Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi Afrika
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya Afrika
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91 Afrika
  • Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu Afrika
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika

Gwamnatin Tinubu Zata Gyara Hanyar Akwanga Zuwa Jos
Published: January 27, 2026 at 10:08 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: January 27, 2026

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yayi alkawarin gyara hanyar Akwanga a jihar Nasarawa zuwa Jos a jihar Filato.

Shugaban kasar yayi wannan alkawari ne yayin karbar gwamnan jahar Filato, Caleb Mutfwang wanda ya chanza sheka daga jami’iyyar PDP zuwa jami’iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Dubban jama’a ne, musamman ‘ya’yan jami’iyyar APC da suka hada da shugaban majalisar dattawan Najeriya, sanatoci, shugaban majalisar wakilai da ‘yan majalisar, gwamnoni da shugabannan APC daga matakin kasa zuwa jaha da kananan hukumomi ne suka yi cincirindo a Jos, don nuna goyon baya wa gwamnan jahar Filato, Caleb Mutfwang daya shiga jami’iyyar APC.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu wanda mataimakinsa sanata Kashim Shettima ya wakilta a wurin taron, ya fara ne da yabawa Gudunmawar da wassu ‘ya’yan jahar Filato da suka hada da Janar Yakubu Gowon, Marigayi Solomon Lar, Marigayi Jeremiah Useni da sauransu, suka bayar wajen gina Najeriya da hada kan kasar da ma sadaukar da kai da suka yi a bangaren siyasa.

Mataimakin shugaban kasar yace nan da makonni uku, dan kwangila zai fara gudanar da aikin hanyar Akwanga zuwa Jos.

A nasa jawabin, gwamnan jahar Filato, Caleb Mutfwang yace shugaban kasa Bola Tinubu ne ya gayyato shi shiga jami’iyyar APC, kuma ya amince ne saboda ya lura da aniyarsa ta sanya fasalin Najeriya don maida ita kan turbar hadin kai da ci gaba.

Gwamnan na jahar Filato, Caleb Mutfwang yace wadansu na cewa mun sauya sheka, sam ba haka bane, muna sake daidaitawa da samadda dabarun samun romon damokradiyya ne wa jahar Filato.

Da yake mika wa gwamnan tutar APC da tsintsiya, shugaban jami’iyyar APC, Farfesa Nentawe Yilwatda yace tsintsiyar zata share rarrabuwar kawuna, ta kuma share rashawa ta kuma samadda hadin kai.

Shugaban jami’iyyar ta APC yace ‘’ina tabbatar maka, Caleb Mutfwang, zaka dawo gidan gwamnati a matsayin gwamna a shekara ta dubu biyu da ishirin da bakwai, don zamu baka goyon baya.’’

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya yi addu’a ne da daukan matakan mai da ‘yan gudun hijira a jahar Filato zuwa gidajensu.

Shugaban majalisar dattawan yace, ina so in shaida maka cewa majalisar tarayya zata tattauna kan matakan samadda kudade da zai baka damar mai da jama’ar ka dake sansanonin gudun hijira zuwa kauyukan su.

Gwamnan jahar Nasarawa, Abdullahi Sule, wanda shine shugaban majalisar gwamnonin Arewa tatsakiya yace a yanzu dukkan gwamnonin shiyyar suna jami’iyya daya.

Abdullahi Sule yace ‘’saboda mun yi imanin APC itace amintacciyar jami’iyya dake da kyakkyawar tawaga ta Bola Tinubu da Kashim Shettima kuma suna da goyon baya mai karfi daga Arewa ta tsakiya.

Gwamnonin jahohin Lagos, Katsina, Borno, Edo, Ebonyi Sokoto da Taraba ne suka halarci taron, yayinda mataimakin gwamnan jahar Gombe da wassu jahohin suka wakilci gwamnoninsu.

A yanzu dai gwamnoni ishirin da tara ne daga cikin talatin da shida a fadin Najeriya ke jami’iyyar APC, a daidai lokacin da jami’iyyar ta sha alwashin mai da Najeriya kasa mai jami’iyya daya.

Daga Jos Ga Rahoton Zainab Babaji

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/01/AUD-20260127-WA0041.mp3

 

Labarai, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Amurkawa Sun Nuna Bacin Rai Saboda Yawaita Kashe ‘Yan Kasar
Next Post: An Tsinci Gawar Yarinya A Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

Yamai Cikin Rashin Tabbas Bayan Karar Harbe-Harbe Da Aka Ji Afrika
Kasar China Ta Kaddamar Da Rawar Daji A Yankin Taiwan Labarai
Fiye Da Mutane 10 Sun Mutu A Hatsarin Hanyar Kano Labarai
CP Chuso Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Gwiwar Hukumomin Tsaro A Gombe Afrika
Hukumar Zaben Najeriya Ta Sanar Da Ranar Zaben Shugaban Kasa Labarai
Gwamnan Jihar Kebbi Ya Amince Da Kasafin Kudi Mai Sauya Fasali Da Karfafa Rayuwar Al’umma Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91
  • Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Rivers: ‘Yan Majalisa 16 Sun Canza Sheka Zuwa APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Real Madrid: Ta Kori Xabi Alonso Bayan Rashin Nasara A Wasan Kofin Sfaniya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Yau Litinin Za’a Mika Daliban Ga Iyayen Su Labarai
  • Gwamnatin Filato Ta Gurfanar Da Maharan Rukuba A Kotu Afrika
  • Addini Ko Kabilanci Basu Da Gurbi Cikin Ta’addanci Labarai
  • Gwamnatin Najeriya Tace Ta Farmaki Mayakan ISIS A Jihar Sokoto Labarai
  • Gwamnatin Tarayya Tana Neman Kudi Domin Aiwatar Da Kasafin Kudin 2026 Najeriya
  • Jamhuriyar Dimokraɗiyya Kwango Zata Karbi ‘Yan Gudun Hijirar Da Amurka Ta kora Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.