Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Shugaba Tinubu Ya Kafa Kwamitin Gaggawa Akan Cutar Ebola
Published: June 11, 2026 at 3:33 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Bola Ahmed Tinubu, ya amince da kafa Kwamitin Musamman na Fadar Shugaban Ƙasa kan Shirin Kariya daga Cutar Ebola da Sauran Barazanar Lafiyar Jama’a, tare da bayar da umarnin sakin naira biliyan 10 domin shirye-shiryen gaggawa.

A cewar sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Talata, kuɗaɗen za su taimaka wajen ƙarfafa shirye-shiryen Hukumar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Ƙasa (NCDC) da kuma ayyukan da suka shafi tunkarar duk wata barazanar gaggawa ga lafiyar al’umma.

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ne zai jagoranci sabon kwamitin, wanda zai haɗa da wakilai daga ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati daban-daban, da kuma wakilan jihohi.

Matakin ya biyo bayan sake bullar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) da kuma Uganda.

Shugaba Tinubu ya amince da kafa kwamitin ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa ya jagoranta domin nazarin irin shirin da Najeriya ta yi da kuma dabarun da za su hana cutar shiga ƙasar.

Daga cikin mahalarta taron akwai wakilai daga Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN), Hukumar Shige da Fice (NIS), Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama (NCAA), da gwamnatin jihar Legas.

Shugaban ƙasar ya kuma umarci dukkan jihohin da ke da filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa da kuma manyan hanyoyin shiga ƙasar daga ƙasashen waje da su gabatar da tsare-tsarensu, buƙatun kuɗi da irin tallafin da suke buƙata domin aiwatar da matakan kariya cikin haɗin gwiwa.

A cikin matakan da aka sanar za a ɗauka akwai ƙara tsaurara binciken fasinjoji a dukkan filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa, ciki har da duba zafin jiki da tsara yadda jama’a ke shiga da fita.

Haka kuma za a ƙarfafa sa ido kan fasinjojin da ke shigowa ta wasu hanyoyin jiragen sama da gwamnati ta ayyana a matsayin masu haɗari, ciki har da Air Uganda, RwandAir, Air Tanzania, Air Angola, Kenya Airways da Ethiopian Airlines.

Gwamnatin ta ce za a gaggauta bude cibiyoyin killace marasa lafiya da wuraren tura waɗanda ake zargin sun kamu da cutar a filayen jiragen saman Legas da Abuja, kafin daga baya a faɗaɗa tsarin zuwa sauran filayen jiragen saman ƙasar.

Sauran matakan sun haɗa da wajabta cike bayanan lafiyar matafiya ta hanyar tsarin QR Code kafin su iso ƙasar idan sun fito ko suka bi ta ƙasashen da aka ayyana masu haɗari, da kuma tsaftace dakunan tashi da saukar jirage, wuraren kaya da sauran sassan filayen jiragen sama.

Shugaba Tinubu ya kuma umarci kwamitin da ya tattauna da hukumomin tsaro, diflomasiyya da sufurin jiragen sama kan yiwuwar ɗaukar ƙarin matakan da suka shafi zirga-zirgar jirage daga ƙasashen da cutar ta bulla ko waɗanda aka sanya cikin jerin masu haɗari.

Bugu da ƙari, kwamitin zai duba yiwuwar ware wasu filayen jiragen sama ko tashoshi na musamman domin karɓar jiragen da ake ganin suna da haɗari, tare da nazarin sauya lokutan saukar wasu jirage domin rage haɗuwar fasinjojin da ake sa ran za su buƙaci ƙarin bincike da sauran matafiya.

Afrika, Kiwon Lafiya, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Shirye-Shirye

Post navigation

Previous Post: ‘Yan Sandan Gombe Sun Fara Kama Motocin Da Ba Su Da Lambar Rajista ko Masu Boye Lambobinsu
Next Post: Uefa Ta Zabi Artan, Ya Jagoranci Wasan Cin Kofin Uefa Super Cup

Karin Labarai Masu Alaka

‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Gwamnatin Soji A Nijar Ta Hana Fitar Da Albarkatun Kasa Afrika
Gwamnatin Bauchi Ta Amince Domin Inganta Kasuwancin Nama A Jihar Labarai
Asusun IMF Ya Bukaci Afirka Ta Kudu Ta Rage Bashin Da Suke Karba Afrika
Amurka Tafara Yiwa Kasar Iraq Barazana Amurka
‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 30 A Jihar Neja Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Guterres: Babban Kuskure Ne Yadda Isra’ila Ta Kai Farmaki A Gaza Labarai
  • Jami’an Diflomasiyyar Iran Dana Amurka Sun Tattauna A Kasar Oman Afrika
  • Bayan Ya Ziyarci Kwankwaso Gawuna Zai Karbi Katin ADC Afrika
  • Masar Ta Jibge Jiragen Yaki Marasa Matuka Afrika
  • Dakarun Operation Fansan Yamma Sun Ceto Mutane 48 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Afrika
  • EU Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Amurka Da Iran Afrika
  • Man Da Matatar Dangote Take Fitarwa Zuwa Kasashen Afirka Ya Karu Afrika
  • Najeriya: Ta Aiwatar Da Tsarin Ba Aiki Ba Albashi Ga Ma’aikata Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.