Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Masana Yanayi Sun Bukaci Haɗin Gwiwa Kan Barazanar El Niño A Najeriya Afrika
  • Kotu: Atiku Abubakar Haramtaccen Dan Takarar ADC Ne A 2027! Afrika
  • Tinubu Zai Ciwo Bashin Dala Biliyan 7.7 Afrika
  • Gwamnatin Tinubu Ta Ƙaddamar Da Tsarin Bada Kudi Na SPARK Afrika
  • Jam’iyyar PDP Ta Sallami Manyan ’Ya’yanta Biyu A Gombe Labarai

An Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman Don Neman Zaman Lafiya
Published: December 31, 2025 at 1:45 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: December 31, 2025

An Gudanar da addu’oi karshen Shekara a Masarautar Kaltungo dake jihar Gombe, a yayin kamallah bukin al’adu na Karamar Hukumar Kaltungo na shekarar 2025.

A jawabin sa Mai Kaltungo Injiniya Saleh Muhammadu ya yabawa kokarin dukkan wanda suka bada gudunmawa tare da kira ga ‘yan Masarautar dasu samar da Makarantu domin inganta Ilimi da zummar yakar jahilci a yankin.

Sannan kuma ya bukaci inganta harkokin noma ta hanyar samar da kayan aiki na zamani.

Shima a jawabin sa Shugaban kwamitin tsara bukin na wannar Shekarar Mr. Muhammad Dantata Ndus ya godewa dukkan ‘yan Jarida da kafafen yada labarai da suka yayata Bukin na wannan shekarar.

Taron addu’oi’n wanda ya gudana a Fadar mai Kaltungo ƙarƙashin jagorancin Alhaji Saleh Muhammadu yasamu halartan manyan Malaman addinin Musulunci dana Mabiya addinin Kirista a Masarautar.

Daga cikin Malaman da suka halarta akwai Limamin Masallacin Fadar Gombe Barrister Aliyu Hammari Walama da Shugaban Jama’atul Nasrul Islam na jihar Gombe Alhaji Saleh Danburam, Pastor Babale Garus da shugaban CAN na shongom Pastor Enoch Timothy da Bishop Yilde Lapan.

Malaman addinin sunyi wa’azi tare da bukatar al’umma su hadakai su zauna lafiya da juna kuma kowa yayi addinin sa batare da tsangwama ba.

Masu wa’azin sun gudanar da addu’o’i na wanzuwar zaman lafiya a Masarautar Kaltungo, jihar Gombe dama Najeriya baki daya.

Labarai

Post navigation

Previous Post: An Yi Fashin Kaguwa Da Dodon-Kodi Na Miliyoyin Dalar Amurka
Next Post: Tsarin Haraji Mai Cike Da Ayoyin Tambaya Na Shirin Fara Aiki

Karin Labarai Masu Alaka

Majalisun Najeriya Sun Amince Ta Karin Kasafin Kudi Afrika
Kotu A Kasar Faransa Ta Daure Roger Lumbala Shekaru 30 Labarai
Tinubu Ya Nemi ‘Yan Najeriya Su Sake Zaɓensa A 2027 Afrika
Azumin Ramadan Yahadu Da Azumin Lent Da Mabiya Addinin Kirista Sukeyi A Wannan Shekarar Labarai
Hukumar DSS Ta Sake Kama Abubakar Malami Labarai
Mutfwang Ya Yi Wa Fursunoni 130 Afuwa Yayin Bikin ’Yancin Kan Najeriya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Masana Yanayi Sun Bukaci Haɗin Gwiwa Kan Barazanar El Niño A Najeriya
  • Kotu: Atiku Abubakar Haramtaccen Dan Takarar ADC Ne A 2027!
  • NFWP-SU Sun Gargadi Mata Kan ’Yan Damfara
  • Tinubu Zai Ciwo Bashin Dala Biliyan 7.7
  • Gwamnatin Tinubu Ta Ƙaddamar Da Tsarin Bada Kudi Na SPARK

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Matatar Man Dangote Zata Bada Kwangilar Sayar Da Gas Da Man Jirage Afrika
  • An Gudanar Da Addu’oi Ga Mutane 16 Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe a Australiya Tsaro
  • Hukumar ICPC Ta Gayyaci Dangote Labarai
  • Sojoji Sun Dakile Harin ’Yan Ta’adda a Kukareta Afrika
  • Limamin Da Ya Ceci Kiristoci Lokacin Rikicin Addini A Jihar Filato Ya Rasu Labarai
  • Shugaba Donald Trump Yabada Umarnin Hana Jiragen Dakon Mai Shiga Venezuela Amurka
  • Shugaba Tinubu Ya Kara Aika Sunayen Jakadu Ga Majalisa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Tarayya Ta Ce Babu Musguna Wa ’Yan Jarida A Mulkin Tinubu Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.