Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Gwamna Inuwa Yahaya ya Rusa Majalisar Zantaswa ta Jihar Gombe
Published: April 8, 2026 at 5:35 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: April 9, 2026

A zaman Majalisar Zantaswar jihar Gombe Karo na 53 Gwamna Inuwa Yahaya ya rusa Majalisar Zartarwa ta Jihar a yau laraba 08 Afrilun 2026

“Mun rusa majalisar zartarwa ta jiha ne don baiwa kwamishinonin mu dake da sha’awar takara a zaben 2027 dake tafe dama su cinma muradun su na siyasa. Bayan kwamishinoni Kazalika na bada umurni wa duk masu mukamai na siyasa a matakai daban daban dake sha’awar takara a zaben dake tafe da su ajiye aikin su daga nan zuwa 10th April, 2026 don cinma burin su na takara a mukaman da suke muradin nema. Ina musu godiya maras adadi sabida rawar da suka taka wajen nausa gwamnatin mu gaba cikin kusan shekaru uku da mukayi a zangon gwamnati na na biyu”

Gwamna Inuwa Yahaya biyo bayan rusa majalisar zartarwa ta jiha da yayi.

Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, ya rushe Majalisar Zartarwar Jihar, wanda hakan ya kawo ƙarshen wa’adin kwamishinonin da suka yi aiki a majalisar zartaswar tsawon shekaru biyu da rabi da suka gabata.

An sanar da wannar shawara ce yau Laraba yayin wani taron manema labarai da Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya jagoranta jim kaɗan bayan zaman Majalisar Zartarwar karo na 53.

Farfesa Njodi ya bayyana cewa Gwamna Inuwa Yahaya ya umarci duk kwamishinonin su miƙa harkokin ma’aikatunsu ga manyan Sakatarori nan da ranar Juma’a, 10/04/2026, don ci gaba da shugabanci cikin kwanciyar hankali a ma’aikatun.

Farfesa Njodi ya ƙara da cewa a lokacin zaman, Gwamna Inuwa Yahaya ya miƙa godiya ga kwamishinonin saboda sadaukarwa, biyayya da jajircewarsu wajen ciyar da jihar gaba, tare da yaba musu kan rawar da suka taka a ɗaiɗaikunsu da kuma a ƙungiyance kan manufofi da shirye-shiryen da suka yi tasiri ga rayuwar al’ummar jihar.

Ya ƙara da cewa Gwamnan ya yi musu fatan alheri a harkokin da za su yi nan gaba, yana mai bayyana ƙwarin gwiwar cewa da yawa za su ci gaba da bada gudummawa mai ma’ana ga ci gaban Jihar Gombe dama ƙasa baki ɗaya.

A wani lamarin makamancin haka, Gwamnan ya umarci duk waɗanda aka naɗa a muƙaman siyasa, ciki har da mataimaka da masu riƙe da muƙaman siyasa dake son tsayawa takara a babban zaɓen 2027 mai zuwa, su yi murabus daga mukamansu ya zuwa ranar Juma’a 10/04/2026.

An ɗauki wannan matakin ne don tabbatar da gaskiya, riƙon amana da kuma bin ƙa’idoji da dokokin zaɓe.

A yayin zaman majalisar na bankwana, kwamishinonin sun yi cikakken nazari kan ayyukansu tun lokacin da aka rantsar da su, sannan suka yi nazari kan gudummawar da majalisar ta bayar ga ƙudurin ci gaba na gwamnati.

Sun yaba da muhimman ci gaban da aka samu a fannoni daban-daban na tattalin arziƙin jihar.

A ƙarshen zaman, majalisar ta kaɗa ƙuri’ar amincewa da Gwamna Inuwa Yahaya, inda ta yaba da salon jagorancinsa, da alƙiblar manufofi da jajircewarsa wajen sauya Jihar Gombe.

Sun bayyana cewa a ƙarƙashin jagorancinsa, jihar ta shaida gagarumin ci gaba a fannin samar da ababen more rayuwa kamar kiwon lafiya, ilimi, da sauye-sauyen tattalin arziki da sauransu, wanda hakan ya sanya Gombe ta zama jihar da ake samun ci gaba a fannin shugabanci a Najeriya.

Kwamishinonin masu barin gado sun nuna matuƙar godiya ga Gwamnan bisa damar da ya ba su na yiwa jihar hidima a irin wannan mataki, inda suka bayyana wa’adin aikinsu a matsayin mai tasiri da armashi, suna masu cewa suna alfahari da bada gudummawa ga nasarorin da gwamnatin ta samu.

Sun yi alƙawarin ci gaba da biyayya da goyon bayansu ga Gwamnan da kuma hangen nesansa na mayar da Jihar Gombe mai arziki da wadata, ko da kuwa sun koma ga harkoki na ƙashin kansu.

A lokacin taron manema labaran, Sakataren Gwamnatin ya isar da godiyar gwamna Inuwa Yahaya ga manema labarai bisa rawar da suke takawa a matsayin abokan hulɗar ci gaba da kuma goyon bayan da suke bayarwa wajen tallata manufofi da shirye-shiryen wannar gwamnatin.

Labarai, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Rundunar Sojin KTK Ta Harba Makami Teku
Next Post: Kasashen Amurka,Israela Da Iran Sun Amince Da Dakatar Da Yaki

Karin Labarai Masu Alaka

Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
An Harbo Jirgin Yakin Amurka A Iran Amurka
Akwai Yiwuwar Farashin Mai Zai Kara Tashi Afrika
Tsarin Haraji Mai Cike Da Ayoyin Tambaya Na Shirin Fara Aiki Labarai
Gwamnatin Najeriya Tace A Maboyar ‘Yan Ta’adda Aka Kai Harin Jilli Afrika
Kungiyar ‘Yan Jarida Ta Najeriya Ta Tabbatar Da Kyautata Rayuwar Mambobin ta Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Trump Yace Zai Dakatar Da Kai Hari Cibiyar Makamashin Iran Afrika
  • An Bude Kamfanin Sarrafa Ma’adanai A Kasar Mozambique Labarai
  • Take Hakkin Dan Adam Zai Haifar Da Juyin Juya Hali A Najeriya Najeriya
  • Amurka Zata Fara Sayar Da Maganin Hana Kiba Da Jin Yunwa Amurka
  • Gwamnan Gombe Ya Taya Sarkin Musulmi Murnar Cika Shekaru 70, Ya Yi Masa Addu’ar Ƙarin Lafiya Da Tsawon Rai Afrika
  • Hawan Nasarawa A Jihar Kano Afrika
  • Malaman Tsangaya A Gombe Sun Goyi Bayan Inuwa Yahaya Da Jamilu Gwamna Afrika
  • Anfara Tantance Lafiyar Maniyyatan Jihar Gombe Kiwon Lafiya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.