Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
Published: September 6, 2026 at 5:11 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: September 6, 2026

Gwamnan jihar Jigawa a Najeriya Malam Umar Namadi, ya amince da naɗin, Dakta Lawan Ahmed Muhammad Sani, a matsayin Sarkin Gumel na 17.

Sakataren Gwamnatin jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ne ya sanar da naɗin ta cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, inda ya ce naɗin ya biyo bayan shawarar da Majalisar Masu Zaɓen Sarkin Gumel da Majalisar Sarakunan jihar Jigawa suka gabatar wa gwamnan.

Kafin naɗinsa ya kasance shi ne Chiroman Gumel, sannan yana riƙe da muƙamin Daraktan Tsaron Intanet na Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Najeriya (NITDA).

Dakta Lawan dai ya gaji mahaifinsa, Alhaji Ahmed Muhammad Sani II, ne wanda ya rasu a ranar Alhamis, 3 ga Satumban shekarar 2026, bayan shafe shekaru 46 yana mulkin Masarautar Gumel.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya, Shirye-Shirye, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
Next Post: IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya

Karin Labarai Masu Alaka

Asusun IMF Ya Bukaci Afirka Ta Kudu Ta Rage Bashin Da Suke Karba Afrika
Gwamna Abba Gida-Gida Na Dari-Darin Shiga APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Iran Ta Kama Wani Jirgin Ruwa Shake Da Mai Labarai
Gwamna Fubara Ya Koma Jam’iyar APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Isra’ila Zata Rusa Gidajen Da Suke Iyakarta Da Lebanon Labarai
Kasar Sham Ta Sanar Da Tsagaita Wuta Tsakaninta Da Kungiyar Kurdawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Isra’ila Ta Dau Alwashin Kawo Karshen Falasdi Labarai
  • CAF, Zata Ci Tarar Wasu Kasashe AFCON 2025 Wasanni
  • Shugaba Tinubu Ya Gana Da Takwaransa Na Kasar Jamus Akan Sha’anin Tsaro Labarai
  • Atiku: Zaben 2027 Zai Zamo Karo Na Karshe Da Zan Nemi Shugabancin Najeriya Afrika
  • Kungiyar Kiristoci Ta Karyata Kubutar Da Mambobin Su A Kaduna Afrika
  • Hamma Saleh Ya Yi Fatali da Bai Wa Pantami Takarar Gwamna a PDP Afrika
  • Chadi Ta Sauyawa ‘Yan Gudun Hijira Matsuguni Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.