Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

An Harbo Jirgin Yakin Amurka A Iran
Published: April 3, 2026 at 9:44 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

An harbo jirgin yakin Amurka a sararin samaniyar Iran, kuma an fara aikin ceto wadda tuni yasa aka gano daya daga cikin matuka jirgin bayan da yayi amfani da laimar tsira, kamar yadda wani jami’in Amurka ya gayawa kamfanin dilancin labarai na Reuters, lamari irinsa na farko da aka sani tun bayan kaddamar da yakin wanda yanzu kusan mako biyar ana gwabzawa.

Yanayi da zai sa wani sojan Amurka ya fada hanun abokan gaba zai kasance kalubale ga Amurka, a yakin da kamar yadda kuri’un neman ra’ayin jama’a suka nuna bashi da farin jini a gun Amurkawa.

Jami’an Iran suna kira ga ‘yan kasar su zuba ido ko za su ga wani sojan Amurka da ya tsira, hukumomin sun cika kafofin sada zumunta da abunda suka ce baraguzan jirgin yakin na Amurka ne.

Jami’an Amurka biyu suka ce jirgin samfurin F15E ne, yana da wurin zaman mutum biyu, daya na matukin jirgin, guda kuma na mai harba makamai. Babu tabbas kan wanene daga cikinsu aka ceto ahalin yanzu. Jami’an Amurka da suka bada labarin ceton, ba su yi bayanin yadda aka ceto shi ba.

Ma’aikatar tsaron Amurka da ake kira Pentagon, da kuma cibiyar tafiyar da yake yake ta Amurka, duk biyu basu maida martani ba da aka tuntube su dangane da wannan batu.

Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
Next Post: Kungiyar Tsaro Ta NATO Tana Fuskantar Kalubale

Karin Labarai Masu Alaka

Koriya Ta Arewa Ta Gudanar Da Gwajin Makami Mai Linzami Tsaro
Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Gargadi Jama’ar Arewa Maso Gabas Afrika
Rangadin Ayyukan Tinubu Ya Kai Tawaga Zuwa Kano Northern Bypass Afrika
Kasar India Ta Sayi Iskar Gas Daga Iran Labarai
Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 1,597, Sun Ceto Mutane 1,516 – DHQ Afrika
Hukumar MDD Tace Wadanda Suka Mutu A Harin Sudan Sun Haura 70 Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Najeriya Da Amurka Sun Amince Su Haɗa Kai Don Inganta ’Yancin Addini Da ƙarfafa Tsaro A Nijeriya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Tarayya Tayi Baje Kolin Nasarorin Tinubu Afrika
  • ‘Yan Tawaye A Burkina Faso Sun Kashe ‘Yan Kasar Ghana Afrika
  • Rundunar ‘Yan Sanda Sun Ceto Wani Daga Hannun Masu Garkuwa Najeriya
  • Zelensky Na Ukraine Zai Gana Da Takwaransa Na Faransa A Yau Labarai
  • Yaki Tsakanin Amurka, Isra’ila Da Iran Ya Shiga Kwana Na Biyar Afrika
  • Kasar Amurka Tabada Tabbacin Bawa Ukraine Tsaron Shekarun 15 Amurka
  • Anyi Asarar Biliyoyin Naira A Gobarar Kasuwar Singa Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.