Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Gombe: ‘Yan Sanda Sun Tarwatsa Ƙungiyar Masu Fashi Da Damfara Ta Yanar Gizo
Published: July 8, 2026 at 4:50 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe ta sanar da samun gagarumar nasara a yaƙi da aikata manyan laifuka, inda ta kama wata ƙungiyar mutum takwas da ake zargi da aikata fashi da makami da damfarar intanet, tare da ceto wani yaro mai shekara takwas da aka sace da kuma kama mutum huɗu da ake zargi da hannu a lamarin.

Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a helkwatar Hukumar Dake Gombe, inda ya yi bayani kan nasarorin da rundunar ta samu da kuma matakan tsaro da take ɗauka domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

.

A cewarsa, bincike ya fara ne bayan wasu mazauna unguwar Wuro Birji da ke ƙaramar hukumar Akko sun kai rahoton cewa wasu mahara sun tare su tare da kwace wayoyin salularsu a ranar 7 ga Yunin 2026.

Binciken ‘yan sanda ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun yi amfani da bayanan da ke cikin wayoyin wajen shiga asusun ajiyar kuɗin waɗanda abin ya shafa ba tare da izini ba, inda suka cire Naira dubu 296 da 790, sannan suka karɓi rancen gaggawa na Naira dubu 205 da 205 ta hanyar yanar gizo.

Kwamishinan ya ce bayanan sirri da binciken fasaha sun kai ga cafke jagoran ƙungiyar, Mustapha Kabiru, wanda aka fi sani da “Musty Bobo”, ɗalibi mai shekara 19 a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Kaltungo. Furucinsa ya kai ga kama sauran mutum bakwai da ake zargi suna cikin ƙungiyar.

Ya ƙara da cewa bincike ya nuna ƙungiyar na da alaƙa da fiye da hare-hare goma sha uku da suka faru a Wuro Birji, Riyal, Bomala da Jauro Jatau, yayin da ake ci gaba da neman sauran waɗanda suka tsere.

Dangane da aiwatar da dokokin hanya, CP Chuso ya ce rundunar ta tsaurara matakan kama motocin da ke amfani da lambobin rajista da aka rufe, aka lalata, aka sauya ko kuma ba su da lambobin rajista.

Ya bayyana cewa tun bayan fara wannan sintiri a ranar 16 ga Yunin 2026, rundunar ta kama motoci 121, yayin da aka gurfanar da mutum 114 a kotu bisa laifin karya dokokin zirga-zirgar ababen hawa.

Kwamishinan ya kuma buƙaci masu ababen hawa su tabbatar da cewa sun yi wa motocinsu rajista tare da sanya lambobin rajista yadda doka ta tanada.

Haka kuma, CP Chuso ya sanar da nasarar ceto wani yaro mai shekara takwas da aka sace bayan ya fita daga gidansu a ƙaramar hukumar Akko a ranar 27 ga Yunin 2026.

Ya ce binciken da aka gudanar ya kai ga kama Abdullahi Mohammed a Kumo, wanda furucinsa ya taimaka wajen kama wasu mutum uku da ake zargi da hannu a lamarin, wato Mohammed Magaji, Sale Sale da Walida Ya’u.

An ceto yaron cikin ƙoshin lafiya tare da miƙa shi ga iyalansa, yayin da ake ci gaba da bincike kafin gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu.

A wani ɓangare kuma, Kwamishinan ya ce rundunar ta ƙaddamar da shirin Yaƙi da Ƙungiyoyin Asiri da Sauran Munanan Ɗabi’u (POCACOV) domin wayar da kan matasa da ɗalibai game da illolin daba, shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka.

Ya kuma ce wani samame da aka kai maboyar masu aikata laifuka a cikin birnin Gombe a ranar 7 ga Yuli ya kai ga kama mutum 44, inda aka samu wasu daga cikinsu da makamai masu haɗari, tabar wiwi da sauran miyagun ƙwayoyi.

CP Umar Ahmed Chuso ya jaddada kudirin rundunar na ci gaba da gudanar da aikin ‘yan sanda bisa bayanan sirri da haɗin gwiwar al’umma, tare da kira ga mazauna jihar da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Gombe.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Yayale Ahmed Ya Jagoranci Kwamitin Amintattu Na Asusun Tsaron Arewa
Next Post: Gobara Ta Lalata Babban Zauren Majami’ar ECWA Gospel A Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

Kawayen Amurka Bazasu Shiga Matakin Shugaba Trump Ba Amurka
Domin Karfafa Tsaro Babban Hafsan Sojin Najeriya Ya Ziyarci Jos Afrika
Hukumar Tsaro Ta DSS Ta Aika Sammaci Dr. Yusuf Baba-Ahmed Labarai
Gwamnatin Najeriya Tana Saka Ido Akan Matsalolin Gabas Ta Tsakiya Afrika
Sama da mutane dubu 500 ne yanbindiga suka kora daga gidajensu a Jihar Nejan Najeriya. Najeriya
Birtaniya Zata Hana Jiragen Ruwan Rasha Wucewa Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gidauniya: An Fara Tiyatar ‘Hernia’ Da ‘Hydrocele’ Kyauta A Jihar Katsina Labarai
  • Gurbin Yaya Tongo: INEC Ta Tsayar Da 19 Ga Satumba Don Zaɓen Cike Gurbi Afrika
  • Kungiyar Mata Manoma A Najeriya Ta Raba Kyautar Abinci A Gombe Afrika
  • Jirgin Ruwa Ya Kife A Yammacin Kasar Gambiya Labarai
  • Chelsea Tayi Kaca-Kaca Da Barcelona A Gasar UCL Wasanni
  • APC Ta Yi Babban Taron Amincewa Da Shugabannin Jam’iyyar Ba Hamayya Najeriya
  • Shugaba Tinubu Ya Yabawa Dakarun Tsaro Bisa Ceto Matar Marigayi Janar Rabe Afrika
  • Koriya Ta Arewa Ya Goyi Bayan Iran Wajen Zaben Sabon Jagora Mojtaba Khameni Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.