warkar da cutar daji idan aka gano ta da wuri. Ya kuma bukaci jama’a da su gaggauta neman kulawar likita idan sun lura da wasu sauye-sauye ko alamomi da ba su saba ba, tare da karfafa musu gwiwa su yada wannan sakon wayar da kai a cikin al’ummominsu.

Sauran masu jawabi, ciki har da shugabar taron, Dakta Halima Usman Farouk, Farfesa Danladi Adamu Bojude da Ferfesa Aliyu Lawal na Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe, da kuma shugabannin al’umma Musa Mustafa da Danimoh Mustafa, sun jaddada bukatar kara hadin gwiwa tsakanin ‘yan jarida, ma’aikatan lafiya da sauran masu ruwa da tsaki domin yakar cutar daji yadda ya kamata.

Sun bayyana wasu daga cikin nau’o’in cutar daji da suka fi yawaita a jihar da suka hada da na mama, huhu, mafitsara ta maza, mahaifa, hanta, ciki, pankiriyas, koda, mafitsara, fata, kwakwalwa, ovaries, mahaifa ta mata da kuma esophagus.

Masu jawabin sun bukaci jama’a da su rika anfani da ayyukan kiwon lafiya da ake da su ta hanyar yin gwaje-gwaje akai-akai. Wadanda aka gano suna dauke da cutar an shawarce su da su nemi magani da wuri, yayin da sauran kuma aka karfafa musu gwiwa su yi allurar rigakafi inda ya dace.

Kungiyar ta sake jaddada kudirinta na kara fadada shirye-shiryen wayar da kai da kuma inganta samun damar ayyukan rigakafi domin rage mace-macen da ke da alaka da cutar daji a Jihar Gombe.

Daga jihar Gombe ga Rahoton Wakilin GTA Hausa Amurka Ke Magana Aliyu Bala Gerengi

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/04/HPV-GOMBE.mp3
Afrika, Kiwon Lafiya, Labarai, Najeriya, Rumbun Hotuna

Post navigation

Previous Post: Majalisar Dokokin Kamaru Ta Amince Da Wasu Sauye Sauye
Next Post: Rundunar Sojin Najeriya Ta Kubutar Da Wasu Mutane 31 Da Aka Yi Garkuwa Dasu

Karin Labarai Masu Alaka

Akwai Nasara A Tattaunawar Da Akeyi Tsakanin Iran Da Amurka Afrika
Jam’iyar APC A Jihar Gombe Ta Tsayar Da Jamilu Isiyaku Gwamna Takarar Gwamna Afrika
Ministan Yaɗa Labarai: Ceto Daliban Neja An Samu Natsuwa A Kasa Labarai
Kasar Togo Ta Kori Paul Henri Damiba Zuwa Kasar Sa Ta Haihuwa Afrika
Hukumomi A Kasar Syri Lanka Suna Kokarin Fidda Jirgin Yakin Iran Daga Kasar Afrika
Kasar Ukraine Ta Yabawa Tarayyar Turai Bisa Bata Tallafi Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • IBB: Ba Shakka Abiola Ya Lashe Zaben Yuni 12 Rediyo
  • Gombe Ta Ƙarfafa Matasa da Ƙwarewar da Za Ta Kai Su Masana’antar Mai Da Iskar Gas Afrika
  • Motsepe, Daga 2028 AFCON Zata Sauya Daga Shekaru Biyu Zuwa Hudu Wasanni
  • Nnamdi Kanu Ya Nemi A Mayar Da Shi Abuja Daga Gidan Yarin Sokoto Labarai
  • Trump Yace Amurka Ta Kai Hare-Hare Masu Yawa Akan ‘Yan Ta’adda A Najeriya Amurka
  • Amurka Ta Nuna Damuwa Kan Matsalar ‘Yan Gudun Hijira A Najeriya Najeriya
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • ‘Yan Bindiga Sun Kama Akalla Mutane 13 A Wani Coci A Jihar Kogi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.