Irin hanyoyin da zanbi in cika burin ci gaba da kyautata rayuwar Al’ummar Jihar Bauchi – Yakubu Adamu
Daga Ahmed Mohammed, Bauchi
Dokta Yakubu Adamu,tsohon kwamishinan kudin Jihar Bauchi,gogaggen ma’aikacin bankine, gashi matashi, shine Dan Takarar Gwamnan Jihar Bauchi a Jam’iyyar APM Mai alamar rogo,cikin zantawarsa da Yan Jarida ya bayyana aniyarsa ci gaba da ayyukan Alheri da ciyar da jihar a gaba.
Lokacin da aka baka wannan takara me ya fara zuwa Maka a ranka, kuma yaya kaji?
To Alhamdu lillahi muna godiya wa Allah daya bamu wannan dama , a gaskiya lokacin da aka zabeni aka bani wannan takara abuna farko daya fara zuwa min raina gaskiyar Magana shine godiya wa Allah ne ,saboda Allah madaukakin Sarki shi yake komai cikin ikonsa da rahamar sa., shi yake bada mulki wa wanda yaga dama ya kuma hana wanda yaga dama,
Abu na biyu gaskiya nayi farin cikin matuka, saboda bani da wani burin daya wuce inci gaba da aikin da baban mu Mai gidan mu , mai girma Gwamnan Jihar Bauchi , Sanata Bala Mohammed Kauran Bauchi, irin ayyukan daya shimfida a Jihar Bauchi, bani da burin da ya wuce da yaya za’ayi bayan wa’dinsa ya wuce a ci gaba da yin irin wadannan ayyukan. To wadannan abubuwa guda biyu sune sukazo min raina, nace ikon Allah Kenan yanda nake da damuwa a raina ga Allah Yana da nufin ya cika min wannan burina don ni nazo na ci gaba da wadannan ayyukan alheri a bangarori dabam dabam ,muna godiya wa Allah.
A bayan an san Jihar Bauchi tana da masana’antu sosai, amma a yau duk sun durkushe, kusan Jihar Bauchi tafi dogara da samun kudaden shigan ta daga Gwamnatin tarayya, In Allah ya baka mulkin Jihar Bauchi wani tsari zaka bi wajen ganin Jihar ta dogara da samun kudaden shiga daga masana’antu da ke Jihar?
Alhamdulillahi Wannan tambaya ya shafi bangarena dana fito tunda na shekara akalla goma sha biyar zuwa goma sha shida a banki , kuma na shekara uku a Gwamnati to a gaskiya tun zuwan wannan Gwamnati mai ci a Shekarar 2019 Mai girma Gwamnan Jihar Bauchi Babanmu kuma Jagoranmu yazo ya Sami batun kudaden Shigan Jihar Bauchi a cikin wani mawuyacin Hali, abinda ake Samu a gaskiya bai Kai ma miliyan dari uku ₦300,000,000 ba, in anyi kokari ne sai a Sami miliyan dari ukun. Amma a yanzu dana ke Maka magana, saboda hikima sanin aiki ,DA gogewa irin na Mai girma Gwamnan da yaga girman matsalar sai ya kawo masana gogagu kuma kwararrun ma’aikata da suka San wannan fannin ,suka yi jan aiki akai, abin farin ciki a yau abin ya canja ana kawo Naira biliyan biyu da rabi ₦2,500,000,000 zuwa biliyan uku ₦3,000,000,000 kowani wata, mu kuma idan munzo tunda muna tare, Gwamnati ne na ci gaba Gwamnati ne kuma wanda damu akayi , burinmu shine muga yaya zamuyi mu maida wannan biliyan uku ya koma biliyan biyar ₦5,000,000,000 ko biliyan shida ₦6,000,000,000, Yadda zamuyi kuma abu ne da yake da sauki, saboda akwai bangarori da yawa wadanda har yanzu muna kokarine mu cika wadansu ka’idoji domin mu rika samun kudaden shiga daga wadannan bangarori misali bangaren dandalin yada labarai ta yanar gizo wato bangaren (Social Media) dukkansu daga yawan mutanen da suke amfani da wannan bangaren na yanar gizo a wannan Jihar, saboda yawan mu da yawan amfani da muke yi dashi ya kamata arika bamu wani abu na kudaden shiga daga wannan bangaren Amma mu a Jihar Bauchi ba’a taba bamu ko sisin kwabo ba, kama daga masu amfani da shafukan “You tube, ya kai Instagram, har face book da sauransu”. Muna so muga munyi kokari mun ga ana biyanmu wannan kudin zai Kara mana kudin shiga, haka kuma akwai wassu bangarori kuma da shima ba’a karban kudaden shiga misali bangaren kudaden hakar ma’adinai, dana yin rijistan filaye dana harkan wassu kaddarori da mutane suke mallaka a Jihar duka wadannan bangarori ne da a gaskiya ba muyi nisa a cikinsu wajen karban haraji ba. Muna sa ran a watanni masu zuwa Ko daga nan zuwa shekara daya gaskiya za’a Sami karin kudaden shiga a wannan bangaren. Shi kuma ta wajen batun kamfanoni kuwa , gaskiyar Magana shine mai kamfani ba zai zo Jihar ka ba sai Ka Sama masa dama da zai Sami saukin kasuwan cinsa, misali batun haraji , yaya zaka sawwaka masa biyan haraji, yaya zaka sama masa saukin yanayin da zai gudanar da kasuwan cinsa,yaya zakayi jadawalin Yadda za’a sami saukin dokoki daga Majalisar dokokin Jihar domin su sami saukin dokokin gudanar da kasuwan cinsu , yaya zaka yi Ka inganta maganan tsaro domin in sun zo hankalinsu ya kwanta. duk wadannan abubuwa mai girma Gwamnan Bauchi yayi kokarin Samar da da yawa daga cikin har ya kaimu ga Yadda ya Kira wani gagarumin taro na zuba jari na duniya, in da duk muka zo mu Ka taru gabaki dayan mu, mutane da dama sunvzo suka yi kokarin zuba jari har ya Kai zasu sa hannayen jari da ya Kai dalar Amurka biliyan shida, kaga inda baiyi wannan taro na zuba jari ba da masu zuba jari daga cikin Nijeriya da kasashen waje ba zasu zo bama ballantana suga irin albarkatun da muke dasu ,suga irin tsare tsaren da gwamnati, tayi domin su sa hannayen jarinsu. to irin wannan shine zamu ci gaba dayi domin mu sami wadanda zasu sa hannayen jarinsu domin mu farfado da kamfanonin mu na Jihar mu kakkafa wassu sababbi domin mu samawa mutanen mu ayyuka Masu nagarta Kuma mu Kara bunkasa tattalin arzikin jihar.
Yaya Zakayi da dimbin matsalolin dake damun Mata da matasa kasance war kaima matashi ne ?
Alhamdulillahi naji dadin wannan tambaya , saboda matasa a Bauchi da Mata mutane ne Masu hazaka , mutane ne Masu kokari kwarai da gaske, a gaskiya Ko a yanzu in ka tashi ka shiga cikin gari zaka ga matasan mu da Maza da Mata Suna kokarin yin sana’o’i Iri iri kama daga masu aikin faci, Masu aikin gini ,masu Sana’ar tuki, Ko Kafinta Ko walda Ko kira Wassu Mata kuma Zaka Suna tuya kona kosai, Ko awara, Ko Sai da goro ko wassu sana’o’i dabam dabam, matasan mu da mata Suna kokari wajen gujewa zaman banza, mu Idan munzo ba wani abu zamu yi shi sabo ba,zamuyi kokari mu duba muga yadda zamu inganta musu sana’arsu da suke yi, na biyu Kuma zamu duba Wani abu da ake Kiransa wato hanyoyin taimakawa masu kananan Jari, gaskiyan Magana a yau in kun lura da wadanda suka yi fice a kasashen Afrika mutum biyar gaba daya ta fannin kasuwanci na Zamani da ake Ji dasu a kasashen Afirka zaka ga sun fito ne daga Nijeriya, Kuma a Nijeriya ma daga Jihar Legas suka fito, abin tambaya anan shine me yasa suka fito daga Jihar Legas kadai? dalili shine saboda Jihar Legas ta bada dama wa mutanen da suke da kamfanoni irin na zamani suka yi fice da suke da jarin a kalla Naira biliyan 140,000,000,000. Kuma irin wadannan kamfanonin basu Jima ba, Kuma gwamnati ne ta taimake su, ta basu dama suka zo suka baza Hajar su a nan Jihar Legas din, kafin kace wani abu Sai gashi sunyi fice a cikin kasashen Afirka, in Allah ya bamu nasara zamu duba Irin wannan hanya saboda Kishi, kunga kamfanonin nan ba bu Ko guda daya a Arewa, zamu duba Muga ta Yaya za’a sami wani Ko wassu daga Jihar Bauchi Suma suyi fice haka, in sha Allahu mu taimaka musu.
Zamu taimaka wa matasa sosai saboda na Lura abinda yasa ake samun koma baya a wassu gwamnatoci shine raina matasan akeyi, Zaka Samu matashi ya na da tsari Mai kyau na kasuwa, Yana bukata a taimaka masa a bashi dama,Ko a bashi fiii, ko a bashi dan karamin kudi,ko yana nema a tsaya masa ta yadda zai rika Karbo Kaya daga kasar Amurka, Ko Ingila Ko kasar sin Ko India, amma Sai kaga wassu gwamnatoci suna raina shi , gwamnatin taki yi masa Komi.
Mu in Allah yasa aka zabe mu, zamu zo da tsarin da zai taimakawa matasa, da Mata ,Kuma Alhamdulillahi Mai Girma Gwamna shekara Daya daya wuce, ya shiga ‘yarjejeniya da kasar Kanada, don koyawa Matasa ilmomin fasaha da Dogaro da kai, ya yadda zasu Iya samun ayyukan da zasu iyayi a duk fadin duniya, Alhamdulillahi har an yaye kashi na farko, za’a shiga kashi na biyu, Irin wannan ne muke so in Allah ya bamu nasara in muka zo mu kara habaka su,ta yadda za’a dauki matasan mu aiki a ko’ina.
Bangaren mata kuwa ba abinda suke so sai abinda zai sawwaka musu sana’oinsu, Misali zamu Yi kokari a Sama musu firij Mai aiki DA hasken rana,ta yadda Yan’uwan mu Fulani in sun yi tallen nononsu basu sayar ba, zasu Iya ajiye shi a cikin firijin Ko man Shanu, Idan sun tara basu kai talle ba saboda ruwa Ko Kogi ya kawo duka zasu ajiye shi cikin firijin domin su sami sauki Kuma ba Zai lalace ba. Irin wannan firiji Zai yi amfani a birni da kauye, ta wannan hanya zamu bunkasa dukkan sana’oin da akeyi da suke bukatar na’urar Sanyi domin.a Sami nasara.misali Yan’Uwan mu Mahauta ma zamu Samar musu da manyan wuraren da zasu rika ajiye nama don karya lalace saboda lafiya na da lafiyarku da lafiyan al’ummar Jihar Bauchi. Kaga in mahauci ya sayo nama kilo goma ya sayar da kilo bakwai saura uku to ga wurin da zai kai ajiya, za’a yi wurin ne na gwamnati yadda zai Iya biya da kudi kadan ,don asamu yadda za’a biya Masu lura da wurin ajiyan kuma za’ayi aikinne da kungiyoyin Mahautan , haka ma sauran sana’o’i kowacce zamu duba yadda zamu ingantata a Zama nan ce.
Haka zamu Yi wadannan tsare tsaren don mu sawwaka wa Jama’a , kaga kudin wuta yayi yawa, kudin ruwa yayi yawa, kai kudin Komi ma yayi yawa, hatta bangaren sufuri Zamu Samar da ababen hawa masu amfani da hasken rana ta yadda zai zama Idan mutane Suna biyan Naira dari biyar ne zuwa Tirwun Ko Wuntin dada, Ko railway Daga Wunti Idan muka Kawo Mota Mai amfani da hasken rana da mashin Mai amfani da hasken rana Ko Keke NAPEP Mai amfani da hasken rana, kaga burinmu su biya Naira dari Ko kasa da haka.
Bangaren Ma’aikata fa,an San Jihar Bauchi Jiha ce ta Ma’aikata Idan kasami Mulki Wani tsari za kayi,? kama daga daukan aiki, biyan albashi, ga kuma tulin kudin fansho da kudin sallamar aiki da Ma’aikata ke bi bashi, Yaya Zaka yi?
Alhamdulillahi Ma’aikata sune Kashin bayan kowace gwamnati, da gwamnatocin da Suka shude da wadanda suke ci da kuma masu zuwa, Ma’aikata sune suke rike gwamnatin ta hanyar ayyukan raya kasa da kyautata rayuwar al’umma,
Mu a tsarinmu bamu dauki ma’aikaci da wasa ba Ko mace Ko namiji Muna daukar su da muhimmanci,
Kuma a Yau a Jihar Bauchi Mai Girma Gwamna Yana Biyan Mafi karancin Albashi na ₦70,000 Kuma ya kawo tsare tsaren biyan Albashi da duk abinda ya kamata wa Ma’aikata a Fannonin kula da lafiya, da Fannin aikin gona da sauransu, Misali likitan da yake aiki a jihar Bauchi albashinsa dai dai yake da Wanda yake aiki a Gwamnatin Tarayya, Kuma duk ana biyan su, to mu Idan Allah yasa muka Kafa gwamnati zamu kyautata wa Ma’aikata ta hanyar lura da kwazonsu, don kwazonsu ba Iri daya bane, zamu lura da kwazon sune ta hanyar amfani da fasahar zamani da Kuma amfani da Jama’a da ma’aikatunsu da Kuma ofishin Shugaban Ma’aikata, ba zai Yiwu Misali muce dan siyasa ne kawai zamu baiwa Mota ba, A’a Ma’aikata ma zamu lura da kwazonsu mu basu motoci, Misali ace Wanda yafi kwazo mu bashi gida Wanda yayi na biyu mu bashi Mota na uku mu bashi kujeran Hajji , na hudu mashin na biyar mu bashi kudi, haka dai zamu lura da aikin kowani ma’aikaci mu rika Saka masa gwagwadon iko. badon Komi ba Sai saboda wannan ne yasa nayi fice a duk bankunan da nayi aiki, kaga nayi aiki a
bankin FCMB ,nayi aiki a bankin Skye Na Kuma Yi Aiki a bankin Polaris a duk lokacin da aka duba kwazon ma’aikaci aka bashi lambar yabo Ko aka saka masa Wani lokaci in aka bashi kudi Sai kaga kudin yafi albashinsa, Ko a kai ku wassu kasashen, Ko abaka labar yabo, Wani lambar yabo in aka baka kowace Shekara ma sai ka samu karin girma , shine nake so muma in Allah ya bamu dama mu aiwatar wa Ma’aikatanmu, masu kwazo. Idan Kuma kaje Kan batun fensho da kudin sallamar aiki na giratuti na ma’aikaci , a gaskiya ni Ina daga cikin wadanda muka zauna muka yi tsare tsare da Mai Girma Gwamna Kan yadda za’ayi Idan Yau ma’aikaci yayi ritaya zai shiga fansho Kuma Zai tafi da kudin sallamar sa aiki wato giratutinsa., Alhamdulillahi yanzu daga ma’aikaci yayi ritaya yake fara karbar fanshonsa bangaren giratuti ma saboda kudine da muka yi gadon bashinsa sosai, Wanda kudin ya kai Naira biliyan 70,000,000,000 amma damuwar mai girma gwamna ba wai kudinne bayaso ya biya ba, amma damuwar sa wa za’a biya? saboda bincike ne ake tayi,don a tantance a daidaita, wadanda za’a biya bisa gaskiya, Misali a Wani wurin Sai kaga sunan mutum daya ya fito a shekarar 2013,ya Kuma fitowa a 2014, ya fito a 2017, ya fito a 2019 Kuma ya fito a 2023. Haka zaka ga sunan yana ta maimaituwa Shi yasa Mai girma gwamna ya ce a tantance a gano masa gaskiyar wadanda za’a biya da Kuma ainihin yawan kudin da za’a biya.saboda abin ya yi tashin gwauron zabi, saboda lokacin da ya Karbi mulki a 2019 kudin bai wuce biliyan ashirin da uku ba. ₦23,000,000,000 ko Wani karshen shekara in yayi yunkurin Biya Sai ace kudin ya haura biliyan 30 Ko ya haura biliyan 40 Ko biliyan 50 haka abin yake ta hauhawa, har a yau ya zama sama da biliyan ₦70,000,000,000 . zuwa lokacin dana sauka daga mukamin kwamishinan kudi , ana Kan bincike an kawo hukumar fansho Suna Kan tantance wadannan sunaye, Kuma su Karbo kudin da za’a biya duk Wanda yake bin bashi bayan sun tantance, duk da irin wannan aikin da akeyi a kowani wata Mai girma gwamna yana ware Naira Miliyan dari biyar ₦500,000 a rage wa wadanda suka yi ritaya a cikin Ma’aikatan Jihar,ya Kuma sake ware Naira Miliyan dari biyar ₦500,000 a ragewa Ma’aikatan da sukayi ritaya a Kananan hukumomi ,Kuma kowani Wata Yana biyan wannan kudin , kafin a gama tantance wanda za’a biya, in an Kammala aikin in sha Allahu Zai biya Kowa, in ba’a kammala ba in mu ne Allah ya kawo mu zamu ci gaba abin mu daya ne har mu tabbatar kowa ya samu kudin sa.


