Ƙungiyar Mata ‘yan Jarida a Najeriya ta jaddada cewa ya kamata a tallafa wa ’ya’ya mata domin su samu ingantaccen ilimi da kiwon lafiya, su bunƙasa basirarsu, tare da shiga cikin yanke shawarar da ta shafi rayuwarsu.
NAWOJ reshen Gombe ta yi kira ga Gwamnatin jihar Gombe da hukumomin da abin ya shafa da su ƙarfafa aiwatar da dokoki da manufofin da ke kare yara, magance abubuwan da ke haddasa auren wuri, tare da tabbatar da cewa an hukunta waɗanda suka aikata laifukan take haƙƙin ’ya’ya mata bisa tanadin doka.
Haka kuma, ƙungiyar ta buƙaci iyaye da masu kula da yara da su ba da fifiko ga ilimi da jin daɗin ’ya’yansu mata, tana mai cewa ilmantar da yarinya na ɗaya daga cikin hanyoyin da suka fi tasiri wajen rage barazanar da take fuskanta, karya kangin talauci daga tsara zuwa tsara, da kuma samar da al’umma mai ingantacciyar lafiya da ci gaba.
Sanarwar ta kuma yi kira ga sarakunan gargajiya da shugabannin addinai da su yi amfani da matsayinsu wajen ƙalubalantar munanan al’adu da suka zama ruwan dare, haɓaka kyakkyawan ra’ayi game da ilimin ’ya’ya mata, tare da tallafa wa shirye-shiryen al’umma da ke kare yara daga auren wuri da sauran nau’o’in cin zarafi.
Bugu da ƙari, ƙungiyar ta yi kira ga ’yan jarida da kafafen yaɗa labarai da su ci gaba da wayar da kan jama’a kan illolin auren wuri, cin zarafi da ya danganci jinsi, nuna wariya da sauran munanan al’adu, tare da yaɗa labaran nasarorin ’ya’ya mata da ke shawo kan ƙalubale domin cimma burinsu na ilimi da sana’a.


