Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Cin Karensu Babu Babbaka A Najeriya
Published: March 19, 2026 at 4:15 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Akalla mutane 18 ne aka kashe a ranar Talata a jihar Katsina, hukumomi da ‘yan sanda suka bayyana hakan, wannan harin shi ne na biyu bayan cimma wata yarjejeniya da aka yi da ‘yan ta’adda.

Jihohin Katsina da makwabta sun bi yarjejeniyoyin yin afuwa da yarjejeniyar tsaro da al’umma don shawo kan matsalar gungun ‘yan bindiga. amma har yanzu kauyukan na fuskantar hare-hare na kai-tsaye, ramuwar gayya da tashe-tashen hankula.

Hare-haren na baya-bayan nan ya fara ne lokacin da ‘yan banga suka kashe wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a kauyen Falale, lamarin da ya haifar da ramuwar gayya daga wasu ‘yan bindiga da suka kashe mutane 15 a Falale da kuma makwabtan Kadobe, in ji kwamishinan tsaro na jihar Katsina, Nasir Mua’zu.

Kakakin ‘yan sandan Katsina Abubakar Aliyu ya kuma yace harin ramuwar gayya ya yi sanadin mutuwar mutane 15.

Yayin da ake samun kananan hare-hare a makonnin da suka gabata, adadin wadanda suka mutu a harin na ranar Talata shi ne mafi girma tun ranar 3 ga watan Fabrairu, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kashe akalla mutane 21 a garin Doma da ke jihar Katsina, lamarin da ya haifar da tsagaita bude wuta na tsawon watanni shida.

Afrika, Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: An Kai Hari Babbar Tashar Iskar Gas A Iran
Next Post: Matsayar Iran Na Kera Makamin Nuclear Bazai Sanja Ba

Karin Labarai Masu Alaka

Anyi Rashin ‘Yan Jarida 6 A Jihar Gombe Sakamakon Hatsarin Mota Labarai
China Ta Dawo Da Harajin Magungunan Hana Haihuwa Labarai
Masarautar Borgu a Jihar Neja na neman daukin Gwamnatin Najeriya akan matsalar rashin tsaro Najeriya
Gwamnatin Sokoto Tabada Umarnin Biyan Albashin Watan Fabrairu Labarai
Afirka Ta Kudu Ta Kubutar Da ‘Yan Kasar Da Suke Taya Sojojin Rasha Yaki Afrika
Hukumar Tsaro Ta DSS Ta Aika Sammaci Dr. Yusuf Baba-Ahmed Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Majalisar Dattawa Ta Amince Tinubu Ya Tura Sojoji Benin Labarai
  • Gobara Ta Tashi A Hukumar FIRS Dake Abuja Najeriya
  • Alkalan Wasannin Kwallon Kafa A Ghana Zasu Samu Inshora Wasanni
  • Ruwa Kamar Da Bakin Kwarya Ya Haifar Da Mutuwar Mutane A Nairobi Afrika
  • Samar Da Tsaro A Jihar Kano Ba Sai An Sa Siyasa Ba! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Dakarun Sakai A Kasar Sudan Sun Kashe Mutane 28 A Wani Farmaki Afrika
  • Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Aikin Wutan Lantarki A Jami’ar Bayero Afrika
  • Ambaliyar Ruwa Yayi Ajalin Mutane A Nairobi Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.