Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Hadakar Gwamnatin Najeriya Da Amurka Ne Suka Kai Hari Sokoto
Published: December 26, 2025 at 9:50 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin Najeriya ta sanar da nasarar kai hare-haren da aka tsara cikin tsanaki kan wasu manyan sansanonin ’yan ta’addan ISIS guda biyu da ke cikin dajin Bauni, a ƙaramar hukumar Tangaza ta Jihar Sokoto.

A cewar sanarwar da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta fitar, an gudanar da harin ne tare da haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Ƙasar Amurka, bayan bayanan sirri sun tabbatar da cewa ’yan ISIS daga yankin Sahel na amfani da wuraren a matsayin wajen taro da shiryawa domin kai manyan hare-haren ta’addanci a cikin ƙasar nan, tare da taimakon wasu ƙungiyoyin t’addanci na cikin gida.

Sanarwar ta ce an kai hare-haren ne tsakanin ƙarfe 12:12 na dare zuwa 1:30 na safiyar Juma’a, 26 ga Disamba, 2025, bayan samun cikakken amincewar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR.

An bayyana cewa an gudanar da aikin ne a karkashin tsayayyen tsarin umarni da jagoranci, tare da shigar Rundunar Sojin Najeriya, a ƙarƙashin kulawar Ministan Tsaro, Ministan Harkokin Waje, da Babban Hafsan Tsaro.

Hare-haren sun samo asali ne daga tashar jiragen ruwa da ke yankin Tekun Guinea, bayan dogon nazarin bayanan sirri, shirye-shiryen aiki da bincike na sama.

Jimillar harsasai masu bin tsarin GPS guda 16 ne aka yi amfani da su ta hanyar jiragen sama marasa matuƙa samfurin MQ-9 Reaper, lamarin da ya kai ga kawar da ’yan ISIS ɗin da ke ƙoƙarin shigowa Najeriya ta hanyar yankin Sahel.

Sai dai a yayin aikin, wasu ragowar harsasai sun faɗo a yankin Jabo da ke Ƙaramar Hukumar Tambuwal ta jihar Sokoto, da kuma a Offa ta Jihar Kwara, kusa da wani otel.

Gwamnati ta tabbatar da cewa babu wani farar hula da ya jikkata a wuraren, kuma jami’an tsaro sun gaggauta killace yankunan.

Gwamnatin Tarayya ta jaddada aniyarta ta ci gaba da kawar da duk wata barazanar ta’addanci, musamman daga ƙungiyoyin ta’addanci na ƙetare da ke ƙoƙarin tauye ikon Najeriya da tsaron al’ummarta.

Sanarwar ta ƙara da cewa Najeriya na ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da ƙawayenta na dabarun tsaro da abokan hulɗa domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa, tsaron iyakoki da kwanciyar hankali a yankin.

Gwamnati ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa tana da cikakken iko kan tsarin tsaron ƙasa, tare da ƙudirin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, sannan kuma an buƙaci al’umma da su kasance cikin kwanciyar hankali da taka-tsantsan yayin da ake ci gaba da ɗaukar matakan murƙushe duk wata ƙungiyar ta’addanci da ke barazana ga ƙasa.

Najeriya

Post navigation

Previous Post: Ankara Gano Wani Abu Mai Kama Da Abun Fashewa A Jabo Jihar Sokoto
Next Post: Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Hadakar Ta Da Amurka Wajen Yakar ‘Yan Ta’adda

Karin Labarai Masu Alaka

Tinubu Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwanin APC Da Kuri’u Miliyan 11 Afrika
Sanata Barau Ya Raba Motoci Da Babura Ga Al’ummar Kano Ta Arewa Afrika
Aminu Tambuwal Ya Fice Daga PDP Ya Koma ADC Afrika
An Kamallah Jigilar Alhazain Najeriya Domin Hajjin 2026 Afrika
Tinubu Na Kokarin Rage Tsadar Sufuri Ta Hanyar Shirin CNG Afrika
Gwamnatin Bola Tinubu Ta Raba Taraktoci Dubu Biyu Domin Inganta Noma Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Tinubu Ya Yi Allah Wadai Da Kashe-kashen Jos Da Kaduna Afrika
  • Kasar Malawi Ta Kaddamar Da Rigakafin Shan Inna Kiwon Lafiya
  • Arsenal Ta Doke Manchester City 3-0, Ta Ɗauki Kofin Community Shield Wasanni
  • Gwamnatin Tinubu Ta Karyata Kafa Kamfanin Gwal A Legas Labarai
  • Fanny Amun Ya Yi Murabus A Matsayin Shugaban Kwamitin Binciken NFF Wasanni
  • Akwai Bukatar APC Tayi Gyare-Gyare Kafun Zabe Afrika
  • Gwamnatin Kebbi Ta Samu Tankokin Yaki Tsaro
  • Dan Majalisar Wakilai Yaya Bauchi Tongo Ya Rasu A Abuja Bayan Doguwar Jinya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.