Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Shugabannin Kasashen Afirka Ta Tsakiya Sun Kamallah Taron Koli
Published: January 23, 2026 at 1:33 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugabannin kasashe dake Afirka ta tsakiya sun kammala taron koli da suka yi tare da bada umarnin a dauki matakai cikin gaggawa domin kawo daidaito ga al’amuran kudi da tattalin arziki na kasashen, domin karfafa su ganin koma baya na tattalin arzikin su, da suka hada da dawo da kudaden kasashen da suke ketare.

Shugabannin kasashen shida, sun amince da adawo da kudaden kasashen da suka samu ta fuskar albarkatun kasa, kamar yadda jawabin bayan taro na musamman da suka yi a birnin Brazaville ya nuna.

Taron kolin wadda aka gudanar karkashin laimar kungiyar raya tattalin arzikin kasashe dake Afirka ta tsakiya, an yi zaman na gaggawa domin tunkarar tafiyar hawainiyar tattalin arzikin yankin, faduwar farashin albarkatun kasa, matsalolin sakewar yanayi, da kuma tsuke bakin aljihu daga hukumomin duniya.

A bara babban bankin kasashe dake yankin Afirka ta tsakkiya, da suka hada da manyan bankunan kasashen Kamaru, da Chadi, da kasar Afirka ta tsakiya,da Gabon, da Kwango, da Equatorial Guinea, sun bukaci kamfanonin hakar mai a yankunan su adana kudaden farfado da muhalli da aka tanadar karkashi asusun babban bankin kasashen da asusun bada lamuni na duniya watau IMF a takaice, yake bada goyon baya, mataki da kamfanonin hakar man basu ji dadi ko amince dashi ba.

Kudaden wadanda kamfanonin mai din suka tanadar domin ayyukan tsabtacewa da farfado da muhalli idan aka gama hakar mai sun kai dala bilyan biyar zuwa 10.

Haka nan shugabannin sun bada umarnin hukumomin kasashen su kammala shirye shirye da yarjejeniya gamda kasafin kudi da tattalin arziki da asusun bada lamuni na duniya IMF.

Afrika

Post navigation

Previous Post: Tinubu Ya Rantsar Da Shugabar Hukumar FCC
Next Post: Shugaban Mulkin Soja A Mali Ya Kirkiro Mukami Kamar Minista

Karin Labarai Masu Alaka

Shugabannin Sojojin Najeriya sun Kai Ziyarar Aiki Maiduguri  Afrika
Yayale Ahmed Ya Jagoranci Kwamitin Amintattu Na Asusun Tsaron Arewa Afrika
RSF Ta Kasar Sudan, Tana Yin Garkuwa Da Mazauna A Yankin Darfur Afrika
Muna Kira Ga Kasashen Duniya Su Sa Baki Don A Saki Mohamed Bazoum Afrika
Hawan Babbar Sallah A Masarautar Kaltungo Dake Jihar Gombe Afrika
JEI Da Abokan Hulɗar Sun Gudanar Da Aikin Shuka Itatuwa Domin Bikin Ranar Muhalli Ta Duniya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasar Belarus Zata Taffawa Jamhuriyar Nijar Afrika
  • Masarautar Borgu a Jihar Neja na neman daukin Gwamnatin Najeriya akan matsalar rashin tsaro Najeriya
  • Shugaba Putin Ya Bukaci Kawo Karshen Yaki Da Iran Afrika
  • An Bude Gasar Kwallon Kafa Ta Mata A Najeriya NWFL 2025 Wasanni
  • Gwamnan Jihar Kano Ya Fice Daga Jam’iyar NNPP Siyasa
  • Shugaban Amurka Ya Ya Bukaci Iran Ta Mika Wuya Afrika
  • Shugaba Tinubu Ya Ayyana Dokar-Ta-Baci A Fannin Tsaro Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.