Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Hukumar EFCC Ta Kwace Gidan Tsohon Antoni Janar Abubakar Malami
Published: December 17, 2025 at 9:53 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC) ta rufe wani gida da ke da alaka da tsohon Antoni Janar na ƙasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, a daren Laraba, a matsayin wani bangare na binciken cin hanci da rashawa da ake yi masa.

Rahotanni sun ce jami’an EFCC tare da jami’an tsaro sun isa gidan, inda aka ce Nana Hadiza Buhari, ’yar tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kuma matar Malami, tana nan a lokacin da aka gudanar da aikin.

Matakin na zuwa ne yayin da EFCC ke ci gaba da tsare Malami bisa zargin cin hanci da rashawa, halasta kudaden haram da wasu laifuka da suka shafi kudaden Abacha da aka kwato.

EFCC ta bayyana cewa belin da aka ba Malami a baya an soke shi saboda rashin cika sharudda, kuma har yanzu yana hannun hukuma domin ci gaba da bincike.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata sanarwa daga bangaren Malami ko iyalan Buhari kan lamarin.

Najeriya

Post navigation

Previous Post: Afirka Ta Kudu Ta Kama ‘Yan ƙasar Kenya Su Bakwai
Next Post: ‘Yan Tawayen M23 Masu Samun Goyon Bayan Rwanda Basu Jamye A Ulvira Ba

Karin Labarai Masu Alaka

Jami’an ‘Yan Sanda A Gombe Sun Kama Barayi Afrika
Gwamnatin Najeriya Ta Samar Da Wuta Mai Aiki Da Hasken Rana A Jami’ar ADUSTECH Afrika
Mutane 27 Sun Rasa Rayukan Su A Najeriya Afrika
An Damke Wani Likita Da Ke Taimakawa ‘Yan-Ta’adda Najeriya
Damara Ya Tallafa Wa Gasar Karatun Al-Qur’ani Da Naira Miliyan Biyar A Bambam Afrika
Tsohuwar Ministan Albarkatun Mai Ta Bayyana A Kotu Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Dakarun Tsaron Ruwan Amurka Sunfara Killace Hanyoyi Amurka
  • APC Ta Bayyana Abba Yusuf A Matsayin Halastaccen Ɗan Takara Bayan Cika Sharudda Afrika
  • Kasar Gambiya Ta Gayawa Kotun MDD Shirin Myanmar Akan Musulmai Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Tace A Maboyar ‘Yan Ta’adda Aka Kai Harin Jilli Afrika
  • Sama da mutane dubu 500 ne yanbindiga suka kora daga gidajensu a Jihar Nejan Najeriya. Najeriya
  • Kasar Spain Zata Bada Diyya Ga Iyalen Wadanda Da Suka Rasu A Hatsarin Jirgin Kasa Labarai
  • UPF Ta Bukaci Haɗin Gwiwa Da NERDC Domin Gina Al’umma Mai Zaman Lafiya Afrika
  • Kadan Daga Cikin Abubuwan Da Suka Faru A 2025 A Nan Amurka Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.