Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Allah Ya Yi Wa Sheikh Dahiru Bauchi Rasuwa
Published: November 27, 2025 at 9:55 AM | By: Bala Hassan | Updated: November 27, 2025

A daren jiya Laraba jikin malam yayi zafi, kuma da safiyar yau Alhamis, Allah yayi wa fitaccen Malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi rasuwa.

Sheikh Dahiru Bauchi ya rasune yana da shekaru 102 bayan gajeruwar rashin lafiya. Ɗan margayi, Sayyadi Ali Dahiru Usman Bauchi ne, ya sanar da rasuwar malamin. Ya ce sun karɓi wannan ƙaddara tare da gode wa Allah bisa rayuwar da malamin ya yi.

“Tabbas Sheikh ya koma ga Mahaliccinsa. Daga Allah muke, kuma gare shi za mu koma,” in ji Sayyadi.

“Lokacin Sheikh ya yi. Mun gode wa Allah Maɗaukaki. Ya bai wa Sheikh tsawon rai, kuma rayuwarsa ta yi kyau. Alhamdulillah,” in ji shi.

Rahotanni sun bayyana cewar jikin malamin ya tashi a ranar Laraba, inda aka garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi ATBU, inda ya rasu da sanyin safiyar ranar Alhamis.

Za a yi jana’izar Dahiru Bauchi gobe ranar Juma’a.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi, daya ne daga cikin manyan Malaman addinin Musulunci dake Nijeriya, kuma shine Babban jigo a darikar Tijjaniyya a Nijeriya da Afrika, kuma shine mataimakin shugaban Majalisar koli da ke bayar da fatwa a addinin Musulunci a Nijeriya.

Ga kadan daga cikin tarihin Sheihi:

A zantawar da yayi da manema labarai shekarun baya a Bauchi, Shehu Dahiru ya bada takaitaccen tarihinsa inda yace “Ni dai Bafulatani ne, dukanin kakannina hudu Fulani ne, domin kowane mutum yana da kakanni hudu ta wajen mahaifinsa biyu, ta wajen mahaifiyarsa biyu.

To ni dukanin kakannina Fulani ne babu inda muka hadu da wata kabila ta kowace fuska. Mu Fulanin Bauchi ne a lokacin da Jihar Bauchi take hade da Jihar Gombe. Bayan da aka raba Jihar Bauchi da Jihar Gombe, sai muka zama mu Fulanin Jihar Bauchi ne, a lokaci guda kuma Fulanin Jihar Gombe ne.

Ta wajen mahaifina ni Bafulatanin Jihar Bauchi ne, ta wajen mahaifiyata ni Bafulatanin Nafada ne da ke Jihar Gombe. An haife ni ne a watan Janairun 1927 wanda ya yi daidai da watan Muharram 1346 Bayan Hijira a ranar Laraba.

Sunan mahaifina Alhaji Usman dan Alhaji Adamu, shi mahaddacin Alkurani ne. Na rayu ne a hanunsa shi ya koya mini karatu har na haddace Alkurani a hannunsa. Sunan mahaifiyata Hajiya Maryam. Bayan na haddace Alkurani a hannun mahaifina ne ya tura ni duniya domin in je in gyara tilawata ta Alkurani.

Na shiga duniyar Allah Ya taimake ni na gyara tilawar tawa, lamarin da ya sanya wadansu kan ce mini Gwani na Alkurani, wadansu mutanen kuwa kirana suke yi da Gangaran a fagen haddar Alkurani. Bayan nan sai mahaifina ya ce zai tura ni duniya in je in sake nemo ilimi, daga nan aka turo ni nan Bauchi domin neman ilimi.

Na fara neman ilimi ban riga na samu ilimin da yawa ba, sai Allah ya sa Failar Shehu Ibrahim Kaulaha din nan ta bayyana. Dama mahaifina dan Tijjaniyya ne Mukaddami ne ta salsalar Umaru Futi, wato ta wajen Muhammadu Ghali.

Kuma shi mahaifina ne ya ba ni darikar Tijjaniyya. Bayan da muka shiga Failar Shehu Ibrahim, sai ya zama kowace harka tawa sai ta hada da maganar Shehu Ibrahim. Alhamdulillahi na samu rabo mai tarin yawa a sha’aninsa, na soma yin tafsirin Alkurani ne a wajajen 1950, sannan na yi aurena na farko a 1948.

Cikin alherin da Allah Ya yi mini, yayana tun suna qanana suke haddace kurani. Da farko yayana suna haddace kurani tun suna yan shekara 11, aka dawo 10, aka zo 9 har ya zamana cewa akwai yayana da suka haddace kurani suna yan shekara bakwai-bakwai da haihuwa”.

Yace Abin da ya fi ba ni shaawa a rayuwata , irin yadda na mayar da kur’ani sana’ata da kuma yadda na rungumi darikar Tijjaniyar nan ta zama rayuwata, kuma da dukanin wani mutumin da yake dangantuwa da son Annabi da son Allah ina sha’awar in sadu da shi, A duk lokacin da nake hutu ina shagaltuwa ne da Karatun Al-Kur’ani da karanta Salatul Fatihi da Tasbihi da Istigfari da Salatin Annabi (SAW) da sauran zikirori.

Shehin Malamin Yanada Jikoki da dama da kuma Yayan Jikokinsa wadanda dukkansu sun haddace Alkurani.

Da aka tambayeshi kan Mutane na mamakin dimbin ilimin da Allah Ya bai wa Malam ko akwai fannin da ya fi kwarewa? Sai yace “Na yi dukkan karatuna na addini a karkashin kulawar mahaifina, har na haddace Qur’ani, kuma ta hannunsa ne na karbi darikar Tijjaniya.

Shi mahaifina ya karbi darikar Tijjaniya ne ta hannun wani mutum mai suna Alhaji Gwani Abba,Daga baya sai mahaifina ya bani izinin na tafi duk inda nake so domin zurfafa ilimina na addini da haddar Qur’ani mai girma,bangaren da na fi kwarewa sosai shi ne Alkurani.

Daga nan kuma sai bangaren tafsiri, a nan malaman tafsiri sun ce lallai na iya tafsiri inji su. Sai kuma bangaren Maarifa, ma’anar Maarifa shi ne ilimin (gyaran) zuciya wanda ake kiransa ilimin tarbiyya, a nan ma masu irin ilimi kan ce ina da sani a fannin.

Shehu Ibrahim ya ce lallai na san wannan bangare. Sauran ilimomi ina tattabawa, su Hadisi da Lugga da Liirabi da Tasrifi da Fikihu duk ina tattabawa.

Da aka sake tambayarsa cewa Jama’a na mamaki idan aka yi wa Malam fatawa sai ya hada da ba da misali maimakon gundarin amsar, ko me ya sa Malam yake yin haka? Sai yace.

Wato shi buga misali wata runduna ce ta Allah mai shigar da ilimi cikin kawunan mutane, idan ka kawo amsar magana sai ka buga misalin da za ta hau kan mutane domin fahimtar da su. Shi buga misali yana jawo hankali a fahimci mene ne aka fada. Misali na da matukar muhimmaci wajen ba da amsa”.

Shehin malamin ya zama masanin tafsirin Alkur’ani mai girma wanda ya samu lambobin yabo a wannan ɓangaren, shine mutum Na farko a Nijeriya da ya fara yin Tafsirin Alkur’ani daka, ya kuma samu digirin girmamawa a bangarori daban-daban a Najeriya dama faɗin duniya baƙi ɗaya.

Babban jami’ar tarayya dake garin lafiya jihar Nassarawa sun bashi lambar yabo ta Digirin girmamawa, kana kuma Gwamnatin Tarayya ta bashi lambar Girmamawa da yabo na kasa ta OFR.

Kadan daga cikin irin nasarorin da Shehu Dahiru Usman Bauchi ya samu a tsawon shekaru sa.

Ya musuluntar da dubban mutane a wurin addinin musulunci a hannun sa. Ya kuma baiwa dubban Jama’a darikar Tijjaniyya. Shehi a duk lokaci bayan lokaci yana karanta Alkur’ani kuma sai yayi saukar Alkur’ani a kwana biyu.

Shehi ya bada lazumin Darikar Tijjaniyya ga dubban mutane da dama a fadin duniya.

Mutane fiye da 240,924 suka haddace Alqur’ani mai girma a makarantun sa dake fadin Najeriya. Shehun malamin ya kafa makarantun haddar Alqur’ani sama da 1700 a Nijeriya dama Afrika. Karkashin gidauniya sa an gina dakunan karatu guda 153,060 a Arewacin Najeriya.

Shehi mutum ne mai kishin kasarsa mai son Najeriya wanda aduk lokacin day a budi baki zaiyi addua ai ya rki Allah ya bamu lafiya da zama lagiya da kwanciyar hankali a Najeriya.

Wani bincike da wani wanda yayi nazari kan rayuwar Shehin kuma ya rubuta littafi akansa Mai Suna Shehu Dahiru Bauchi Ginin Allah Shekaru uku da suka wuce Farfesa Khalid Abdullahi Zaria, yace:

‘Ya’yan da Shehu ya haifa aduniya su 100; Mata 48, Maza 47, mahaddata Alkur’ani daga ciki, su 82. Daga cikinsu ya’yansa 21 sun rasu saura 79.

3. Jikokinsa, su 506; suka haifa, su 170. Yayi Shekatu 75 Yana Tafsirin Alqurani.

Yaje Aikin Hajji Fiye dasau 55, Yayi aikin Umrah fiye da 250.

Tsohon Shugaban Hukumar Sharia na Jihar Bauchi Mallam Ahmad Tijjani Said, yace rayuwar Shehi Gaba daya Makarantace , ta raya ilimi da kuma tarbiyyantar da alumma, saboda ayau araye shine cikin Malamai wanda zaka samu yayi tafiya daga Fataskum zuwa Filto a kafa don yada Addinin Musulunci.

Yayi tafiya daga Arewa har qasashen kudu a kan Jaki da doki don yada addinin musuluci, yayi tafiya a kan keke zuwa qauyuka da dama kamar Tafawa Balewa qasashen gidiri da arewa ta tsakiya da Arewa maso yamma don yada addinin Musulunci, haka lokacin da mota tazo Shehi bai huta ba har lokacin da Jirgin sama yazo duk da tsfansa yana yawon gwagwarmayan yada addinin musulunci da Darika

Yace baa bin Mamaki cikin Shaanin Shehi kamar Yadda daukan nauyi baya bashi tsoro baya damunsa , Yana da gidaje fiye da dubu daya afadin kasarnan amma ba inda ake haya bayin Allah masu neman ilimi yake zubawa a ciki kyauta.

Jamaar da yake ciyarwa Allah kadai yasan adadinsu, a kullum, in Shehi zai fito zai salami baqi fiye da dubu uku da sukazo Ziyararsa daga ciki da wajen Nijeriya, kuma zaka samu dalibansa Shehi ya musu auren fari ya musu suna kuma bai gaji ba ya maka mace ta biyu ya dauki nauyinku ire iren wadannan halaye na Shehi da wuya kasamu wanda zai iya yin haka.

Allah yaji kansa ya gafarta masa.

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2025/11/Tarihin-Sheikh-Tahir-Bauchi-_105948390.mp3

 

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Liverpool Tayi Rashin Nasara A Wasanni Tara
Next Post: Gobara Mafi Muni Cikin Shekaru 60 A Hong Kong Ta Hallaka Rayuka

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaba Tinubu Ya Ayyana Dokar-Ta-Baci A Fannin Tsaro Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Zelensky Na Buƙatar Ganawa Da Trump Domin Cimma Matsaya Kan Batutuwa Masu Sarƙaƙiya Labarai
Putin, Sakon Sabuwar Shekara Ya Jinjinawa Dakarun Rasha Da Suke Yaki A Ukraine Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Kwamitin Aikin Hajjin Najeriya Ya Shigar Da Korafi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Samar Da Tsaro A Jihar Kano Ba Sai An Sa Siyasa Ba! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Jami’ai Daga Amurka Sunce Yakin Amurka Da Iran Zaizo Karshe
  • An Gudanar da Taron Kwana Biyu kan Tsarin Sa Ido da Tantance Ayyukan AGILE a Jihar Gombe 
  • Rwanda Zata Janye Dakaru Daga Mozambique
  • Ruwan Sama Yayi Ajalin Mutane 70 A Nairobi
  • Shugaban Amurka Yayi Watsi Da Tattaunawar Kawo Karshen Yaki Da Iran

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Gwamna Abba Gida-Gida Na Dari-Darin Shiga APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Indonesia Zata Kafafa Rundunar Kiyaye Zaman Lafiya A Gaza Labarai
  • Sojoji Sunkai Farmaki Gidan Dan Adawa A Kasar Uganda Bobi Wine Afrika
  • Ana Cigaba Da Kai Kayan Agaji Kasar Morocco Sakamakon Tsananin Hunturu Afrika
  • Mutane Biyu Sun Rasa Rayukansu A Hatsarin Da Ya Rutsa Da Antothy Joshua Najeriya
  • Jam’iyar NNPP: Abba Kabir Yusuf Yaci Amanar Mu Siyasa
  • Chelle: Rashin Jituwa Tsakanin Osimhen Da Lookman Matsala Ce Ta Cikin Gida Wasanni
  • An Gurfaranar Da Wadanda Ake Zargi Takai Hari Gaban Kotu Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.