Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Gwamnonin Arewa Sunyi Allah Wadai Da Harin Jos
Published: March 31, 2026 at 11:38 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, ya yi Allah wadai da harin da aka kai Angwan Rukuba dake Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin takaici, abin zargi kuma wadda ya yi hannun riga da kyawawan ɗabi’un Arewacin Najeriya.

Da yake tsokaci martani jim kaɗan bayan kammala taron shekara-shekara na ƙungiyar da aka gudanar a masauƙin Gwamnan jihar Gombe dake Abuja, Gwamna Inuwa Yahaya yace gwamnonin sun kammala wata bita mai zurfi kan sha’anin tsaro a faɗin Arewa, inda suka sabunta ƙudurinsu na fuskantar ƙalubalen tsaro da tattalin arziki dake fuskantar al’ummar yankin.

Yace abin takaicin da ya faru a Jihar Filato ya ƙara ƙarfafa himmatuwar Ƙungiyar na tabbatar da zaman lafiya, tsaro da kuma yin haɗin gwiwa mai ƙarfi da hukumomin tsaro.

Shugaban ƙungiyar ya jaddada cewa irin waɗannan aika-aikan tashin hankali baƙon abu ne ga Arewa, yankin da aka san shi da zaman tare, girmama juna da ‘yan’uwantaka mai ɗorewa tsakanin al’ummomi daban-daban.

Gwamna Inuwa Yahaya ya yi ƙira ga al’ummar Jihar Filato, musamman waɗanda ke cikin yankin da abin ya shafa, su kwantar da hankalinsu su guji ɗaukar doka a hannunsu. Ya yi gargaɗin cewa ɗaukar fansa da kuma ɗaukar matakin tayar da hankali na iya ƙara ta’azzara yanayin da ya riga ya ƙazance.

Ya buƙaci shugabannin al’umma, malaman addini, kungiyoyin matasa, da duk masu ruwa da tsaki su yi aiki tare don samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Gwamna Inuwa Yahaya ya kuma yabawa Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, saboda matakan gaggawa da ya ɗauka don daƙile lamarin, musamman sanya dokar hana fita ta awanni 48 a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa da kuma tura jami’an tsaro cikin gaggawa don dawo da doka da oda.

A cewarsa, matakan da Gwamnatin jihar Filato ta ɗauka sun nuna kyakkyawan jagoranci wajen kare rayuka da kuma daƙile ci gaba da faɗaɗar rikicin.

“Ina yabawa ɗan’uwana gwamna mai girma Caleb Mutfwang, bisa matakan gaggawa da ya ɗauka don shawo kan lamarin da kuma dawo da kwanciyar hankali. Waɗannan matakai sun dace kuma suna da matuƙar muhimmanci wajen daƙile taɓarɓarewar doka da oda,” in ji shi.

Gwamnan na Gombe ya sake jaddada ƙudurin gwamnonin Arewa na ci gaba da baiwa rundunonin tsaro da sauran hukumomi tallafin da ya dace don sauƙe nauyin dake kansu na kundin tsarin mulki.

Yace kan ƙungiyar a haɗe yake kan ƙudurinta na ƙarfafa haɗin gwiwa don yaƙi da laifuka, tashin hankali da duk wata barazana ga zaman lafiya.

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa za a kamo waɗanda suka kai harin kuma a gurfanar da su gaban kuliya, yayin da yake miƙa ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar Jihar Filato, musamman iyalan da suka rasa ‘yan uwa a cikin wannan bala’i.

Ya yi addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka mutu, ya kuma yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga waɗanda suka jikkata

Afrika, Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Bayan Ya Ziyarci Kwankwaso Gawuna Zai Karbi Katin ADC
Next Post: Yusuf Gawuna Ya Koma Jam’iyar ADC

Karin Labarai Masu Alaka

Tinubu Yace Zayyi Hadaka Da Kasashen Duniya Domin Kawo Karshen Rashin Tsaro. Najeriya
Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata Afrika
Kudaden Shigan Kasar Namibia Ya Bunkasa Saboda Tashin Farashin Gwal Labarai
Bankin Duniya Ya Rage Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Afirka Da Yankin Sahara Afrika
Harin Makami Mai Linzami Da Rasha Ta Kai Yayi Barna Sosai A Ukraine Afrika
Jami’ar Tarayya A Gombe Ta Karyata Harin ‘Yan Bindiga Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Dan Takarar Gwamna Na Jam’iyyar APM A Bauchi Ya Bada Gudummawar Naira Miliyan ₦21 Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Bara Da Shira Labarai
  • Gwamnatin Najeriya Tace Ta Farmaki Mayakan ISIS A Jihar Sokoto Labarai
  • Barayin Waya Sun Yanke Yatsun Hannu Guda Biyu Da Gefen Kunne A Bauchi Labarai
  • Hukumar EFCC Ta Kwace Gidan Tsohon Antoni Janar Abubakar Malami Najeriya
  • Gwamnan Jihar Filato Ya Karbi Katin APC Labarai
  • Kotu A Abuja Tabawa Goodluck Jonathan Daman Tsayawa Takara Afrika
  • Farashin Danyen Mai A Amurka Ya Tashi Afrika
  • Tattalin Arzikin Najeriya Ya Farfardo Bisa Samun Wasu Sauye Sauye Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.