Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

Shugaba Trump Yace Amurka Ce Zata Rika Gudanar Da Harkokin Kasar Venezuela
Published: January 5, 2026 at 5:26 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

A yayin da ake ci gaba da zaman kaka-ni-ka-yi a kasar Venezuela, shugabar wucin gadi Delcy Rodriguez, a yanzu ta maye gurbin babban abokin huldar siyasar ta, shugaba Nicolas Maduro, wanda sojojin Amurka suka kama a wani farmakin cikin dare da suka kai a kasar.

Tun shekarar 2018 Rodriguez take rike da kujerar mataimakiyar shugaba Maduro, tana mai kula da harkokin tattalin arzikin kasar da ya dogara kusan kacokan kan man fetur, tana jagiorancin hukumar leken asirin kasar, kuma ita ce magajiyar kujerar shugabanci.

Rodriguez tana daga cikin manyan jami’an gwamnatin shugaba Maduro wadanda a bisa dukkan alamu sune suke rike da madafun iko na Venezuela, duk da cewa shugaba Donald Trump na Amurka da jami’ansa sun ce zasu matsa ma gwamnatin ta lamba don ganin ta yi aiki da manufofinsu game da kasar mai arzikin man fetur.

A ranar asabar ne kotun kolin kasar ta umurce ta da ta karbi ragamar shugabancin kasar, inda kuma ta samu goyon bayan rundunar sojojin Venezuela.

A cikin jawabin da tayi ma kasar ta talebijin, Rodriguez ba ta nuna alamun cewa zata hada kai da shugaba Trump ba, tana mai bayyana gwamnatinsa a zaman ta ‘yan tsagera.

A yayin da manyan jami’an fararen hula da na soja suke kewaye da ita, Rodriguez ta ce shugaba guda daya kasar Venezuela take da shi, kuma shine shugaba Nicolas Maduro, ta ce abinda ake aikata ma kasar Venezuela, ta’asa ce wadda ta keta dokoki na kasa da kasa.

Rodriguez, lauya kuma ‘yar siyasa mai shekaru 56 da haihuwa, ta jima tana wakiltar akidar gurguzu da juyin juya halin da marigayi shugaba Hugo Chavez ya kafa a kasar.

A ranar asabar da safe, an yi mamaki da aka ji shugaba Trump yana cewa sakataren harkokin wajensa Marco Rubio yayi magana da Rodriguez, kuma ta yi godiya, sannan zata yi aiki da gwamnatin Amurka yayinda Rubio yace gwamnatin Amurka zata iya yin aiki tare da Rodriguez, ba kamar Maduro ba.

Ranar lahadi, lafazin shugaba Trump ya canja a yayin da Rodriguez da sauran jami’an gwamnatin Venezuela suka ci gaba da caccakar gwamnatin sa, tare da jaddada cewa sune suke rike da kasar ba Amurka ba.

A cikin wata hirar da yayi da jaridar The Atlantic, shugaba Trump yayi barazanar cewa idan har ba ta yi abinda ya kamata ba, to zata dandana kudarta ita ma, fiye ma da Maduro.

A ranar lahadin kuma Rubio yace ba ya daukar Rodriguez da gwamnatinta a matsayin halaltattu a saboda a cewarsa, kasar ba ta gudanar da zaben gaskiya ba.

A halin da ake ciki, sakataren harkokin wajen na Amurka Marco Rubio, yace Amurka ba zata dauki nauyin gudanar da harkokin mulkin yau da kullum na Venezuela ba, sai dai zata ci gaba da matsa lamba ta hanyar tabbatar da ci gaba da yin aiki da takunkumin mai da aka sanya ma kasar.

Wannan kuwa, babban juyi ne daga kalamen da shugaba Trump yayi kwana guda kafin nan inda yace Amurka ce zata rika gudanar da harkokin kasar ta Venezuela a bayan hambarar da Nicolas Maduro da kama shi.

Amurka, Labarai

Post navigation

Previous Post: Tinubu: Abba Magajin Aminu Kano Ne A Fagen Siyasa
Next Post: Koriya Ta Arewa Ta Gudanar Da Gwajin Makami Mai Linzami

Karin Labarai Masu Alaka

Ukraine Tana Cigaba Da Tattaunawa Da Amurka Domin Kawo Karshen Yakin Kasar Amurka
Amurka Ta Bada Tabbacin Baiwa Ukraine Tsaron Na Shekaru 15 Amurka
Jarman Deba Ya Kada Senata Goje A Zaben Fidda Gwani Afrika
Amurka Zata Fice Daga Iran Cikin Gaggawa Afrika
Kasashen Faransa Da Italiya Sun Nuna Rashin Amincewa Da Matakan Sojoji Amurka
Sojoji Sun Dakile Harin ’Yan Ta’adda a Kukareta Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sojin Najeriya Da Amurka Sun Hallaka Jagoran ISIS Afrika
  • Gwamna Inuwa Yahaya Ya Bukaci Al’ummar Gombe Su Haɗa Kai Wajen Yaƙi Da Ta’addanci Afrika
  • Janar Christopher Zai Maye Gurbin Ministan Tsaron Najeriya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Gudun Hijira A Kasar Libya Suna Fuskantar Cin Zarafi Afrika
  • Rasha Da Ukraine Sun Cigaba Da Yakar Juna Afrika
  • Ana Jimamin Mutuwar Giwa Mai Shekaru Kusan 60 A Kasar Kenya Sauran Duniya
  • Dr. Kabiru Hassan Ya Kammala Wa’adinsa A GOGIS, Ya Yi Bitar Sauye-Sauyen Harkokin Filaye Afrika
  • Jam’iyyar APC Ta Ayana Jamilu Gwamna A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Gombe Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.