Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Jirgin Ruwa Ya Kife A Yammacin Kasar Gambiya
Published: January 2, 2026 at 12:00 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: January 2, 2026

Kasar Gambia ta ceto mutane 96, da gawarwakin wasu mutane bakwai, bayan jirgin ruwa dauke da fiye da bakin haure 200 ya kife a yammacin kasar, kamar yadda ma’aikatar tsaron Gambia ta fada a cikin wata sanarwa data bayar ranar Alhamis. Ma’aikatar ta kara da cewa ana ci gaba da aikin ceto.

Wannan shine mummunar hatsari na baya bayan nan akan hanya mafi hadari da bakin haure galibi daga Afirka ta yamma suke bi a kokarin da suke yi na isa Spain ko Andalusiya ta wani tsibiri da ake kira Canary Island.

An sami rahoton cewa jirgin ya kife ne a tsakiyar dare kusa da wani kauye daga bisani aka sami jirgin ya kafe cikin yashi a wani yanki na kasar dake arewaci, kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar ta fada.

Kungiyar tarayyar turai tace bakin haure na ba safai ba dubu 46 ne suka isa tsibirin Canary a shekarar 2024, adadi mafi yawa da aka gani, fiye da mutane dubu 10 suka mutu a kokarin su na zuwa turai, wanda ya nuna karin kashi 58 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar 2023, inji wata kungiyar kare hakkin bil’adma da ake kira Caminando.

Amma alkaluma daga hukumar kula da shige da fice ta kunigyar tarayyar turai watau EU a takaice, tace a watanni 11 na shekarar 2025, an sami ragowar korarar irin wadanan mutanen daga Afirka ta yamma masu niyyar zuwa turai da kashi 60 cikin dari.

Hukumar shige da fice ta turai tace raguwar masu tafiya turan, ya ta’allaka ne kan matakan hana tafiye tafiye masu tsanani da kasashe da ake tashi cikinsu wadanda suke aiki da kungiyar tarayar turan suke dauka.

Akalla mutane 70 ne suka halaka cikin watan Agustan bara, lokacin da jirgin da suke ciki, da aka ce ya ta so daga Gambiya ya kife, a hatsari mafi muni da aka gani a cikin shekarun baya bayan nan.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Jamhuriyar Congo Zata Cigaba Da Fitar Da Ma’adanai
Next Post: Darajar Kudin Afirka Ta Kudu Ya Tashi

Karin Labarai Masu Alaka

Fafaroma Leo Yayi Allah Wadai Bisa Karuwar Yake Yaken Gabas Ta Tsakiya Amurka
Tinubu Ya Yi Allah Wadai Da Kashe-kashen Jos Da Kaduna Afrika
APC Ta Bayyana Abba Yusuf A Matsayin Halastaccen Ɗan Takara Bayan Cika Sharudda Afrika
Isra’ila Ta Cire Sunayen Wasu Mutane Biyu Cikin Wadanda Take Fako Afrika
Kannywood: Ali Nuhu Ya Shiga Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu Afrika
Masar Tayi Yarjejeniyar Makamashi Da Kasashen Norway Da China Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Muhimmin Sako Ga Alhazai Dake Kasar Saudiya Afrika
  • Shugabar Hamayya A Venezuela Ta Gana Da Paparoma Leo Amurka
  • Gombe Ta Ƙarfafa Ilimin Almajirai Da Tsangaya Don Rage Yaran Da Ba Sa Zuwa Makaranta Afrika
  • Kasashen Yankin Gulf Sun Bada Sanarwa Afrika
  • Kamfanonin Jiragen Sama Suna Fama Da Karin Farashin Mai Labarai
  • Gwamnatin Najeriya Ta Karyata Raɗe-Raɗin Canza Sunan Kasar Da Soke Shari’a A Arewa Afrika
  • Makiyaya Sun Shiga Matsala Sakamakon Fari A Kasar Kenya Afrika
  • Hukumar DSS Ta Sake Kama Abubakar Malami Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.