Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja Afrika
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe Afrika
  • Billiri/Balanga: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Sabon Zabe, Amma Gwamnati Ta Yi Shiru – AB Ibrahim Afrika
  • Hukumomin Kashe Gobara A Gombe Sun Ƙarfafa Haɗin Kai Don Hana Gobara A Lokacin Bazara Labarai

Ana Kokarin Dawo Da Wutan Lantarki A Cuba
Published: March 23, 2026 at 10:33 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ƙasar Cuba ta ce ta fara ƙoƙarin dawo da wutar lantarki tun da sassafe a ranar Lahadi, bayan da tsarin rarraba wutar lantarki na ƙasar ya rushe karo na biyu cikin mako guda, a yayin da takunkumin man fetur na Amurka ke ci gaba da yi wa gundarin tsarin makamashin tsibirin illa mai tsanani.

Tsarin wutar ya rushe ne a yammacin ranar Asabar da misalin ƙarfe 6:32 na yamma (2232 GMT), bayan da wata babbar tashar samar da wuta a Nuevitas, a lardin Camaguey na gabashin Cuba, ta samu matsala ta daina aiki, a cewar kamfanin kula da wutar lantarki na ƙasar UNE. Wannan ya haddasa jerin matsaloli da suka janyo katsewar wuta ga kusan mutane miliyan 10 na ƙasar.

Ma’aikatar makamashi da ma’adinai ta Cuba ta ce da sassafe ranar Lahadi ta kafa ƙananan tsarin wutar lantarki masu zaman kansu a dukkan lardunan ƙasar, domin dawo da wuta ga muhimman ayyuka kamar asibitoci, samar da ruwa da rarraba abinci.

Ma’aikatar ta kuma bayyana a shafukan sada zumunta cewa tashoshin wutar lantarki guda biyu da ke aiki da iskar gas, waɗanda kamfanin Energas ke sarrafawa, suna aiki a yankunan Varadero da Boca de Jaruco, sannan an samu isar da wutar lantarki zuwa tashar Santa Cruz da ke amfani da man fetur.

Afrika, Labarai, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Akwai Yiwuwar Farashin Mai Zai Kara Tashi
Next Post: Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta

Karin Labarai Masu Alaka

’Yan Sanda, Sojoji Da DSS Sun Ceto ‘Yan NYSC Da Aka Sace A Kogi Afrika
An Ceto Iyalan Ahmed Zakka Da Aka Sace A Kaduna Afrika
Shugaba Tinubu Ya Ware Kudade Domin Bunkasa Rayuwar ‘Yan Najeriya Afrika
Amurka Da Kasashen Yamma Suna Cigaba Da Kai Ruwa Rana Akan Nukiliyar Iran Afrika
‘Yan Sandan Najeriya Sunyi Nasarar Hallaka ‘Yan Ta’adda A Katsina Afrika
Amurka Ta Kulla Yarjejeniya Da Kasashe Hudu Domin Inganta Kiwon Lafiya Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Agadez: An Gudanar Da Jana’izar Mutane Da Suka Mutu A Wani Harin Ta’addanci
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja
  • Tambuwal Ya Karyata Rahotannin Shirin Komawarsa APC
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ghana Tayi Watsi Da Yarjejeniya Akan Hakar Ma’adanai Afrika
  • Yeriman Ingila Ya Mayarwa Trump Martani Amurka
  • Usman Maiyama Ne Gwarzon Kamun Kifin Argungu Bana Labarai
  • Dakarun Sojin Najeriya Sun Kashe Yan Kungiyar Lakurawa Afrika
  • Sarkin Gombe Ya Ziyarci Gwamna Inuwa Yahaya Afrika
  • Isra’ila Ta Cire Sunayen Wasu Mutane Biyu Cikin Wadanda Take Fako Afrika
  • Baital Malin Amurka Tace Sahannun Trump Zai Fito A Kudin Kasar Amurka
  • Ruwa Kamar Da Bakin Kwarya Ya Haifar Da Mutuwar Mutane A Nairobi Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.