Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Amurka Da Iran Sun Cimma Yarjejeniya Tsagaita Wuta Na Makonni
Published: April 8, 2026 at 7:05 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaba Donald Trump na Amurka, ya yarda da shirin tsagaita wuta na tsawon makonni biyu da kasar Iran, ana saura sa’o’i biyu kafin wa’adin da ya ba hukumomin Tehran na su bude mashigin ruwan Hormuz, ko kuma ya sa sojojinsa su kai munanan hare-hare a kan cibiyoyi da kayayyakin bukatu na fararen hular kasar domin aiwatar da abinda ya kira shafe jinsin Farisawa daga doron kasa.

A nata bangaren, Iran ta ce za a fara tattaunawa tsakaninta da Amurka ranar jumma’a a Islamabad, babban birnin Pakistan, kasar da firayim ministanta ya shiga tsakani domin ganin an cimma tsagaita wutar.

Har ya zuwa wannan lokaci, Amurka ba ta tabbatar da yin tattaunawa ido da ido tsakanin kasashen biyu ba, amma ta ce ana tattauna hakan.

Shugaba Trump yace Iran ta gabatar da wasu ka’idoji guda 10 wadanda yace ana iya amfani da su a zaman harsashin yin shawarwari, kuma yana sa ran za a kammala a rattaba hannu a kan yarjejeiya cikin wannan wa’adi na makonni biyu.

Trump yace wannan tsagaita wuta da aka cimma daiai lokacin da aski ke zuwa gaban goshi a wa’ad9n barazanarsa, ta dogara a kan cewa Iran zata kyale a c gaba da jigilar mai ta mashigin ruwan Hormuz.

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya fada cikin wata sanarwar da ya bayar cewa Iran zata dakatar da kai hare-haren ramuwar gayya, kuma zata bari jirage su shige cikin lumana ta mashigin ruwan na Hormuz.

Gidan telebijin na Iran ya ce shugaba Trump ya amince da ka’idojin da Iran ta shimfida na kawo karshen yakin, tana mai bayyana hakan a zaman ba da kai bori ya hau ga shugaban na Amurka.

Kakakin fadar White House Karoline LEavitt ta maida martani da cewa gaskiyar magana ita ce shugaba Trump da karfin sojojin Amurka suka sa Iran ta yarda zata sake bude mashigin ruwan Hormuz, kuma za a ci gaba da tattaunawa.

‘Yan mintoci kadan a bayan da shugaba Trump ya bada sanarwar tsagaita wutar, hannayen jari a Amurka sun cira sama. Farashin man fetur ya subuto kasa, inda a Amurka Farashin gangar danyen mai ya fado da kimanin kashi 17 cikin 100.

Wannan sanarwar tsagaita wuta ta shugaba Trump, sauyin alkibla ce ta mai gaba daya daga abinda ya furta ‘yan sa’o’i kafin nan inda yayi gargadin cewa idan har ba a biya masa bukatunsa ba, to zai shafe jinsin Farisawa daga bangon duniya baki daya cikin daren nan da ya shige.

A halin da ake ciki, jaridar New York Times ta buga rahoton cewa wani jami’in Amurka ya shaida cewa Amurka ta dakatar da duk wani harin sojan da take kaiwa kan kasar Iran bisa sharrudan wannan yarjejeniyar tsagaita wuta ta makonni biyu.

Sai dai kuma a wani bangaren gidan telebijin na Channel 12 na Isra’ila, ya ce sojojin kasar sun kai sabbin hare-hare ta sama kan Iran cikin asubahin larabar nan, a bayan da Trump ya bada sanarwar tsagaita wuta.

Gidan telebijin din yace an kai hare-haren ne a saboda Iran ta ci gaba da harba makamai masu linzami a kan Isra’ila.

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Jami’an Tsaro A Jihar Borno Sun Kama ‘Yan Bindiga
Next Post: Iran Da Amurka Sun Gindayawa Juna Ka’idojin Tsagaita Wuta

Karin Labarai Masu Alaka

Kungiyar Kwadago Ta NLC Ta Gudanar Da Zanga-Zanga Bisa Matsalar Tsaro Tsaro
Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran Amurka
Harin Iran A Kasar Saudiya Ya Haifar Da Tattaunawa Tsakanin Shugabanni Afrika
Emmanuel Macron: Yakamata Wani Sashi Ya Rika Takawa Wani Sashi Birki A Tsarin Demokradiya Amurka Amurka
Hawan Durba A Fadar Sarkin Zazzau Afrika
Gwamnatin Najeriya Ta Samar Da Wuta Mai Aiki Da Hasken Rana A Jami’ar ADUSTECH Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasar Gambiya Ta Gayawa Kotun MDD Shirin Myanmar Akan Musulmai Afrika
  • Gwamnatin Kasar Ghana Ta Rage Farashin Cocoa Afrika
  • Shugaban Rasha Yafara Ganawa Da Jakadun Amurka Domin Kawo Karshen Yakin Ukraine Amurka
  • Zabebben Shugaban Hungary Yace Zaidawo Da Tsarin Dimokraɗiyya Afrika
  • Farashin Mai Yana Cigaba Da Karuwa Afrika
  • Isra’ila Ta Kashe Babban Jami’in Tsaron Iran Ali Larjani Afrika
  • Kungiyar Mata Manoma A Najeriya Ta Raba Kyautar Abinci A Gombe Afrika
  • Kasar Saudiya Ta Sanar Da Ganin Watan Azumi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.