Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Wani Jirgin Kasa Yayi Hatsari A Kudancin Spain
Published: January 19, 2026 at 8:58 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Wani jirgin kasa mai saurin tafiya ya goce daga kan layin dogonsa ya kara tare da ture wani jirgin daban daga kan layinsa na dogo a yankin kudancin Spain, inda hukumomin ‘yan sanda suka tabbatar da cewa mutane akalla 21 sun mutu.

Wannan hatsarin ya faru ne a kusa da Adamuz a lardin Cordoba, inda gidan telebijin na kasar, Television Espanola, ya kara da cewa mutane 100 sun ji rauni, guda 25 daga cikinsu mummunan rauni.

Gidan telebijin na Espanola ya kara da cewa direban daya daga cikin jiragen wanda ya taso daga Madrid a kan hanyar zuwa Huelva, na daga cikin wadanda suka mutu.

Kamfanin dake tafiyar da layukan dogo na kasar, Adif, ya fada a wata sanarwar da ya bayar ta shafin sada zumunci cewa jirgin da ya fito daga Malaga a kan hanyar zuwa Madrid shine ya fara kauce ma layin dogonsa a Adamuz, ya fada kan daya layin dogon, ya kara da jirgin da ya taso daga Madrid a kan hanyar zuwa Huelva.

Kamfanin Adif yace hatsarin ya faru da karfe 6:40 na maraicen kasar, kimanin minti 10 bayan da jirgin farko ya bar Cordoba ya doshi Madrid.

Kamfanin Iryo, wanda ya mallaki jirgin kasan ya bayyana jimami da mummunan takaicin abinda ya faru, ya kuma kaddamar da shirinsa na gaggawa da yin aiki tare da hukumomin da abin ya shafa wajen tinkarar wannan lamari.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Senegal Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirka Afcon 2025.
Next Post: An Gano Wani Kurkukun Sirri Da Ake Azaftar Da Mutane A Kasar Libya

Karin Labarai Masu Alaka

EU Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Amurka Da Iran Afrika
Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Gwamna Abba Gida-Gida Na Dari-Darin Shiga APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Shugabannin Kiristoci Sun Taya Musulmi Murnar Sallah Domin Ƙarfafa Zaman Lafiya Afrika
Sanata Sa’idu Alkali Ya Kaurace Wa Zaben Fidda Gwani Afrika
Najeriya Ta Mika Koke Ga FIFA Tana Zargin DR Congo Ta Sanya ‘Yan Wasan Da Basu Cancantaba Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sauya Sunan Lafarge Africa Zuwa HBM Nigeria Plc Zai Samar Da Cigaba – Sarkin Fulanin Gombe Afrika
  • Baba Buhari Yayi Zargin Ansaka Masa Na’urar Tsaro Labarai
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Juma’a 11.21.2025 Rediyo
  • Amurka Zata Bada Gudunwa Ga Masu Zanga-Zanga A Iran Sauran Duniya
  • NUT Ta Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani Afrika
  • Sojin Kasar Congo Da ‘Yan Tawaye Sun Kara Shiga Yankin Uvira Labarai
  • Gobara Ta Tashi A Makarantar Koyon Jinyar Dabbobi Dake Jihar Kano Najeriya
  • Wani Alkali A Amurka Ya Kalubalanci Gwamnatin Kasar Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.