Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Masu Ruwa Da Tsaki 60 Sun Samu Horon Sasanta Rikici Don Ƙarfafa Zaman Lafiya
Published: September 5, 2026 at 11:15 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ƙungiyar Network of Peace Journalists (NPJ) ta yaba wa Ofishin Jakadancin Jamus a Najeriya, Cibiyar Sasanta Rikicin Addinai (IMC) da Kotun Sasanta Rikici ta Jihar Kaduna (KDMDC), bisa shirya wani horo na kwanaki biyu kan Madadin Sasanta Rikici ba tare da zuwa kotu ba (ADR), wanda ya samu halartar sama da masu ruwa da tsaki 60 daga sassa daban-daban na jihar Kaduna a Najeriya.

Shugaban ƙungiyar ta NPJ, Ambassador Ibrahima Yakubu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai bayan kammala horon na kwanaki biyu.

Ya bayyana shirin a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa ƙwarewar masu ruwa da tsaki wajen hana rikice-rikice, sasanta bambance-bambance da kuma inganta zaman lafiya tsakanin al’umma.

A cewarsa, horon ya haɗa sama da mahalarta 60 da suka fito daga ɓangaren shari’a, lauyoyi, ƙungiyoyin farar hula da jami’o’i, da kuma shugabannin mata da na addinai daga shiyyoyin sanatoci uku na Jihar Kaduna.

Mahalarta sun haɗa da wakilan Hukumar Korafe-Korafen Jama’a, Hukumar Kare Haƙƙin Bil’adama ta Ƙasa da Ƙasa, Cibiyar Sasanta Rikicin Addinai, alkalai, lauyoyi, malamai, shugabannin mata da shugabannin addinai, da sauran masu ruwa da tsaki.

Ambassador Yakubu ya ce horon ya bai wa mahalarta damar koyon dabaru na fahimtar yanayin rikici, nazarin rikice-rikice, fahimtar nau’ikan halayen mutane da kuma hanyoyin daban-daban na Alternative Dispute Resolution (ADR).

Ya ce ilimi da ƙwarewar da mahalarta suka samu za su taimaka musu wajen shiga tsakani cikin rikice-rikicen al’umma yadda ya kamata, tare da hana ƙananan saɓani rikidewa zuwa rikici mai ɗauke da tashin hankali ko kuma shari’o’in da za su ɗauki tsawon lokaci a kotu.

Ya ƙara bayyana cewa an ƙarfafa mahalarta da su kafa abin da ya kira “tantunan sasanci” a cikin al’ummominsu da wuraren aikinsu, domin a rika magance saɓani ta hanyar tattaunawa da sasanci kafin lamarin ya kai ga shigar da ƙara a kotu.

Shugaban NPJ ya yaba wa Ofishin Jakadancin Jamus, IMC da KDMDC bisa nasarar aiwatar da shirin tare da haɗa masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na Jihar Kaduna.

Ya ce shirin ya nuna muhimmancin ƙarfafa hanyoyin da al’umma ke amfani da su wajen hana rikici da kuma sasanta saɓani cikin lumana, musamman a lokacin da al’ummomi ke buƙatar samun damar tattaunawa da sasanci cikin sauƙi.

Ambassador Yakubu ya kuma yaba wa Ofishin Jakadancin Jamus da Cibiyar Sasanta Rikicin Addinai bisa ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen samar da zaman lafiya, musamman shirye-shiryen da ke ƙarfafa shigar mata cikin ayyukan samar da zaman lafiya, kare haƙƙin bil’adama da kuma ’yancin yin imani da addini.

Ya jaddada cewa saka hannun jari wajen sasanci, tattaunawa da samar da zaman lafiya mai haɗa kowa zai taimaka wajen gina al’ummomi masu ƙarfi tare da samar da zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa a Jihar Kaduna da Najeriya baki ɗaya.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Shirye-Shirye

Post navigation

Previous Post: Gombe Ta Ƙarfafa Ilimin Almajirai Da Tsangaya Don Rage Yaran Da Ba Sa Zuwa Makaranta
Next Post: Jihar Filato Ta Rufe Makarantu Don Dakile Yaduwar Diphtheria

Karin Labarai Masu Alaka

An Kama Tsohon Jakadan Birtaniya A Amurka Peter Mandelson Amurka
Kamfanonin Jiragen Sama Suna Fama Da Karin Farashin Mai Labarai
Shugaban Kasar Uganda Yana Kokarin Mayar Da Mulkin Kasar Na Gado Labarai
Wasu Yara 50 Sun Kubuta Daga Hannun ‘Yan-Ta’adda Labarai
Iran Ta Kama Wani Jirgin Ruwa Shake Da Mai Labarai
Amurka Da Isra’ila Sunkai Hari Kan Iran Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Hamas Ta Mika Ma Isra’ila Gawar Daya Daga Cikin Mutane Biyu Sauran Duniya
  • Gwamnatin Najeriya Zata Rabawa Al’umma Tallafin Noma Afrika
  • Gwamnan Jihar Kebbi Ya Amince Da Biyan Hakkokin Tsofin Ma’aikata 800 Labarai
  • ‘Yan-Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Daliban St. Mary! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugaban Kasar Amurka Yakara Hana Wasu Kasashe Shiga Amurka Ciki Harda Nijar Amurka
  • Kadan Daga Cikin Abubuwan Da Suka Faru A 2025 A Nan Amurka Amurka
  • Gwamnatin Amurka Tana Ganawa Da Manyan Jami’an Leken Asiri Amurka
  • Jamhuriyar Dimokraɗiyya Kwango Ta Bukaci Rwanda Ta Daina Marawa ‘Yan Tawayen M23 Baya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.