Yayin da manyan shugabannin harkokin kiwon lafiyar duniya ke taruwa a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu domin halartar taron duniya karo na 18 kan lafiyar jama’a, shirin SARMAAN na Najeriya na samun yabo da kulawa saboda yadda yake aiwatar da manyan shirye-shiryen inganta lafiyar yara tare da tabbatar da tsaro da kuma sa ido kan juriyar ƙwayoyin cuta ga magunguna.
An gudanar da taron ne karkashin taken “Lafiya Ba Ta Da Iyaka: Daidaito, Haɗa Kowa da Dorewa,” inda ake tattauna muhimman batutuwa da suka haɗa da juriyar ƙwayoyin cuta ga magunguna, daidaito wajen samun damar kiwon lafiya da kuma tsarin One Health.
A halin yanzu, shirin SARMAAN ya kai maganin Azithromycin ga sama da yara miliyan 16 a jihohi 11 na arewacin Najeriya.
Shirin ya haɗa bayar da maganin ga dimbin yara da kuma sa ido kan lafiyarsu, tare da gudanar da bincike kan juriyar ƙwayoyin cuta ga magungunan kashe ƙwayoyin cuta.
Masu gudanar da shirin sun ce wannan tsarin na tabbatar da cewa yayin da ake faɗaɗa ayyukan zuwa ga miliyoyin yara, ana kuma kiyaye matakan da suka dace na kare lafiyar jama’a.
Babban mai bincike na shirin SARMAAN kuma Daraktan Bincike a Cibiyar Nazarin Likitanci ta Najeriya, Farfesa Oliver Ezechi, ya ce bin ƙa’idojin kimiyya da kuma gudanar da manyan shirye-shiryen kiwon lafiya na iya tafiya tare.
A Najeriya, adadin mace-macen yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar ya ragu daga mutuwar yara 132 cikin kowane haihuwa 1,000 a shekarar 2018, zuwa 102 cikin 1,000 a binciken Demographic and Health Survey na shekarar 2023 zuwa 2024.
Sai dai duk da wannan ci gaba, adadin ya kasance sama da burin da aka gindaya a cikin Muradun Ci Gaba Mai Ɗorewa na Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda ke nufin rage mace-macen yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar zuwa 25 cikin kowane haihuwa 1,000.
Jakadiyar shirin SARMAAN, Dakta Zainab Shinkafi-Bagudu, ta ce samun daidaito na gaskiya a fannin kiwon lafiya na nufin tabbatar da cewa kowane yaro ya samu damar cin gajiyar matakan ceton rai, ba tare da la’akari da inda yake zaune ba.
A jihar Jigawa kuma, Uwargidan Gwamnan jihar, Hajiya Hadiza Umar Namadi, ta jaddada muhimmiyar rawar da iyaye mata, masu kula da yara da kuma al’umma ke takawa wajen samar da amincewa da shirin.
Ta ce haɗin kan iyaye da al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da nasarar shirye-shiryen kiwon lafiyar yara.
Kwarewar shirin SARMAAN ta nuna cewa jagorancin gwamnati, amincewar al’umma da kuma hujjojin kimiyya na iya haɗuwa wajen aiwatar da manyan shirye-shiryen kiwon lafiya, tare da ba da fifiko ga tsaro da kare lafiyar jama’a.


