Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Shugaban Miyetti Allah Zai Fuskanci Shari’a Kan Zargin Badakalar Kuɗi da Ta’addanci
Published: June 24, 2026 at 8:05 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC) ta shigar da ƙara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo, bisa zargin badakalar kuɗi da kuma tallafa wa ayyukan ta’addanci.

Rahotanni sun nuna cewa hukumar ta gabatar da tuhume-tuhume guda 12 a kansa, inda ake zarginsa da hannu a wasu mu’amalolin kuɗi da suka kai kimanin dala miliyan 2.53 na Amurka da ake zargin sun samo asali ne daga haramtattun ayyuka.

A cewar takardun tuhumar da aka gabatar wa kotu, EFCC ta ce Bodejo ya karɓi kuɗaɗe daga tsohon Akanta Janar na Jihar Bauchi, Sa’idu Abubakar, ba tare da amfani da hanyoyin banki da dokokin Najeriya suka tanada ba.

Daga cikin zarge-zargen da ake yi masa, akwai karɓar dala 100,000 a watan Janairun 2022 da kuma dala 200,000 daga wani mutum a wani lokaci daban. Haka kuma, ana zarginsa da karɓar dala 980,000 a watan Fabrairun 2024 da kuma dala 500,000 a watan Maris na shekarar 2024, duk a tsabar kuɗi.

Hukumar EFCC ta kuma yi zargin cewa Bodejo ya mallaki wasu kuɗaɗe da ake kyautata zaton sun samo asali ne daga ayyukan da suka saɓa wa doka, lamarin da ya sa aka shigar da ƙarar a kansa.

Ana sa ran kotun za ta sanya ranar fara sauraron shari’ar nan ba da jimawa ba.

Bello Bodejo dai na ci gaba da cin gajiyar haƙƙinsa na kasancewa marar laifi har sai an tabbatar da zarge-zargen da ake yi masa a gaban kotu.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: NAHCON Ta Yaba da Nasarar Hajjin 2026, Ta Fara Shirin Hajjin Shekara Mai Zuwa
Next Post: Hukumar NDLEA Ta Lalata Gonakin Wiwi A Ekiti

Karin Labarai Masu Alaka

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Shugaban Makaman Nukiliya Afrika
Papa Roma Leo Yace Zai Cigaba Da Sukan Yake Yake Afrika
Gwamnatin Sham Tace Harin Kurdawa Ya Hallaka Sojojin Kasar Afrika
Harin Jirgi Maras Matuki Ya Hallaka Mutane A Sudan Labarai
Gwamnatin Kano: Zamu Kara Daukar Malamai Domin Inganta Ilimi Najeriya
Jami’an Tsaro Na Amfani Da Damar Su Wajen Cin Zarafin Jama’a Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kaduna: Masana Sun Nemi A Sauya Tsohon Wurin Zubar Da Shara Na Tudun-Ilu Afrika
  • Chelsea Tayi Kaca-Kaca Da Barcelona A Gasar UCL Wasanni
  • Harin Bom Din Maiduguri Ya Kashe Mutane Biyar Ya Raunata Fiye Da Talatin Najeriya
  • Baitul Malin Amurka Zata Bawa Venezuela Da Cuba Damar Sayar Da Mai Amurka
  • Za’a Jima Ana Fama Da Tsadar Farashin Mai Afrika
  • Akwai Yiwuwar Iran Da Amurka Su Cimma Matsayar Dakatar Da Shirin Nukiliya Amurka
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Kasar Gabon Ta Nemi Tallafin Asusun Bada Lamuni Na IMF Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.