Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi Afrika
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya Afrika
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91 Afrika
  • Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu Afrika
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika

Shugaba Trump Yace Amurka Da Iran Suna Cigaba Da Tattaunawa
Published: February 3, 2026 at 10:47 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

A gabas ta tsakiya kuma, Shugaban Amurka Donald Trump, ya fadawa manema labarai a fadar White House ranar Litinin cewa, Washington da Iran suna ci gaba da gudanar da shawarwari, yayinda manyan jiragen yaki na ruwan Amurka suke kara zuwa yankin inji Mr. Trump.

A halinda ake ciki kuma, rahotanni suna nuni da cewa mahukunta a Tehran suna kara nuna damuwa sosai cewa duk wani hari daga Amurka zai sake tunzura masu zanga zanga a kasar da suka hau kan tituna, kuma wannan karon saboda mummunar matakin murkushe masu zanga zangar da hukumomin kasar suka yi a baya bayan nan, mutane sun fusata wadda ya kawar da duk wani tsoro. Akwai alamun jama’ar kasar yanzu a shirye suke su tunkari jami’an tsaro.

Rahoton yace wannan mataki zai kai ga rushewar gwamnati, kamar yadda wasu majiyoyi suka ce an gayawa shugaban addinin kasar Ayatollahi Ali Khamei a zaman shawarwari da suka yi.

Daya daga cikin jami’an kasar ya gayawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, makiyan Iran suna son ganin karin zanga zanga domin kawo karshen gwamnatin kasar mai bin tafarkin Islama, yace idan haka ta faru abun takaici ne domin hakan zai haifar da tarzoma idan zanga zanga ta sake barkewa.

Amurka, Labarai

Post navigation

Previous Post: Shugaban Trump: Washington Zatayi Cinikayya Da Indiya
Next Post: Rundunar Wanzar Da Zaman Lafiya Zata Tabbatar Da Tsagaita Wuta A Kwango

Karin Labarai Masu Alaka

RUWASSA Ta Hada Masu Ruwa Da Tsaki Domin Inganta Aiwatar Da Shirin NG-SURWASH Afrika
Majalisar Dattawa Ta Amince Tinubu Ya Tura Sojoji Benin Labarai
Wakilan Majalisar Dokokin Phillipines Suna Yunkurin Tsige Shugaban Kasar Afrika
Trump: Zamu Kawo Zaman Lafiya A Fadin Duniya Amurka
Mala Buni: Zai Jagoranci Kwamitin Sassanci Na Jam’iyar APC Labarai
Afirka Ta Kudu Ta Kubutar Da ‘Yan Kasar Da Suke Taya Sojojin Rasha Yaki Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91
  • Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Tarayya Na Kokarin Hana Demokraɗiyya A Najeriya Siyasa
  • “Hotuna” An Sako Daliban Makarantar St. Mary’s Su 100 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ana Cigaba Da Ceto Masunta Daga Ruwa A Ghana Labarai
  • An Gudanar Da Zanga-Zanga A Guinea-Bissau Afrika
  • Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Gargadi Jama’ar Arewa Maso Gabas Afrika
  • Abu Mafi Daukar Hankali A Wasan Dambe Na Yau Wasanni
  • Mutane Da Dama Sun Rasa Rayukansu Yayin Rikici A Uganda Siyasa
  • Kasar China Tana Cigaba Da Nuna Fin Karfi Ga Kasar Taiwan Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.