Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana cewa ta samar da motocin bas 40 masu amfani da iskar gas (CNG), motocin lantarki guda bakwai da kuma sama da keke Napep 200 masu amfani da CNG a Jihar Kano cikin shekara guda da kaddamar da shirin sauya fasalin harkokin sufuri zuwa makamashi mai araha.
Shugaban Hukumar Pi-CNG da EV, Barista Ismaeel Ahmad, ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da rahoton shekara guda na ayyukan shirin da Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kaddamar domin rage radadin tsadar sufuri da samar da hanyoyin makamashi masu rahusa ga ‘yan Najeriya.
Ya ce an fara aiwatar da shirin CNG da motocin lantarki na yankin Arewa daga Kano, inda aka bude tashoshin CNG da LCNG a jihohin Kano State, Katsina State, Gombe State da Kaduna State domin kara saukaka amfani da makamashin iskar gas a fannin sufuri.
Barista Ismaeel Ahmad ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta bullo da shirin samar da kayan sauya motoci 100,000 zuwa amfani da CNG tare da tsarin “Convert Now, Pay Small Small”, wanda ke bai wa masu ababen hawa damar sauya motocinsu ba tare da matsin lambar kudi ba.
A cewarsa, babban burin shirin shi ne rage tsadar zirga-zirga, bunkasa amfani da makamashi mai tsafta, kare muhalli da kuma inganta rayuwar al’umma ta hanyar samar da hanyoyin sufuri masu araha da dorewa.


