Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Shugaba Tinubu Ya Ayyana Dokar-Ta-Baci A Fannin Tsaro
Published: November 27, 2025 at 1:24 AM | By: Yusuf Aliyu Harande

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya ya ayyana dokar-ta-baci a bangaren tsaro a fadin kasar, ya umurci rundunar soja da ta ‘yan sanda da su gaggauta daukar dubban sabbin kurata domin shawo kan tashe-tashen hankula a kasar.

Shugaba Tinubu yace za a dauki sabbin ‘yan sanda dubu 20, abinda zai kara yawansu zuwa dubu 50, ya kuma bayar da iznin yin amfani da sansanonin masu aikin bautar kasa a zaman wuraren horas da sabbin kuratan. Har ila yau ya bada umurnin janye ‘yan sandan dake gadin manyan mutane, a sake maida su wurin horaswa domin a tura su bakin daga.

Shugaban na Najeriya ya ba ‘yan sandan leken asiri na cikin gida, DSS, izinin tura kwararrun masu gadi zuwa cikin dazuzzuka tare da diban wasu kari domin zakulo ‘yan ta’adda dake boye cikin dazuzzuka.

Tinubu ya ce daga yanzu babu wurin buya ga dillalan shedan a cikin daji.

Wannan jawabi na shugaba Tinubu ya biyo bayan hare-haren da aka kai cikin ‘yan kwanakin nan a jihohin Kebbi, Borno, Zamfara, Naija, Yobe da Kwara inda aka kashe fararen hula da dama aka saci wasu.

Shugaban na Najeriya yayi kira ga majalisar dokoki da ta sake nazarin dokokin kasa don ba jihohi ikon kafa rundunonin ‘yan sanda, yayin da ya roki makiyaya da su rungumi tsarin yin kiwo a wurin da za a kebe na kiwo zalla, su kuma mika makamansu don gujewa yawan fadace fadace da manoma.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Shirin Dare 26.11.2025
Next Post: Sojojin Da Suka Kifar Da Farar Hula A Guinea-Bissau Sun Sanar Da Cewa!

Karin Labarai Masu Alaka

Nada Jakadu Da Tinubu Yayi Sako Ne Ga ‘Yan-Arewa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Kwararru Sun Tabbatar Da Lafiyar Kangimi Dam Bayan Binciken Tsaro Afrika
Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
Uefa Ta Zabi Artan, Ya Jagoranci Wasan Cin Kofin Uefa Super Cup Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
An Gano Gawar Dan Yawon Bude Ido A Kasar Chadi Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • A Kowacce Rana Kasar China Tana Sayan Danyen Mai Ganga Dubu 600 Daga Kasar Venezuela Amurka
  • Gobara Ta Tashi A Hukumar FIRS Dake Abuja Najeriya
  • Najeriya Ta Mika Koke Ga FIFA Tana Zargin DR Congo Ta Sanya ‘Yan Wasan Da Basu Cancantaba Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ECOWAS Da AU Sun Nuna Damuwa Kan Juyin Mulki A Guinea-Bissau Afrika
  • China Ta Dawo Da Harajin Magungunan Hana Haihuwa Labarai
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Tarayya: Bikin Al’adun Argungu Ya Karbu A Idon Duniya Labarai
  • Dakarun Zaman Lafiya Na Majalisar Dinkin Duniya Sun Rasa Rayukan Su Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.