Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

NAHCON Ta Kaddamar da Tawagar Malamai
Published: April 26, 2026 at 2:17 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Ambasada Ismail Yusuf Abba, ya sake jaddada aniyar hukumar na zurfafa fadakarwa da horar da maniyyata ta fuskar addini domin tunkarar aikin hajjin shekarar 2026.

​Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 22 ga watan Afrilun 2026, yayin taron kaddamar da Tawagar Malamai (Ulama Team) na aikin hajjin bana, wanda aka gudanar a dakin taro na gidan hajji da ke Abuja.

​Taron ya samu halartar manyan malaman Musulunci guda 120 da aka zabo daga sassan kasar nan, wadanda suka hada da Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto, Sheikh Bala Lau, Sheikh Abdulmuhyi Nasir (wanda ya wakilci Sheikh Sani Yahaya Jingir), Sheikh Abdulrahman Olanrewaju Ahmed, Sheikh Nasir Adam, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, Sheikh Usman Usman Dahiru Bauchi, da Dr. Isa Akindele Solahuddeen, da dai sauran manyan malamai.

​Babban makasudin taron shi ne tattauna yadda za a mayar da hankali wajen ilimantar da maniyyata da ba su horo na musamman.

Ambasada Abba ya dorawa malaman nauyin taimakawa hukumar wajen gudanar da darusan fadakarwa cikin harsuna daban-daban kafin tafiya da kuma lokacin gudanar da ayyukan hajji a kasa mai tsarki.

​Ya jaddada cewa malaman su tabbatar sun koya wa maniyyata sahihan rukunai da sharuddan aikin hajji dalla-dalla, domin su sauke farali yadda ya kamata.

Haka zalika, ya bukaci malaman da su kasance a shirye wajen ba da amsoshi ga tambayoyin alhazai, musamman idan suka fuskanci kalubalen da ka iya shafar ingancin aikin hajjinsu.

​Baya ga ilimantarwa, tawagar malaman za ta shirya addu’o’i na musamman a wurare masu tsarki, musamman a filin Arfa, domin rokar wa Najeriya da shugabanninta zaman lafiya, hadin kai, tsaro, da bunkasar tattalin arziki.

​A nasa bangaren, Farfesa Bashir Umar ya bukaci malaman da su ja hankalin alhazai su yi addu’ar samun nasarar babban zaben shekarar 2027 da ke tafe, ganin cewa aikin hajjin na bana zai gudana ne a daidai lokacin da kasar ke shirin fuskantar zaben.

​Daga karshe, malaman sun jaddada muhimmancin shirya zukatan maniyyata ta fuskar hakuri, ikhlasi, da kuma sadaukar da kai ga Allah, inda suka bayyana shirinsu na ganin ‘yan Najeriya sun samu gamsasshen aikin hajji karbabbe.

Afrika, Labarai, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Ga Fili Ga Doki Dambarwar APC Da ADC
Next Post: Kungiyoyin Fararen Hula A Gombe Sun Bukaci A Bawa Mata Jagoranci

Karin Labarai Masu Alaka

Amurka Zata Kamallah Yaki Da Iran A Makonni Biyu Masu Zuwa Amurka
Amurka Na Gargadin Rwanda Da Ta Mutunta Alkawali Afrika
An Kama Tsohon Jakadan Birtaniya A Amurka Peter Mandelson Amurka
Jamhuriyar Congo Zata Cigaba Da Fitar Da Ma’adanai Afrika
An Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman Don Neman Zaman Lafiya Labarai
Zamu Hada Kai Mu Yaki Cutar Shan’inna (Polio) Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Borno Tsaro
  • Gwamnan Jihar Filato Na Shirin Komawa APC Siyasa
  • Jama’ar Kasar Iran Sun Bayyana Goyon Baya Ga Ayatollah Mojtaba Khameni Afrika
  • Shugaban Ƙasar Koriya Ta Arewa Ya Halarci Gwajin Makami Mai Linzamin Kasar Labarai
  • Kasar India Ta Sayi Iskar Gas Daga Iran Labarai
  • Samar Da Albarkatun Mai Ya Ragu A Iraq Afrika
  • Afirka Ta Kudu Ta Bayyana Yadda Aka Yaudari ‘Yan Kasar Ake Tilasta Musu Ayyukan Bauta Afrika
  • Mutane Da Yawa Ke Mutuwa A Dalilin Shan Magani Ba Bisa Ka’ida Ba Kiwon Lafiya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.