Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 33 Bisa Zargin Kai Hari A Jihar Kwara
Published: April 14, 2026 at 9:00 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

A Najeriya ‘yan sandan kasar sun kama mutane 33 wadanda ta bayyana su a zaman ‘yan banga kan zargin wani hari da aka kai kan wani coci a jahar kwara cikin watan Nuwamba, har aka yi garkuwa da mutane 38, kamar yadda rundunar ta fada a ranar talata, a zaman wani mataki na murkushe masu tada husuma a kasa.

Kakakin rundunar ‘Yan sandan kasar Anthony Okon, yace gungun bata garin ne suka kai harin na ranar 18 ga watan Nuwamba kan cocin Christ Apostilic Chuch dake garin da ake kira Eruku, haka rundundar tana zargin mutanen da laifin wasu sace sacen mutane, da dabbobi, da kuma fashi da makami a fadin yankin.

Sanarwar da kakakin rundunar ‘Yan sandan ya bayar, tace an kama mutanen ne a wasu somame da suka kai fadin jihar Kwara da makwabciyarta jahar kogi, bayan da suka sami bayanan sirri daga mutum da na’urori, azaman wani bangare na matakan tsaro da ya kai ga kama mutane 50 wadanda ake tuhuma, tun cikin watan Janairun bana.

Najeriya ta juma tana fama da matsalolin tsaro, da suka hada da sace sacen gungun mutane, domin neman kudin fansa, da fitinar ‘yan bindiga da wasu mayakan sakai.

Afrika, Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Papa Roma Leo Yayi Gargadi Game Da Rushewar Dimokraɗiyya
Next Post: ADC Ta Kaucewa INEC Ta Gudanar Da Babban Taro

Karin Labarai Masu Alaka

An Zargi Babban Mai Gabatar Da Kara A Kotun Duniya Ta ICC Afrika
Amurka Zata Saidawa Saudiyya Da Jirgin Yaki Samfurin F35 Labarai
Lawanti Ya Ƙara Wa Gombe Daraja A Fannin Aikin Jarida – NUJ Afrika
Gwamnatin Kasar Guinea Ta Soke Wasu Jam’iyyun Siyasa Afrika
Nan Gaba Kadan Kwallon Badminton Zata Samu Karbuwa Kamar Kwallon Kafa A Duniya Labarai
Gobara Ta Lalata Babban Zauren Majami’ar ECWA Gospel A Gombe Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yansandan Uganda Sun Tsare ‘Yar Fafutukar Kare Hakkin Bil’adama Sarah Bireete Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Makarantun Allo Zasu Yi Gogayya Da Na Boko Labarai
  • Babu Alamar Tsagaita Wuta A Yakin Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • Wani Bayahude Ya Harbe Bafalatsine Dan Shekaru 16 Tsaro
  • Ukraine Ta Aika Tawagar Kwararru Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • Gwamna Zulum: Ya Bukaci Sojoji Su Cigaba Da Yakar Boko Haram Da ISWAP Labarai
  • Manchester United Ta Sallami Ruben Amorim Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Majalisa Ta Sanya Baki Akan Rikici Tsakanin Dangote Da Hukumar Albarkatun Mai Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.