Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Taron Sulhu Tsakanin Addinai Mabanbanta Na Arewacin Najeriya
Published: December 18, 2025 at 3:32 PM | By: Yusuf Aliyu Harande

Ganin yadda rabuwar kawunan al-uma da banbance banbance awarewacin Najeriya ke kara rura wutar matsalar tsaro ya sa kungiyoyin yankin hada wata sabuwar kungiyar sulhu da sasanta juna domin hada kan al-umar yankin da nufin magance matsalolin tsaro da tattalin arziki da riki tsakin al-umomin yankin baki daya.
Sabuwar kungiyar sulhu da hada kawunan al-uma a arewacin Najeriyan da ke karkashin Jagorancin tsohon mai-baiwa shugaban kasa shawara kan ta harkokin siyasa a offishin mataimakin shugaban kasa Dr. Hakeem Baba-Ahmed ta hada da kungiyar musulmin Najeriya ta Jama’atu Nasrul-Islam da kuma ta Kiristoci CAN da sauran kungiyoyin arewa kuma a jiya Laraba kungiyar ta fara ziyarar hada kawunan al-umar yankin baki daya.
Daga Kaduna, Wakilin mu Isah Lawal Ikara ya bi tawagar kungiyar zuwa ofisoshin kungiyar Jama’atu Nasrul-Islam da kuma Kungiyar Kiristocin Najeriya ta CAN, kuma ga rahoton da ya aiko mana……
Rashin jituwa tsakanin mabiya addinin Musulunci da Kirista da kuma maganar matsalar tsaro da talauci dai na cikin manyan matsalolin dake damun yankin arewacin Najeriya, harma wasu na ganin hakan ne ya sa shugaba Donald Trump na Amurka barazar aike sojoji yankin da sunan yakar  ‘yan-ta’adda. Sai dai shugaban wannan kungiya ta sulhu Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya ce kungiyar ta shirya share  wannan damuwa dake damun Arewa.
Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya reshen  Arewaci Rebaren Joseph John Hayaf ya ce gaske an sami baraka tsakanin al-umar arewa a baya amma yanzu an gano bakin zaren.
Babban Sakataren kungiyar Jama’atu Nasrul-Islam na Kasa Farfesa Khalid Aliyu Abubakar ya ce Arewa ta gane ciwon da ke damun ta kuma ta samu magani.
Game da banbancin wannan sabuwar kungiyar sulhu da sauran kungiyoyin da aka kafa da irin wadan nan manofofi a arewa kuwa, Rebaren Joseph John Hayaf ya ce ita wannan sabuwar kungiyar hadaka ce ta dukkan manyan kungiyoyin arewacin Najeriya.
Arewacin Najeriya dai ya sha fara da rikice-rikicen addini da na kabilanci wanda wasu ke ganin matsalar tsaron dake damun yankin ma ana shafa mata addini da kabilanci duk lolacin da ‘yan-ta’adda ko ‘yan-bindiga su ka kashe mutane. Abun jira a gani kuma shine, shin wannan sabuwar kungiyar za ta iya magance wannan matsalar da ta ki-ci ta-ki cinyewa.
Labarai

Post navigation

Previous Post: Najeriya Ta Mika Koke Ga FIFA Tana Zargin DR Congo Ta Sanya ‘Yan Wasan Da Basu Cancantaba
Next Post: Tinubu Ya Nada Shugabannin Hukumar NERC

Karin Labarai Masu Alaka

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso Ya Fice Daga NNPP Afrika
Ukraine Zata Sayi Iskar Gas Daga Mozambique Afrika
Amurka Zata Bawa Sojojin Najeriya Horo Labarai
Jam’iyyar APC Ta Rantsar Da Sabbin Shugabanni a Jihar Neja Labarai
An Gudanar Da Tiyatar Ido Kyauta A Gombe Afrika
Shugaban Kasar Tunisiya Ya Tsawaita Dokar Da Baci A Kasar Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Iran Ta Kama Wasu ‘Yan Leken Asiri Afrika
  • Ruwa Kamar Da Bakin Kwarya Ya Haifar Da Mutuwar Mutane A Nairobi Afrika
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Talata 11.18.2025 Rediyo
  • Jami’an Shige Da Ficen Amurka Sun Harbe Wani Har Lahira Amurka
  • Majalisar Dattawa Ta Amince Tinubu Ya Tura Sojoji Benin Labarai
  • Iran Tace Farisa Zata Kai Hari Kan Mayakan Amurka Amurka
  • Ruwan Sama Yayi Ajalin Mutane 70 A Nairobi Afrika
  • Gabannin Harin Amurka Da Isra’ila Iran Farisa Ta Shirya Nata Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.