Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata Afrika
  • NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa Afrika
  • Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno Amurka
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe Afrika
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya Afrika

Rwanda Tana Keta Yarjejeniyar Zaman Lafiya – Tshisekedi
Published: December 9, 2025 at 3:28 AM | By: Ibrahim Alfah Ahmad

Shugaba Felix Tshisekedi na kasar Kwango ta Kinshasa, ya zargi Rwanda da laifin karya alkawarin da ta dauka karkashin yarjejeniyar zaman lafiyar da Amurka ta kulla tsakaninsu, da nufin kawo karshen yakin shekara da shekaru a gabashin wannan kasa mai dimbin arzikin ma’adinai.

Shugaba Tshisekedi yayi wannan zargi a jawabin da yayi gaban ‘yan majalisar dokoki, kwanaki kadan a bayan da ya halarci taron rattaba hannu kan yarjejeniyar a Washington.

Ya zuwa yanzu dai, babu wani martani da aka ji kan wannan zargi daga kasar Rwanda.

Wani jami’in Amurka yace gwamnatin shugaba Trump tana nazari da sa ido kan halin da ake ciki, tare da aiki da dukkan kasashen, kuma tana sa ran za a dauki matakan gaggawa na aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar.

Kazamin fadan da ake yi yana kawo tsaiko ga fara aiwatar da yarjejeniyar, wadda Amurka da Qatar suka kulla tsakanin Kwango da Rwanda da kuma kungiyar ‘yan tawayen M23. A karshen makon nan, mayakan kungiyar M23 sun kutsa kusa da bakin iyaka da Burundi, inda suka kama wani gari mai suna Luvungi.

Rwanda ta musanta zargin cewa ita ce uwargidan ‘yan tawayen na M23.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Yarjejeniyar Britaniya Da Mauritius Kan Tsibiran Chagos Cin Zarafi Ne
Next Post: Sojoji Sun Murkushe ‘Yan Bindiga A Jihar Sakkwato

Karin Labarai Masu Alaka

Amurka Ta Jefa Makamin Tomahawk A Makarantar Yara Mata Afrika
Hukumomin Tsaron Kenya Sunce ‘Yan Kasar Suna Fafata Yaki Da Dakarun Rasha A Ukraine Afrika
SERVICOM, ATBUTH Ta Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Damfara Ne Labarai
An Karrama Darakta Janar Na DSS Bisa Ƙoƙarinsa Na Inganta Alaƙar Hukumomin Tsaro Da Kafafen Yaɗa Labarai Afrika
Akwai Bukatar Bin Dokokin Tuki A Kan Hanyoyi Labarai
China Ta Kori Wakilan Majalisar Dokoki Uku A Kasar Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata
  • NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa
  • Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • EFCC Ta Cafke Fitacciyar Jarumar Kannywood Samha Inuwa Labarai
  • Amurka Da Iran Sun Cimma Yarjejeniya Tsagaita Wuta Na Makonni Afrika
  • Farashin Danyen Mai Ya Fadi A Kasuwar Duniya Afrika
  • Gwamna Zulum: Ya Bukaci Sojoji Su Cigaba Da Yakar Boko Haram Da ISWAP Labarai
  • Kasar Spain Ta Rufe Sararin Saman Kasar Amurka
  • Yusuf Gawuna Ya Koma Jam’iyar ADC Afrika
  • Papa Roma Leo Yace Zai Cigaba Da Sukan Yake Yake Afrika
  • Tinubu Ya Jaddada Aniyar Rage Tsadar Rayuwa Da Samar da Ayyukan Yi Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.