
Hukumar yaki da cin hanci ta ICPC ta ce ta kwato kimanin Naira biliyan 40 daga barayin biro a tsakanin jami’an gwamnati cikin shekarar nan ta 2024 mai karewa.
Shugaban IICPC Dokta Musa Adamu Aliyu ya baiyana haka a taron bitar aiyukan hukumar na shekara da ya samu halartar shugaban EFCC da sauran jagororin hukumomin da su ka shafi mu’amala da kudi.
Dr.Musa Adamu ya ce binciken da su ka gudanar ya bankado aiyukan rashawa masu ban mamaki daga bangarorin da ba a ma tsammani.
Cikin misalan da ya bayar har da karbar makudan kudi wajen biyan ma’aikatan bogi da wasu hanyoyin karkatar da kudin gwamnati.
Shugaban hukumarEFCC Ola Olukoyede ya karfafa muhimmancin aiki tare tsakanin hukumomin biyu na yaki da rashawa na Najeriya “duk aikin da ya shafi ICPC kar a kai wa EFCC hakanan duk aikin da ya shafi EFCC kar a kawo ICPC” Inji Olukoyede.
Shi kuma kwamishinan yaki da cin hanci na Saliyo da ya zama babban bako mai jawabi ya koka kan yanda ya ce a kan gudanar da bincike mai kyau amma a kotuna sai a samu cikas wajen wa imma yanke hukunci marar tsauri ko ma masu laifi su zama an wanke su.
Daya daga mahalarta taron Dokta Sule Yau Sule ya ce matukar an yaki cin hanci to duk ‘yan kasa za su amfana da arzikin kasa.
Taron ya karfafa cewa kudaden da a ke sacewa sun kai matsayin da za su iya samar da ababen more rayuwa ga dukkan ‘yan kasa.
PICS- ICPC Headquarters, Musa Adamu Aliyu of ICPC and Francis Ben with thick hair, other participants