Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Tinubu: Mun Ware Biliyan 42 Don Inganta Lafiyar ‘Yan-Kasa
Published: January 11, 2026 at 3:26 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: January 11, 2026

Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 42 don kula da lafiyar ‘yan Najeriya miliyan 10 masu ƙaramin ƙarfi a 2026.

Gwamnatin Tarayya ta gabatar da kudirin ware Naira biliyan 42.18 domin samar da muhimman ayyukan kiwon lafiya ga ‘yan Najeriya miliyan 10 da ake ganin suna cikin masu rauni, a cikin kasafin kudin shekarar 2026 da aka gabatar wa Majalisar Tarayya.

Wannan kudin na daga cikin jimillar Naira tiriliyan 2.48 da aka ware wa bangaren kiwon lafiya a kasafin kudin shekarar, inda aka tanadi kudaden domin sayen magunguna, kayan amfani a asibitoci, kayayyakin aikin likitanci, sinadaran gwaje-gwaje da kayan gwajin cututtuka, da nufin inganta samun kulawar lafiya musamman ga talakawa a fadin kasar.

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya mika kudirin kasafin kudin shekarar 2026 ga majalisar Dokoki ta Kasa a watan da ya gabata, inda ya bayyana muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta bawa fifiko a daidai lokacin da kasar ke fuskantar kalubalen tattalin arziki da zamantakewa.

A cewar bayanan kasafin kudin, bangaren tsaro da kariya ne ya samu kaso mafi tsoka da Naira tiriliyan 5.4, sai bangaren gine-ginen ababen more rayuwa da Naira tiriliyan 3.56, ilimi da Naira tiriliyan 3.52, sannan kiwon lafiya da Naira tiriliyan 2.48, wanda ya zama bangare na hudu mafi girma a jerin fifikon kashe kudin gwamnati.

Daga cikin jimillar kasafin kudin Tarayya na Naira tiriliyan 58.47, kudin da aka ware wa kiwon lafiya ya kai kusan kashi 4.2 cikin 100. Wannan kasafin ya kunshi shirye-shirye daban-daban na rigakafin cututtuka, samar da ayyukan lafiya, sayen kayan aikin asibiti, da tallafa wa rukunin al’umma masu rauni.

A jawabinsa yayin gabatar da kasafin kudin, Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin bangarorin kiwon lafiya da ilimi wajen gina jari na bil’adama, yana mai cewa babu wata kasa da za ta ci gaba fiye da ingancin mutanenta.

Shugaban kasar ya kuma bayyana rawar da abokan hulda na kasa da kasa ke takawa wajen tallafa wa tsarin kiwon lafiyar Najeriya, inda ya ce tattaunawa da gwamnatin Amurka ta samar da damar samun tallafin fiye da dala miliyan 500 domin aiwatar da muhimman shirye-shiryen lafiya a kasar.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Habasha Tafara Gina Filin Jirgin Sama Mafi Girma A Afirka
Next Post: CAF Ta Fara Binciken Rikicin Bayan Wasa Tsakanin Algeria Da Najeriya

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaban Lebanon Ya Nemi Gudanar Da Shawarwari Kai Tsaye Afrika
Gwamnan Bauchi Ya Shiga Neman Mafita Kan Lalacewar Matatar Ruwan Alkaleri Afrika
Hawan Nasarawa A Jihar Kano Afrika
Kasashen Daular Larabawa Tare Da Saudiya Da Jordan Sunyi Allah Wadai Da kasar Israel Afrika
Anfara Gangamin Kafa Dokoki Masu Tsanani Ga ‘Yan Luwadi A Senegal Afrika
Yara Miliyan 16 Sun Amfana Da Azithromycin A Karkashin Shirin SARMAAN Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • NFF Ta Nemi Afuwar Tinubu Da ’Yan Najeriya Kan Rashin Samun Tikitin Zuwa Gasar Kofin Duniya Ta Mata Wasanni
  • Wani Jirgi Yayi Saukar Angulu Ba Shiri Najeriya
  • Sakon Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu A Ranar Dimokraɗiyya Ta 2026 Afrika
  • Gobara Ta Lalata Babban Zauren Majami’ar ECWA Gospel A Gombe Afrika
  • Shugaban Kasar Tunisiya Ya Tsawaita Dokar Da Baci A Kasar Labarai
  • Harin Bom Din Maiduguri Ya Kashe Mutane Biyar Ya Raunata Fiye Da Talatin Najeriya
  • An Yaba Wa Gwamnatin Bauchi Bisa Karban Bakuncin Gasar Polo Wasanni
  • Isra’ila Ta Zantar Da Hukuncin Kisa Ga Masu Kai Hare Hare Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.