Lauyoyin Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ɗan takarar gwamnan jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, sun bai wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, wa’adin kwanaki uku da ta saka sunansa a cikin jerin sunayen ‘yan takarar zaɓen shekarar dubu biyu da ashirin da bakwai.
A cikin wata wasiƙa da suka aika wa shugaban hukumar ta INEC a ranar Litinin, lauyoyin, waɗanda manyan lauyoyin Najeriya, wato SAN, suka jagoranta, ciki har da Ahmed Raji, A.T. Kehinde da Abdul Mohammed, sun nuna rashin amincewarsu da cire sunan Pantami daga jerin sunayen ‘yan takarar da hukumar ta wallafa a ranar goma ga watan Oktoban shekarar dubu biyu da ashirin da shida.
Lauyoyin sun bayyana cire sunan Pantami a matsayin matakin da ya saɓa wa doka kuma ba tare da wani cikakken bayani ba.
Sun ce babu wani dalili na doka da zai sa hukumar INEC ta cire sunan wanda suke karewa, bayan ya lashe zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar PDP da aka sake gudanarwa a ranar ashirin da tara ga watan Satumban shekarar dubu biyu da ashirin da shida.
Saboda haka, sun buƙaci hukumar INEC ta saka sunan Pantami cikin jerin sunayen ‘yan takarar kafin ranar Laraba, goma sha huɗu ga watan Oktoba, tare da bai wa sunansa irin matsayin da sauran sunayen ‘yan takara suke da shi.
A cewar wasiƙar, Farfesa Pantami ya shiga zaɓen fitar da gwani na farko na jam’iyyar PDP a ranar ashirin da shida ga watan Mayun shekarar dubu biyu da ashirin da shida, inda ya yi nasara.
Sai dai daga bisani, wasu mutane sun ƙalubalanci zaɓen a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe.
A hukuncin da ta yanke a ranar ashirin da huɗu ga watan Satumba, kotun ta soke zaɓen fitar da gwani na ranar ashirin da shida ga watan Mayu, saboda wasu matsaloli da suka shafi yadda aka gudanar da shi.
Kotun ta kuma umarci jam’iyyar PDP da ta sake gudanar da zaɓen fitar da gwani cikin kwanaki talatin.
Sai dai lauyoyin Pantami sun bayyana cewa kotun ta riga ta warware ƙalubalen da ake yi game da kasancewar Pantami mamba a jam’iyyar da kuma cancantarsa ta tsayawa takara, inda ta yanke hukunci a kan masu ƙarar a waɗannan batutuwa.
Sun ce kotun ta tabbatar da cewa masu ƙarar ba su gabatar da hujjojin da za su tabbatar da cewa Pantami bai cancanci zama mamba ko kuma jam’iyyar PDP ta tsayar da shi takara ba.
Lauyoyin sun ƙara da cewa hukuncin kotun ya shafi zaɓen fitar da gwani da aka soke ne kawai, kuma bai hana INEC amincewa da sakamakon sabon zaɓen fitar da gwani da aka gudanar bisa umarnin kotun ba.
Haka kuma, lauyoyin sun yi nuni da wasu hukunce-hukuncen kotuna a baya, ciki har da shari’o’in Dingyadi da INEC, da kuma Raymond da INEC.
Sun bayyana cewa cire sunan ɗan takarar da jam’iyya ta tsayar daga jerin sunayen ‘yan takara mataki ne da ya kamata ya dogara da hukuncin kotu.
A cewarsu, aikin INEC dangane da zaɓen fitar da gwani na jam’iyyu shi ne lura da yadda ake gudanar da zaɓen, sa ido da kuma gabatar da rahoto, ba wai ta yanke hukuncin hana ɗan takara tsayawa takara da kanta ba.
Saboda haka, sun buƙaci hukumar ta INEC da ta ɗauki matakin gaggawa domin gyara abin da suka bayyana a matsayin kuskuren cire sunan Pantami, tare da aika musu da rubutaccen bayani kan matakan da ta ɗauka.
Majoyoyi sun ruwaito a baya cewa sunan Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami bai bayyana a cikin jerin sunayen ‘yan takarar gwamna na ƙarshe da hukumar INEC ta fitar a ranar Asabar ba.
Har yanzu dai ana jiran matakin da hukumar INEC za ta ɗauka kan buƙatar lauyoyin Pantami.


