Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

An Bukaci Matasa Su Taka Gagarumar Rawa Wajen Gina Zaman Lafiya A Arewa Maso Gabas
Published: June 30, 2026 at 6:25 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Masu ruwa da tsaki daga sassan yankin Arewa Maso Gabas sun yi kira da a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da kuma aiwatar da shirye-shiryen zaman lafiya da suka haɗa kowa da kowa domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa a yankin.

An yi wannan kira ne a yayin taron kwana biyu na North-East Peace Mission Conference da Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC) ta shirya a jihar Gombe.

Da yake jawabi a taron, Manajan Daraktan NEDC, Mohammed Alkali, ya bayyana cewa zaman lafiya mai ɗorewa shi ne ginshiƙin sake farfaɗo da yankin da kuma samar da ci gaba mai anfani ga al’umma.

Alkali, wanda Kodinetan NEDC na Jihar Gombe, Arc. Usman Muhammad, ya wakilta, ya ce an shirya taron ne domin ƙarfafa tattaunawa, bunƙasa haɗin kan al’umma da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati, ƙungiyoyin ci gaba, shugabannin al’umma da matasa.

Ya ce hukumar na ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen gina zaman lafiya a faɗin yankin Arewa Maso Gabas, inda ya bayyana cewa ayyukan da suka shafi gine-ginen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, samar da hanyoyin dogaro da kai da sake tsugunar da waɗanda rikice-rikice suka raba da muhallansu na taimakawa wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A cewarsa, NEDC ta samu gagarumar nasara wajen sake gina al’ummomin da matsalar ta’addanci ta daidaita, ta hanyar samar da muhimman ababen more rayuwa, tallafa wa marasa galihu da kuma farfaɗo da harkokin tattalin arziki domin inganta rayuwar jama’a.

Yayin da yake gabatar da muƙala kan rawar da matasa za su taka wajen gina zaman lafiya, Mataimakin Farfesa a fannin Tarihin Soja da Nazarin Tsaro na Jami’ar Maiduguri, Dakta Abubakar Muhammad, ya jaddada muhimmancin bai wa matasa dama da goyon baya domin su kasance sahun gaba wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Ya buƙaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su ƙara zuba jari a ilimi, koyar da sana’o’i da kuma ƙarfafa matasa su shiga harkokin ci gaban al’umma. Haka kuma ya yi kira ga al’umma da su rungumi tare da tallafa wa sake haɗa tsoffin mayaƙan da suka ajiye makamai cikin jama’a a matsayin wani ɓangare na sulhu da farfaɗo da yankin.

Ɗaya daga cikin mahalarta taron, Yasin Idris, ya ce taron ya ba matasa damar bayyana ra’ayoyinsu tare da bayar da gudunmawa wajen samar da mafita ga matsalolin da ke addabar yankin.

Ya yi kira da a ƙara bai wa matasa dama su shiga ayyukan gina zaman lafiya ta hanyar shirye-shiryen wayar da kai, tattaunawa da ayyukan raya al’umma, yana mai nuna kwarin gwiwar cewa haɗin kai da shigar kowa da kowa za su taimaka wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa da ci gaba mai anfani a Arewa Maso Gabas.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: NSCIA Ta Gargadi Gwamnati Kan Zargin Tauye Haƙƙin Musulmi
Next Post: APC Ta Sauya Jerin ‘Yan Takararta Bayan Nazarin Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Fidda Gwani

Karin Labarai Masu Alaka

Tsohuwar Jarumar Kannywood Wasila Ismail Ta Rasu Afrika
Anfara Samun Sakamakon Wucin Gadi a Kasar Guinea Conakry Labarai
Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Ya Zamo Khalifan Sheikh Dahiru Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi Afrika
Ukraine Ta Bayyana Goyon Bayanta Ga Tsarin Cimma Yarjejeniya Sauran Duniya
Mace Ta Farko Da Zata Shugabanci Jami’ar Northwest Dake Kano Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Jirgin Ruwa Ya Kife A Yammacin Kasar Gambiya Labarai
  • Shugaba Bola Tinubu Ya Tafi Turai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Zata Bawa Ukraine Tsaro Na Musamman Amurka
  • ‘Yan Bindiga Sun Jikkata Mutane A Arewacin Kasar Benin Afrika
  • Kakakin Majalisar Kasar Amurka Yana Tsaka Mai Wuya Game Da Kasafin Kudi Amurka
  • Amurka Na Gargadin Rwanda Da Ta Mutunta Alkawali Afrika
  • Cutar Kurkunu Ta Kusa Zamowa Tarihi A Duniya Amurka
  • Kasar Aljeriya Ta Soke Yarjejeniyar Jirgin Sama Tsakaninta Da Daular Larabawa Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.