Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Gwamnatin Tarayya Tayi Baje Kolin Nasarorin Tinubu
Published: April 24, 2026 at 3:51 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana cewa Najeriya ta shiga wani sabon babi na gyara da ci gaba a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ta buƙaci kafofin yaɗa labarai na duniya da su riƙa rahoton gaskiyar abin da ke faruwa a ƙasar.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Alhaji Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wata tattaunawa ta musamman da wakilan gidajen jaridun ƙasashen waje a Abuja.

Ministan ya bayyana cewa a shekarar 2025, tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka da kashi 3.87 cikin ɗari, wanda hakan ke nuna cewa ci gaban tattalin arzikin ya fi ƙaruwar yawan jama’a sauri a karon farko cikin kusan shekara goma.

A cewarsa, cire tallafin man fetur da gyara tsarin musayar kuɗi sun taimaka kwarai wajen tara kuɗaɗen da ake amfani da su yanzu wajen samar da manyan ayyuka da inganta rayuwar al’umma.

Alhaji Mohammed Idris ya jero wasu daga cikin muhimman nasarorin da aka samu, waɗanda suka haɗa da:
• Samar da lamunin karatu ga ɗalibai ta hanyar asusun NELFUND.
• Inganta harkar tsaro ta hanyar amfani da bayanan sirri da leken asiri.
• Yunkurin kafa ’yan sandan jihohi domin bai wa hukumomin gida yancin cin gashin kansu.
• Zuba jari a fannin noma da fasahar zamani domin samar wa matasa ayyukan yi.

A nasa jawabin, Ministan Kuɗi da Tattalin Arziki, Mista Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa Nijeriya ta fita daga yanayin fargaba, yanzu tana matakin tabbatar da cewa al’umma sun fara jin daɗin waɗannan gyare-gyare a cikin rayuwarsu ta yau da kullum.

Haka ita ma Ministar Masana’antu da Kasuwanci, Dr. Jumoke Oduwole, ta jaddada cewa Nijeriya ba kawai tana binsu a bayan Afirka ba ne, tana kokarin zama jagora ne a fannin ciniki da masana’antu a faɗin nahiyar.

Minista Idris ya rufe jawabin nasa da kira ga ’yan jaridun duniya da su riƙa bayyana gaskiya game da Nijeriya.

Ya ce: “Muna son a riƙa bayyana nasarorinmu da kuma ƙalubalen da muke fuskanta duka tare, domin hakan ne kawai zai nuna ainihin hoton Nijeriya.”

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da Bayo Onanuga da Sunday Dare da kuma Abdulaziz Abdulaziz, waɗanda duka ke tallafa wa shugaban ƙasa a fannin yaɗa labarai da sadarwa.

Afrika, Labarai, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Peter Obi Ya Gayyaci Gwamnan Bauchi Bala Abdulkadir Kan Yazo Su Hada Kai Su Gyara Nijeriya.
Next Post: Al’ummar Jihar Nasarawa Suna Cecekuce Bisa Tsaida Aliyu Wadada Takarar Gwamna

Karin Labarai Masu Alaka

Hukumar Kare Hakkin ‘Yan Jarida Tace Isra’ila Ce Ta Kashe ‘Yan Jarida Kashi Biyu Bisa Uku Labarai
Fiye Da Mutane 108 Sun Rasa Rayukansu A Ambaliyar Kenya Afrika
Mamakon Ruwan Sama Da Iska Ya Hallaka Mutane Uku A Jihar Yobe Labarai
Yanbindiga sun Kashe mutun guda tare da yin garkuwa da mutane kimanin 100 a Jihar Nejan Najeriya. Najeriya
An Gudanar Da Jana’izar ’Yan Jaridan Da Suka Rasu A Jihar Gombe Labarai
Cutar Kurkunu Ta Kusa Zamowa Tarihi A Duniya Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Kano Zata Dauki Mataki Game Da Kisan Dorayi Tsaro
  • Sojojin Isra’ila Sun Kashe Babban Kwamandan Kungiyar Hezbollah Afrika
  • Wani Jirgin Sama Ya Karya Dokar Hana Zirga Zirga Amurka
  • Tsofin Ma’aikatan Gwamnati Sunyi Zanga Zanga A Jihar Neja Labarai
  • Kudaden Shigan Kasar Namibia Ya Bunkasa Saboda Tashin Farashin Gwal Labarai
  • Majalisa Ta Tabbatar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan Kano Afrika
  • Gwamnatin Amurka Na Kokarin Watsi Da Tsohuwar Dokar Jones Labarai
  • Za’a Dauko Messi Aro Zuwa Barcelona Deco Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.