Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

‘Yan Tawayen Kungiyar M23 Sun Tsagaita Sakamakon Rokon Da Amurka Tayi
Published: December 16, 2025 at 8:11 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

‘Yan tawayen kungiyar M23 masu samun goyon bayan Rwanda sun ce zasu janye daga garin Uvira na yankin gabashin Kwango ta Kinshasa, a bisa rokon da gwamnatin Amurka ta yi musu.

Gwamnatin shugaba Trump ta bayyana kama wannan gari da ‘yan tawayen suka yi a makon da ya shige a zaman matakin barazana ga kokarin yin sulhu a yankin.

‘Yan tawayen sun kwace garin na Uvira dake bakin iyakar Kwango da Burundi, kasa da mako guda a bayan da shugabannin kasashen Rwanda da Kwango suka gana da shugaba Trump a birnin Washington domin rantaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya.

A ranar asabar sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, yace take-taken Rwanda a yankin gabashin Kwango sun keta haddin yarjejeniyar zaman lafiyar Washinton, ya kuma lashi takobin daukar matakan tabbatar da cewa sassan sun cika alkawuran da suka dauka.

Rwanda ta musanta cewa tana tallafawa ‘yan tawayen na M23, tana mai zargin sojojin Kwango da na Burundi da laifin sake barkewar fadan.

Rahoton da wasu kwararru na MDD suka rubuta a watan Yuli, yace kasar Rwanda ce take ba da umurni tare da tsara dukkan ayyukan ‘yan tawayen.

Amurka

Post navigation

Previous Post: Majalisa Ta Sanya Baki Akan Rikici Tsakanin Dangote Da Hukumar Albarkatun Mai
Next Post: Aliko Dangote: Faruk Ahmed Ya Ci Amanar ‘Yan Najeriya!

Karin Labarai Masu Alaka

Wani Bincike Ya Nuna Cewar Da Wuya Iran Ta Bude Mashigin Hormuz Afrika
Shugaban Amurka Ya Sauke Antoni Janar Amurka
Farashin Zinari Yayi Tashin Gwauron Zabi Amurka
Shugaba Trump Ya Janye Karbar Kudin Fito Daga Wasu Kasashen Turai Amurka
Wani Alkali A Kotun Amurka Ya Dakatar Da Kudurin Shugaba Trump Afrika
Ma’aikatar Tsaron Amurka Zata Kara Samar Da Makamai Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Trump Ya Yabawa Iran Bisa Bude Mashigar Hormuz Amurka
  • Kasar China Ta Sauka Daga Ragamar Bada Bashi Labarai
  • Anfara Kirga Kuri’a A zaben Kasar Guinea Labarai
  • NSC Ta Bai Wa Shugabannin NFF Sa’o’i 24 Su Yi Murabus Wasanni
  • Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Gombe Ya Ziyarci Pindiga Labarai
  • Hukumar NDLEA Ta Kama Wata Mata Da cikin Bogi Na ƙwaya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Amurka Na Kokarin Watsi Da Tsohuwar Dokar Jones Labarai
  • Jirgin Dakon Iskar Gas Daga Rasha Ya Sake Hanya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.