Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Kasar Canada Ta Amince A Shigar Da Motoci Kirar Kasar China Kasar
Published: January 16, 2026 at 10:18 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Wakilin kasuwancin kasa da kasa na Amurka Jamieson Greer ya ce shawarar da gwamnatin kasar Canada ta yanke na barin a shigo da motoci masu amfani da wutar lantarki 49,000 kirar kasar China a haraji me sauki yana da matsala, kuma Canada zata iya yin dana sanin hakan.

Da yake Zantawa da tashar labarai ta CNBC ranar Jumu’a, Greer ya ce abin da ya sa bama sayar da motocin China da yawa a Amurka, shine saboda muna da haraji don bada kariya ga ma’aikatan kamfanonin motoci na Amurka, mu kuma kare Amurkawa daga wadannan motocin.

Ya ce Canada na neman saukin harajin amfanin gona ne, a cikin yarjejeniyar na motocin masu amfani da lantarki, ina ganin nan gaba baza su so kulla wannan yarjejeniya da suka yi ba.

A yau Jumu’a ne Canada da kasar China suka kulla yarjejeniyar kasuwanci da zai rage haraji kan motoci masu aiki da lantarki da man girki na Canola, inda Canadan zata bari a shigo da motocin China masu aiki da lantarki 49,000, kan haraji 6.1 cikin dari.

A farkon makon nan ne shugaban Amurka Donald Trump ya kara jaddada maganar da ya yi lokacin da yake yakin neman zabe a Detroit da ke jihar Michigan cewa zai so masu kera motoci a China su zo Amurka su kera motoci.

Amurka

Post navigation

Previous Post: ‘Yan Kasar Cuba Sunyi Zanga Zanga A Ofishin Jakadancin Amurka
Next Post: Mutane Da Dama Sun Rasa Rayukansu Yayin Rikici A Uganda

Karin Labarai Masu Alaka

Wani Alkali A Amurka Ya Kalubalanci Gwamnatin Kasar Afrika
Shugaban Amurka Yace Zayyi Wahala A Cimma Yarjejeniya Tsakanin Isra’ila, Amurka Da Iran Amurka
Amurka Zata Bada Gudumawar Kudi Dala Bilyan 10 Ga Ayyukan Kwamitin Wanzar Da Zaman Lafiyan Amurka
Rasha Ta Yiwa Amurka Tayin Daina Bada Bayanan Sirri Afrika
Papa Roma Leo Yace Zai Cigaba Da Sukan Yake Yake Afrika
Angano Gawar Wani Dan Myanmar A Arewacin New York Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ambaliyar Ruwan Sama Yayi Ajalin Mutum 13 A Malawi Labarai
  • CBN: An Samu Ƙaruwar Masu Cin Bashin Banki Basa Biya Najeriya
  • Wasan Hamayya (Istanbul Derby) Fenerbahçe Da Galatasaray 1-1 Labarai
  • Mayakan ISWAP Sun Kai Farmaki Kan Sojojin Najeriya Najeriya
  • Gwamnatin Tarayya Tayi Baje Kolin Nasarorin Tinubu Afrika
  • CAF Ta Hukunta Samuel Eto’o AFCON 2025 Labarai
  • Iran Tabada Tabbacin Cigaba Da Rufe Mashigar Hormuz Afrika
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Fiye Da Mutane 50 Tare Da Sace Mata Da Yara A Jihar Zamfara Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.